Tana kaka ta biyu karkashin koci Gaizka Garitano mutumin da ya fitar da Barca a Copa del Rey a watan GFabrairu.
Athletic ta kai wasan karshe a gasar da za ta buga da Real Sociedad karawar hamayya, sai dai bullar cutar korona ta sa aka dakatar da buga wasan karshen.
Sai dai kuma Athletic ta yi rashin nasara a wasa hudu da ta buga a La Liga a cikin watan Fabrairu.amma ta yi biyar tun daga nan ba a doke ta ba, hakan ya sa take ta tara a kan teburi tana kuma neman gurbin shiga gasar Europa League a badi.
Sakamakon wasa biyar da ta buga baya a La LigaAthletic 1-0 VillarrealValladolid 1-4 AthleticAthletic 1-1 Atlético MadridEibar 2-2 AthleticAthletic 1-0 Real Betis
Wadanda ke kan gaba a ci mata kwallaye a Lik da sauran wasanni sun hada da Raúl García(10);Iñaki Williams(9);Iker Muniain(6);Yuri Berchiche(6)