Real Madrid ta koma matakinta na daya a teburin La Liga

Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni da karawar da Real Madrid ke karbar bakuncin Real Mallorca da sanar da ku wainar da ake toyawa a fanni wasanni.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Sai da safenku

    Nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara a shirinmu na ranar Alhamis a fafatawa tsakanin Chelsea da Manchester City.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW TW ke muku fatan alheri.

    Ku tara a shirin radio da safe da hantsi ranar Alhamis don jin labaran wasanni.

  2. Real Madrid 2-0 Mallorca

    An tashi wasa Real Madrid ta samu maki uku da kwallo biyu a raga ta koma ta daya a kan teburin La Liga.

    Barcelona ta koma ta biyu.

  3. Real Madrid 2-0 Mallorca

    Dan wasan Real Mallorca Luca Romero ya zama matashin dan wasa da ya buga gasar La Liga mai shekara 15 da kwana 219.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  4. Wasannin Premier League da aka buga ranar Laraba

    Kai tsaye

    Asalin hoton, BBC Sport

  5. Canji - Real Madrid 2-0 Mallorca

    Real Madrid ta saka Brahim da Mariano sun maye gurbin Vinicius Jr da kuma Karim Benzema.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  6. Atalanta 3-2 Lazio

    Sakamako mai kyau a gasar Serie A bayan da aka zura wa Atalanta kwallo biyu ta farke su ka karawa Lazio na uku,

    Kuma Juventus na daf da lashe kofin na Italiya na tara a jere.

    Yanzu ta bai wa Lazio tazarar maki hudu kenan.

  7. Real Madrid 2-0 Mallorca

    An bayar da lokaci a dan hutu, wato da an yi minti 30 ne ake bayar da dama a sha ruwa sannan a ci gaba da wasa.

  8. Wolves 1-0 Bournemouth

    Wolverhampton ta yi nasarar doke Bournmouth a wasan mako na 31 a gasar Premier League da suka fafata a yammacin nan.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Reuters

  9. Lokaci na kara kurewa Norwich City

    Norwich City ta sha kashi a karo na uku a jere a gasar Premier League tun da aka ci gaba da wasanni.

    Norwich ta yi rashin nasara a gida da ci 1-0 a hannun Everton a wasan mako na 31 da suka fafata a Carrow Road ranar Laraba.

    Norwich ce ta karshe a kasan teburi za ta koma buga Championship a kakar badi kenan.

    Kai saye

    Asalin hoton, EPA

  10. An ci kwallo - Atalanta 3-2 Lazio, José Luis Palomino

    Ta faru ta kare Lazio na kokarin kara kwallo sai Atalanta ta ci na uku, kuma mai tsaron bayan Lazio ne ya bar Jose Luis Palominoto ya sa kai a kwallon da aka bugo daga kwana ta fada raga daga yadi na shida.

  11. Real Madrid 2-0 Mallorca

    Real Madrid ta sa Toni Kroos ya canji Eden Hazard.

    Mallorca ta yi canji uku.

  12. Real Madrid 2-0 Mallorca

    Wannan ne karon farko da Sergio Ramos ya ci kwallo takwas a gasar La Liga yana kuma kaka ta 18 da yake buga wasannin.

  13. Real Madrid 2-0 Mallorca

    Sergio Ramos shi ne na biyu a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a bana da guda 10, illa Karim Benzema da ke gabansa da ya ci 21 da ya ci wa kungiyar a shekara nan.

  14. Liverpool 4-0 Crystal Palace

    Mohamed Salah da Sadio Mane kowanne ya ci kwallo a karawa da Crystal Palace.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  15. An ci kwallo - Real Madrid 2-0 Mallorca, Sergio Ramos

    Kyaftin din Madrid Sergio Ramos ya samu bugun tazara mai kyau ya kuma yi na kwararru inda kwallo ya haura katangar da Mallorca ta yi ya fada raga.

    Real Madrid ta koma ta daya a kan teburin La Liga.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Maki biyu Liverpool ke bukata

    Ko magoya bayan Liverpool za su tuna kofin karshe da suka daga.

    Shekara 30 da yawa fa ga wadanda ke da yawan rai.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, BBC Sport

  17. An ci kwallo - Atalanta 2-2 Lazio

    An jika wa Lazio aiki, bayan da Atalanta ta farke kwallo na biyu.

    Tun farko aka zura mata kwallo biyu daga baya ta farke.

    Kafin wannan wasan Juventus ta bai wa Lazio tazarar maki hudu, saboda haka tana bukatar cin wannan karawar tazarar ta koma daya tal.

  18. Liverpool 4-0 Crystal Palace

    An tashi wasan da Liverpool ta doke Crystal Palace 4-0.

    Liverpool za ta dauki kofin Premier na farko tun bayan shekara 30.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, BBC Sport

  19. Real Madrid 1-0 Mallorca

    Bugun tazara da Real Mallorca ta samu ta kuma buga ta nufi raga amma kuma Thibaut Courtois ya rike gam.

  20. David Luiz zai ci gaba da zama a Arsenal shekara daya

    Mai tsaron bayan Arsenal, David Luiz ya amince da yarjejeniyar shekara daya domin ya ci gaba da taka leda a kungiyar.

    Luiz, dan wasan tawagar Brazil, mai shekara 33, ya koma Gunners daga Chelsea a bara, an kuma yi masa jan kati a wasan da Manchester City ta doke Arsenal 3-0 a gasar Premier da aka ci gaba.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images