Katin gargadi - Man City 2-0 Liverpoo
An bai wa dan wasan Manchester City, Mendy katin gargadi bayan da ya dauki kwallo zai yi jifa sai ya tsaya bata lokaci.
Wannan shafi ne kai tsaye da ke dauke da labarin wasanni a karawar Manchester City da Liverpool da na Real Madrid da Getafe.
Mohammed Abdu
An bai wa dan wasan Manchester City, Mendy katin gargadi bayan da ya dauki kwallo zai yi jifa sai ya tsaya bata lokaci.
Kwallo mai kyau City ta ci Liverpool na biyu.
Kuma tun daga tsakiya aka dauko kwallon aka dunga bani in baka aka kaita hagu aka koma da ita dama daga baya aka nemi Sterling shi kuwa ya take kwallo kuma tsakanin Gomez da van Dijk ya zura kwallon a raga.
Mohammed Salah ya kusan farke kwallo bayan da ya yi gudu zuwa ragar City sai mai tsaron raga Ederson ya yi maza ya fito ya kuma riga Salah taba kwallan ta yi wajen jifa ba wani hadari.

Asalin hoton, AFP
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
An bai wa Gomez katin gargadi sakamakon kokawa da ya yi ya yar da Sterling wanda hakan ne ya sa aka bai wa City fenariti ta kuma buga ta ci.
Wannan ne karon farko da Sterling ya ci Liverpool kwallo.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Raheem Sterling ne aka kayar a cikin gidan Liverpool nan da nan alkalin wasa ya bayar da bugun fenariti.

Asalin hoton, Reuters

Asalin hoton, PA Media
Liverpool ta kusan shiga gaban Manchester, bayan da Mohamed Salah ya samu kwallo ya buga sai ta bugi turke ta kuma je wajen Sadio Mane amma yana sa kafa sai kwallon ya yi nasa waje.
Liverpool na sa wa City matsi.

Asalin hoton, AFP
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Inter Milan ta dauki mai tsaron baya, Achraf Hakimi daga Real Madrid kan yarjejeniyar shekara biyar.
Dan wasan tawagar Morocco mai shekara 22 ya buga wa Real Madrid wasa 17, yi kaka biyu a wasannin aro a Borussia Dortmund.
Wasu rahotanni na cewa Inter ta biya Real Madrid kudin da ya kai fam miliyan 36 ga dan wasan da ya fara wasa daga makarantar koyon tamaula ta Real Madrid.
A wata sanarwa da Real Madrid ta fitar ta yi godiya ga Hakim kan gudunmuwar da ya bayar ta kuma yi masa fatan alheri a sabuwar kungiyar da ya koma.
Hakimi mai tsaron baya ko daga hagu ko dama yana kuma iya wasa a tskaita an nuna hotonsa a lokacin da litkitocin Inter Milan ke gwada lafiyarsa.
Ya buga wa Dortmund wasa sama da 70 ya kuma ci kwallo 12.

Asalin hoton, Getty Images
Sadio Mane ya ja kwallo daga bangaren hagu kuma kwallon da ya yi kokarin bayar wa hakan bai yi wu ba, kuma tuni masu tsaron bayan City suka dauke kwallon don kar ya yi musu illa.
An take wasan Manchester City da Liverpool ko za ku iya cinkar nawa da nawa za a tashi a wasan nan?
Kamar yadda City ta fada ta girmama Liverpool inda yan wasanta suka yi layi masu fuskantar juna.
Hakan ya sa Liverpool ta bi ta tsakani su kuwa 'yan wasan City suka dunga tafa musu saboda sune suka lashe Premier League na bana tun saura wasa bakaw-bakawi a kammala kakar bana.
Tun farko ba a tsara buga karawar a Etihad ba don ana gudun magoya bayan kungiyoyin biyu za su iya zuwa su tsaya a wajen ginin filin don sanin abinda ke faruwa.
Daga baya ne aka amince Manchester City ta karbi bakuncin wasan a Etihad.
Tun da aka koma ci gaba da wasannin bana ba 'yan kallo don gudun yada cutar korona.

Asalin hoton, Man City
Nasarar da Sheffield ta yi ya sa ta koma ta bakwai a kan teburi, saboda haka Arsenal ta yi kasa zuwa mataki na takwas.

Asalin hoton, Reuters
Harry Kane ya ci kwallo a dukkan kungiyoyin Premier 29 da ya fuskanta, kuma shi ne dan wasan da ya buga karawa da kungiyoyi da dama ya kuma zura wa kowacce kwallo.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Babu wanda zai ce maka Burnley za ta yi kan-kan-kan da Tottenham a hada maki a gasar Premier League.
Sai gashi ita ma tana neman gurbin shiga gasar zakarun Turai ta badi.

Asalin hoton, BBC Sport
Saura wasa bakawi a karkare gasar Premier League ta bana, tuni Liverpool ta lashe kofin kuma ita ce ta yi hakan cikin sauri a tarihi.
Wannan ne na farko da Liverpool ta lashe kofin Premier tun bayan shekara 30 kuma na 19 jumulla.
A wasa 11 da Manchester City ta buga ana fara zura mata kwallo a kakar bana -ta samu karin wasa uku fiye da kaka biyu da ta buga. Ta kuma yarda maki 30 a kaka biyu da ta wuce shi ne ta yadda maki 30.