Kamfanin jirgin saman Qantas zai kori ma'aikata 6,000
Kamfanin jiragen saman Qantas ya ce zai kori mutum 6,000 daga aiki a wani bangare na kokarin da yake yi na magance tabarbarewar tattalin arzikin da ya fada sanadin annobar korona.
Adadin ya yi daidai da kashi daya cikin biyar na ma'aikatan kamfani gabanin barkewar annobar. A watan Maris ya bai wa kashi 80 na ma'aikatansa hutu saboda cutar korona.
Kamfanin na kasar Australia ya ce dakatar da sufurin jiragen sama ta yi matukar gigita tattalin arzikinsa da hanyoyin samun kundin shigarsa.
Makon jiya, gwamnatin Australia ta ce iyakokinta za su ci gaba da kasancewa a rufe watakila zuwa baɗi.
Hakan ne ya sa Qantas ya soke dukkan zirga-zirgarsa zuwa watan Oktoba, ban da ta jiragen da za su je New Zealand.