'Yan sanda na gudanar da bincike a kusa da fadar shugaban kasar Kamaru

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya, Halima Umar Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

    To masu bin mu a wannan shafi a nan muka kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku kai tsaye.

    Sai kuma ku tara gobe idan Allah Ya kai mu da misalin karfe 9 na safe inda za mu zo muku da sabbin bayanai kan abin da ke faruwa a duniya idan Allah Ya kai mu.

    Kuna iya ziyartar shafinmu na BBC Hausa don karanta wasu labaran.

    Sannan a yanzu haka muna kawo muku labarai kai tsaye na wasan Gasar Premier da ake fafatawa, sai ku latsa nan.

    A madadin Nasidi Adamu Yahaya da Umar Mik'ail da Mustapha Kai, ni Halima Umar Saleh nake cewa mu kwana lafiya.

  2. Trump ta yi nasara a Kotun Koli kan ikon mayar da 'yan ci rani kasashensu

    Gwamnatin shugaba Donald Trump ta yi nasara a Kotun koli, bayan da ta yanke hukuncin cewa gwamnatin na da ikon maida yan cirani da suka shigo kasar ba bisa ka'ida ba zuwa kasashensu.

    Matakin wanda alkalai bakwai suka amince, yayin da biyu kacal suka ki amincewa na nufin Mr Trump na da damar sallamar yan ciranin ba tare da wani cikas ba.

    Haka ma hukuncin ya shafi masu neman mafaka.

    Tun farko an shigar da kara ne kan wani manomi dan kasar Sri Lanka, da aka ki bashi mafaka a Amurka duk da kwakkwaran dalilin da yake dashi na neman mafakar.

  3. 'Yan sanda na gudanar da bincike a kusa da fadar shugaban kasa na Kamaru

    Jami’an ‘yan sanda da Jandarma na gudanar da bincike a unguwannin da suka yi wa fadar Shugaban kasa a Yaounde da’ira.

    Binciken ya shafi wasu motoci da suke sintiri a kan tituna harma da wasu mutane da suke zirga-zirga dauke da wasu abubuwa a hannayensu.

    Hakan na gudana ne bisa ga umurnin Mukaddashin babban jami’in ‘yan sanda na birnin Yaounde da kewaye.

    Wannan matakin ya biyo bayan tashin da wasu ababan fashewa biyu da suka yi a wasu unguwanni na birnin Yaounde.

    Lamarin da ya kai ga ana zargin shirya wani harin da ‘yan ta’adda ke shirin yi.

    Ku saurari rahoton Babala a kasa:

    Bayanan sautiRahoton Babalala kan binciken da 'yan sanda ke yi a kusa da fadar shugaban kasa
  4. Babu tabbas kan samun riga-kafin cutar korona - Shugaban WHO

    Tedros

    Asalin hoton, EPA

    Shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya WHO ya ce babu tabbas cewa masana kimiyya za su iya samar da ingantaccen riga-kafin cutar Covid-19.

    Dr Tedros Ghebreyesus ya shaida wa kwamitin lafiya na Kungiyar Tarayyar Turai a ranar Alhamis cewa ko da an samar da riga-kafin, to ba zai samu ba a cikin shekara daya.

    ''Zai yi matukar wahala a ba da tabbacin cewa za mu samu riga-kafi,'' kamar yadda Dr Tedros ya shaida wa 'yan majalisar dokokin EU ta taron da suka yi ta bidiyo.

    ''Ba mu taba samun riga-kafin cuatr korona ba. Don haka wannan zai kasance na farko idan aka gano.''

    Riga-kafi na taimaka wa garkuwar jiki ta gane tare da yakar kwayoyin cuta. Ana daukar su a matsayin hanyoyi mafi inganci na kare mutane daga kamuwa da cutar korona daga yaduwa.

  5. 'Shirin Isra'ila na mamaye Gabar Yamma da Kogin Jordan gayyatar yaki ne da Falasdin'

    Israel

    Asalin hoton, AFP

    Kungiyar mayakan Hamas da ke Gaza sun yi gargadin cewa shirin da Isra'ila ke yi na mamaye Gabar Yamma da Kogin Jordan gayyatar yaki ne da Falasdin.

    Mai magana da yawun kungiyar Al-Qassam Brigades ya ce matsawar Isra'ila ta ci gaba to ko za ta yabawa aya zaki.

    Firanministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya ce shirin mamayar wanda zai hada da kwarin Jordan zai fara ne a farkon watan Yuli mai kamawa.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ja kunnen Isra'ila da kada ta kuskura ta aikata hakan, don ya saba wa dokar kasa da kasa.

  6. Waƙoƙin Michael Jackson da suka fi burge ku shekara 11 bayan mutuwarsa

    Michael Jackson

    A ranar Alhamis 25 ga watan Yuni ne tauraron mawaƙi Michael Jackson ya cika shekara 11 da mutuwa bayan shekara kusan shekara 40 yana jan zarensa a fagen waƙa.

    Mawaƙin ɗan Amurka ya karaɗe lungu da saƙo na duniya da waƙoƙinsa, waɗanda da ya fara tun bai balaga ba kuma da alama har duniya ta tashi ba za a manta da su ba.

    Michael Jackson ya rasu ranar 25 ga watan Yunin 2009 yana da shekara 49 bayan ya sha wasu kwayoyi fiye da kima, a cewar rahotanni.

    Daga cikin irin ra'ayoyin da kuka bayyana mana, mun tsakuro irin waƙoƙin da suka burge ku kuma kuke tuna shi da su.

    Waƙar They Don't Care About Us ta yi fice matuƙa tun bayan sakinta a shekarar 1995 kuma samari a ƙasar Hausa musaman waɗnda ba su ƙware a Ingilishi ba kan ba ta sunaye iri-iri.

    Wani mai bibiyarmu mai suna @bukarkundila a shafin Twitter ya ce shi waƙar da ta fi burge shi ita ce "awara da yaji da ɗumi-ɗuminta", yana nufin "They Don't Care About Us".

  7. Labarai da dumi-dumi, Tsohon gwamnan Oyo Ajimobi ya rasu

    .

    Asalin hoton, @AAAjimobi

    Tsohon gwamnan jihar Oyo Isiaka Abiola Ajimobi ya rasu a yau Alhamis bayan ya yi fama da rashin lafiya.

    Wani makusancin marigayin ne ya tabbatar wa BBC labarin rasuwar tasa.

    Rahotanni sun ce tsohon gwaman ya rasu ne a wani asibiti da ke Legas.

    Tun a makon da ya gabata ne dai aka yi ta raɗe-raɗin cewar Ajimobi ya rasu.

    Kafin rasuwarsa, ya jagoranci jihar Oyo a matsayin gwamna tun daga 2011 zuwa 2019.

  8. Jamus da Faransa za su ƙara yawan kuɗin da suke bai wa WHO

    Ƙasashen Faransa da Jamus sun bayyana cewa za su ƙara kason da suke bai wa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, makonni kaɗan bayan Amurka ta bayyana janyewarta daga tallafa wa hukumar.

    Jamus ta yi alƙawarin bai wa hukumar fam miliyan 500 a wannan shekarar., Faransa kuma ta ce za ta bayar da fam miliyan 140.

    Duka ƙasashen biyu sun ce ba wai don shugaba Trump ya ce ya janye hannunsa daga tallafa wa hukumar bane ya sa suka ƙara wannan kason.

    Sai dai sun ƙara jaddada amfanin wannan hukuma, inda suka ce hukumar na taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da annobar korona.

    ..

    Asalin hoton, EPA

  9. An kwaso 'yan Najeriya 167 daga Afrika Ta Kudu – Onyeama

    'Yan Najeriya 167 na hanyar komawa gida daga Afrika Ta Kudu.

    Ministan harkokin wajen ƙasar Geoffrey Onyeama ne ya wallafa hakan a Shafinsa na Twitter inda ya ce tuni 'yan Najeriyar suka baro filin jirgin O.R Tambo da ke Johannesburg zuwa Abuja.

    Ko a kwanakin baya cikin wannan watan na Yuni sai da aka dawo da wasu 'yan ƙasar daga ƙasashen Masar da Indiya.

    Ya bayyana cewa fasinjoji 45 za su sauka Abuja cikin 167 da aka kwaso, sa'annan a wuce da sauran 122 zuwa Legas.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Labarai da dumi-dumi, An amince da maganin korona na farko a Turai

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar da ke sa ido a harkar lafiya a nahiyar Turai ta amince da wani magani mai suna Remdesivir, domin amfani da shi wurin magance cutar korona.

    A shekarun baya dai an yi amfani da maganin wurin yaƙi da cutar Ebola, a halin yanzu kuma, ana nan ana ci gaba da gwajin maganin domin amfani da shi wurin yaƙi da cutar korona.

