Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Man City ta ragargaji Liverpool wadda ta ci Premier na bana

Wannan shafi ne kai tsaye da ke dauke da labarin wasanni a karawar Manchester City da Liverpool da na Real Madrid da Getafe.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Canjin dan wasa - Man City 4-0 Liverpool

    Liverpool' ta yi canji na karshe in da Takumi Minamino ya maye gurbin Sadio Mane.

  2. Karo na biyu da Manchester City za ta yi canji

  3. An je hutu - Real Madrid 0-0 Getafe

  4. Man City 4-0 Liverpool

    Karon farko da aka ci Liverpool kwallo hudu a gasar Premier tun bayan Satumbar 2017 da aka zura mata kwallo 5-0 a kuma Etihad a hannun Manchester City.

  5. Karin lokaci - Real Madrid 0-0 Getafe

    An yi karin lokaci a wasan Real Madrid da Getafe har yanzu dai ba ci kila sai an dawo zagaye na biyu ne Real za ta yi kokarin samun maki ukun.

  6. Man City 4-0 Liverpool

    City sai kara sa kaimi take yi hala so take ta kunyata Liverpool wacce ta karbe kofin Premier League a hannun kungiyar Etihad da take da shi na bara.

    Raheem Streling da De Bruyne kwallo hudu bai ishesu ba sai kara shiga bayan Liverpool suke yi.

  7. Real Madrid 0-0 Getafe

    Har yanzu ba ci a gasar La Liga kuma an kusan yin hutu.

  8. An ci kwallo - GOAL - Man City 4-0 Liverpool, Raheem Sterling

  9. Canji dan wasa - Man City 3-0 Liverpool

    Liverpool ta sa 'yan wasa biyu ta fitar da Roberto Firmino da Georginio Wijnaldum inda Naby Keita da kuma Divock Origi suka maye gurbinsu.

  10. Canji dan wasa - Man City 3-0 Liverpool

    Riyad Mahrez ya shiga fili ya maye gurbin Gabriel Jesus yana da minti 30 da zai nuna mana abinda zai yi..

  11. Real Madrid ta yi canji

  12. Man City 3-0 Liverpool

    Liverpool ta sanmu bugun tazara tun farko ta dauka fenariti ne sai da aka je VAR ta fayyace cewar bugun tazara ne.

  13. Man City 3-0 Liverpool

    Ederson ya yi kokari ya tare kwallo ko da yake ta fice daga hannunsa amma ba wani hadari dai.

  14. Man City 3-0 Liverpool

    Gomez sai ya yi da gaske wajen tsare Sterling a wasan nan.

  15. Real Madrid 0-0 Getafe

    Har yanzu ba ci ko Real za ta bai wa Barcelona tazarar maki hudu ko kuma zai zauna a maki daya tal?

  16. 'Yan wasan Real 11 da aka fara wasa da su

  17. Real Madrid da Getafe

  18. Man City 3-0 Liverpool

    An yi hutu da jan aiki a gaban Liverpool a minti 45 da za a buga gaba.

  19. Man City 3-0 Liverpool

    Daf ake da a je hutun rabin lokaci kuma City ta zura kwallo uku a raga.

    Ba wanda zai faga maka cewar City za ta dura kwallo har uku haka.

  20. An ci kwallo - Man City 3-0 Liverpool, Phil Foden