'Yan sanda a Abuja babban birnin Najeriya sun killace sakatariyar jam'iyyar APC ta kasa, sannan suka hana mukaddashin sakataren jam'iyyar ta kasa Waziri Bulama shiga ofishin.
Wani makusancin sakataren wanda yake tare da shi lokacin da lamarin ya faru ya ce, 'yan sanda sun hana sakataren shiga ofishin yayin da ya je domin gudanar da aiki da safiyar Alhamis din nan.
Tun da farko sai da 'yan sandan suka fitar da duka mutanen da suke cikin sakatariyar sannan suka killace ta.
Har kawo yanzu babu wata sanarwa daga rundunar 'yan sandan Najeriya kan lamarin. Sai dai kafofin watsa labaran kasar sun wallafa wasu hotuna da suka ce na 'yan sanda ne da suka killace sakatariyar ta APC dake unguwar Wuse a Abuja.
'Yan sandan sun shaidawa Waziri Bulama cewa sun dauki matakin ne saboda sun samu bayanan sirri dake nuna cewa za a iya samun matsalar tsaro a ofishin.
Duk yunkurin da Wazirin Bulama ya yi na kokarin ganin ya shiga ofishin ya ci tura, don haka ala tilas ya juya ba tare da samun damar shiga sakatariya ba.
Lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun rikicin shugabanci a jam'iyyar mai mulkin Najeriya, bayan Shugaba Buhari ya goyi bayan Viictor Giadom a matsayin shugaban riko na jam'iyyar ta APC.