    Hukumar da ke sa ido a harkar lafiya a nahiyar ta Turai ta amince a fara amfani da maganin a duka ƙasashen Turai.

    Za a fara amfani da maganin ne kan 'yan shekaru 12 zuwa sama masu fama da nimoniya da kuma waɗanda suke buƙatar a saka musu na'urar taimaka wa numfashi.

    Sai dai kafin a fara amfani da maganin, sai Hukumar Tarayyar Turai ta bayar umarnin ƙarshe sa'annan.

  11. Sanarwa

    ..

    Ku kasance da mu anjima, inda za mu tattauna da shahararren mawaƙin Hausa Ado Gwanja. Ku aiko mana da tambayoyinku a shafinmu na Instagram ko Twitter har ma da Facebook.

  12. Korona ta sake kashe mutum 149 a Birtaniya

    Rahotanni daga Birtaniya na cewa ƙarin mutum 149 sun sake mutuwa sakamakon cutar korona a faɗin ƙasar.

    A halin yanzu jumullar mutum 43,230 cutar ta kashe a ƙasar.

    Mutum 1,118 aka samu sun sake kamuwa da cutar bayan an yi wa mutum 167,023 gwaji.

    A alƙaluman da aka samu a yau, an samu raguwa a mace-mace a ƙasar idan aka haɗa da jiya da aka samu 154.

  13. Hotunan taron kwamitin gudanarwa na APC

    ..

    Asalin hoton, @TolaniAlli

    ..

    Asalin hoton, @TolaniAlli

    ..

    Asalin hoton, @TolaniAlli

  14. China ta bai wa 'yan sandan Najeriya tallafin kayan yaƙi da korona

    Yan Sandan Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Police

    Cibiyar Kasuwanci ta China a Najeriya ta bai wa rundunar 'yan sandan Najeriya tallafin kayayyakin kare kai daga cutar korona, abin da Sufeto Janar na 'yan sanda Mohammed Adamu ya bayyana da cewa "abin koyi ne".

    Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Alhamis ta ce cibiyar ta bai wa 'yan sanda tallafin ne sakamakon rawar da suke takawa wurin yaƙi da annobar ta korona a Najeriya.

    Frank Mba wanda shi ne kakakin rundunar, shi ne kuma ya karɓi tallafin a madadin Sufeto Janar Mohammed Adamu a hedilkwatar rundunar da ke Abuja babban birni ƙasar ranar Alhamis.

    Kayayyakin sun haɗa da takunkumi guda 40,000, da rigunan kare kai guda 500 da kuma na'urar tantance zafin jikin mutum.

    Mohammed Adamu ya sha alwashin za a raba kayan ga 'yan sandan da suke bakin aikin tabbatar da dokokin kariya daga cutar.

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  15. 'Yan fashin teku sun sace ma'aikatan jirgin ruwa a Benin

    'Yan fashin teku sun sace akalla ma'aikatan jirgin ruwan kamun kifi shida a gabar tekun Benin ranar Laraba.

    Biyar daga cikin wadanda aka sace 'yan kasar Koriya ta Kudu ne, yayin da dayan kuma dan kasar Ghana ne, a cewar wasu bayanai da kafofin watsa labarai suka ambato ma'aikatar wajen Koriya ta Kudu tana bayyanawa.

    Kamfanin da ke lura da lafiyar sufurin jiragen ruwa na duniya Dryad Global ya ce gani na karshe da aka yi wa jirgin ruwan mai gudun tsiya mai suna Panofi Frontier da ke dauke da tutar kasar Ghana, shi ne a an hanyarsa ta zuwa yankin tekun Najeriya bayan an sace mutanen.

    Kafofin watsa labaran Koriya ta Kudu sun bayyana cewa ma'aikatar wajen kasar ta kafa kwamitin gaggawa da zai yi aiki wajen ganin an kubutar da 'yan kasarta.

    Gabar tekun Guinea ce wuri mafi hatsari da 'yan fashin teku suke cin karensu babu babbaa a duniya, a cewar Hukumar kula da safarar jiragen ruwa ta duniya.

  16. Kongo ta ce ta kawo ƙarshen cutar Ebola a arewacin ƙasar

    An kawo ƙarshen annobar cutar Ebola a arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, wadda ta ɓarke tun a Agustan shekarar 2018, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

    WHO ta bayyana haka ne a shafin Twitter, inda ta ambato wani ministan gwamnatin ƙasar yana bayyana hakan.

