Nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara a wasan Laraba tsakanin Real Madrid da Real Mallorca.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke muku fatan alheria.
Wannan shafi ne kai tsaye da ke dauke da labarin wasa a gasar La Liga tsakanin Barcelona da Athletic Bilbao da wasu labaran wasanni da suke gudana ranar Talata.
Mohammed Abdu
Nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara a wasan Laraba tsakanin Real Madrid da Real Mallorca.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW ke muku fatan alheria.
Dan kwallon Manchester United, Scott McTominay, zai ci gaba da taka leda a Old Trafford zuwa 2025 da yarjejeniyar za a iya tsawaita masa ita.
An yi wa dan kwallon wannan gatan, bayan rawar da yake takawa tun daga lokacin da ya fara wasa a kungiyar karkashin tsohon koci, Jose Mourinho.
Dan wasan tawagar Scotland mai shekara 23 ya fara buga wa United tamaula a cikin watan Mayun 2017 a fafatawa da Arsenal.
McTominay wanda aka haifa a Lancaster ya buga wasa 75 ya ci kwallo shida a gasar Premier League har da ta biyu da ya zura a ragar Manchester City a watan Maris.
Manchester United wacce take ta biyar a teburin Premier za ta karbi bakuncin Sheffield United ranar Laraba.
United ta buga 1-1 da Tottenham a gasar Premier tun da aka koma ci gaba da wasannin shekarar nan,
A cikin watan Maris aka dakatar da gasar Premier League don gudun yada cutar korona.

Asalin hoton, Getty Images
Raunin da Sergio Aguero ya yi a karawar da Manchester City ta doke Burnley da ci 5-0 ranar Litinin "ba shi da kyawun gani", a cewar kocin kungiyar Pep Guardiola.
An tilasta wa dan wasan fita ana dab da tafiya hutun rabin lokaci bayan Ben Mee ya doke shi abin da ya kai ga bai wa City bugun fenareti wanda ya sa ta ci kwallonta ta biyu.
Guardiola ya bayyana cewa dan Argentina ya kwashe kusan wata daya yana fama da ciwon gwiwa.

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta koma ta daya a kan teburi kafin Real Madrid ta buga da Mallorca ranar Laraba.
Lionel Messi.ya buga kwallo ta bugi yan wasan da suka yi katanga.
Bugun tazara ga Barcelona ko ita ce na 700 da Lionle Messi mai ci ne?
Arturo Vidal ne ya bayar da kwallo a kyauta sai dan wasan Athletic ya dauka wanda Ivan Rakitic ya kai shi kasa hakan ya sa aka ba shi katin gargadi.
Lionel Messi iya kusan cin kwallo na 700. Shi da Ansu Fati ya jawo kwallo daga hagu ya bai wa dan wasan Argentina wanda ya buga daga yadi na 20 amma ta yi fadi da yawa.
Gerard Pique na yake yana rike kafarsa kila ya gama buga wannan wasan kenan.
Bugun tazara daga yadi na 30 kuma wannan karon Lionel Messi ya buga sai dai ta bugi 'yan wasan da suka yi katanga.
Barcelona ta fitar da Luis Suarez ta maye gurbinsa da matashi Martin Braithwaite.
Athletic ta samu bugunh tazara daga gefe ta kuma buga inda mai tsaron baya Gerard Pique da Nelson Semedo suka ci kasuwar sama..
Damar da Lionel Messi ya samu bayan da ya buga kwallo da karfi ta nufi raga daga baya ta bude ta yi waje. kar ku manta ya ci kwallo 699 a tarihin tamaularsa a Barcelona har da 70 da ya ci wa tawagar Argentina yana dai neman daya lissafi ya cika 700.
shin ko zai ci a wannanwasan kuwa?
Athletic ta yi canji na karshe inda Raul Garcia ya maye gurbin Oihan Sancet.
An dan bayar da lokaci asha ruwa suna kuma shirin ci gaba da taka leda.
Wannan ne karo na 250 da Lionel Messi ya bayar da kwallo aka zura a raga in ji wani kamfani mai tara bayanai da ake kira Gracenote.
Wannan ne karon farko da Ivan Rakitic ya ci kwallo a gasar La Liga a bana.
Rabon da ya ci tun karawar El Clasico ranar 2 ga watan Maris na 2019.
Barcelona ta shiga gaba inda Ivan Rakitic ya samu kwallo bayan da aka tare kwazon da .Lionel Messi shi kuwa nan da nan ya buga ta kuma fada raga yanzun nan ya shiga karawar.
Hankalin Barcelona zai dan yi sanyi kena.
Ansu Fati ina ta sa kwazo inda ya ja kwallo a guje tun daga tsakiya ya kusan cimma mai tsaron raga wanda ya fito a guje ya cire ta.
Ansu Fati ya samu kwallo ya sa kai amma ta haura saman raga.
Matashin yana da kyau a sama yana da tsawon kafa biyar da inci 10.