    Garin Ituri be cibiyar cutar amma akwai masu ɗauke da ita a Arewaci da kuma Kudancin Kivu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Sai dai an samu ɓarkewar wata annobar - irinta ta 11 kenan a ƙasar - a yammacin ƙasar.

    An sanar da samun mai ɗauke da cutar ranar 1 ga watan Yuni.

    Kafin a bayana kawo ƙarshen annoba, sai an shafe kwana 42 ba tare da samun mai ɗauke da ita ba sannan kuma sai waɗanda suka kamu sun warke kuma an sallame su.

    A cikin wata 23 da aka shafe ana annobar a Kongo, mutum 3,463 ne suka harbu da ita sannan 2,280 suka mutu.

  17. Labarai da dumi-dumi, An nada Mai Mala Buni shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC

    An nada gwamnan jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya Mai Mala Buni shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC.

    Kwamitin gudanarwa na kasa na jam'iyyar ne ya dauki wannan mataki bayan da ya soke kwamitin rikon APC din a wani taro da ya gudanar a ranar Alhamis da rana.

    Hakan ya biyo bayan shawarwarin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar ne, kamar yadda mai taimaka masa kan shufakan sada zumunta Bashir Ahmed ya fada a shafinsa na Twitter.

  18. An hana sakataren APC shiga ofishin jam'iyyar

    'Yan sanda a Abuja babban birnin Najeriya sun killace sakatariyar jam'iyyar APC ta kasa, sannan suka hana mukaddashin sakataren jam'iyyar ta kasa Waziri Bulama shiga ofishin.

    Wani makusancin sakataren wanda yake tare da shi lokacin da lamarin ya faru ya ce, 'yan sanda sun hana sakataren shiga ofishin yayin da ya je domin gudanar da aiki da safiyar Alhamis din nan.

    Tun da farko sai da 'yan sandan suka fitar da duka mutanen da suke cikin sakatariyar sannan suka killace ta.

    Har kawo yanzu babu wata sanarwa daga rundunar 'yan sandan Najeriya kan lamarin. Sai dai kafofin watsa labaran kasar sun wallafa wasu hotuna da suka ce na 'yan sanda ne da suka killace sakatariyar ta APC dake unguwar Wuse a Abuja.

    'Yan sandan sun shaidawa Waziri Bulama cewa sun dauki matakin ne saboda sun samu bayanan sirri dake nuna cewa za a iya samun matsalar tsaro a ofishin.

    Duk yunkurin da Wazirin Bulama ya yi na kokarin ganin ya shiga ofishin ya ci tura, don haka ala tilas ya juya ba tare da samun damar shiga sakatariya ba.

    Lamarin na zuwa ne a dai dai lokacin da ake ci gaba da samun rikicin shugabanci a jam'iyyar mai mulkin Najeriya, bayan Shugaba Buhari ya goyi bayan Viictor Giadom a matsayin shugaban riko na jam'iyyar ta APC.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Juventus tana son ɗauko Aubameyang, Koulibaly zai koma Manchester City

    Juventus ta bi sahun wasu kungiyoyi wajen zawarcin kyaftin din Arsenal da Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 31. Da maBarcelonadaInter Milansuna son dauko dan wasan.(Le10 Sport - in French)

    Ana sa ran dan wasan Napoli da Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, zai komaManchester Citya bazarar nan bayanLiverpoolta mayar da hankalinta zuwa wani dan wasan.(Express)

    Manchester United ce kungiya daya tilo da dan wasan Borussia Dortmund da Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20 zai zabi komawa a bazara. Sai dai Dortmund ba za ta sallama shi ba a kan ƙasa da £118m.(Bild - in German)

    Dan wasan Brazil Fred, mai shekara 27, yana son sabunta kwangilarsa a Manchester United.(Sun)

    Pierre-Emerick Aubameyang

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Mai shekara 114 'ya warke daga cutar korona' a Ethiopia

    Wani dattijo mai shekara 114 dan kasar Habasha ya warke daga cutar korona, a cewar wani sakon Facebook da Dr Yared Agidew, likitan asibitin da aka kwantar da mutumin a Addis Ababa, ya wallafa.

    Ana kallon mutane masu fiye da shekara 80 a matsayin wadanda suka fi kasadar rashin warkewa idan suka kamu da cutar korona.

    Sai dai sakon da Dr Yared ya wallafa da harshen Amharic ya ce mutumin "ya warke sarai. Yanzu yana cikin koshin lafiya."

    Mutum kusan 5,000 ne suka kamu da cutar korona a Habasha inda ta yi ajalin mutum 75.