Everton 0-0 Liverpool
Tun lokacin da Jurgen Kloop ya zama kocimn Liverpool. Everton ta kasa doke shi a wasan Premier League a wasan hamayya na Merseyside derbies a kuma Goodison Park.
Ko wannan karon za su ci wasan?
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke dauke da labaran wasanni da ake gudanarwa a karshen mako don sanar da ku irin wainar da ake toyawa.
Mohammed Abdu
Tun lokacin da Jurgen Kloop ya zama kocimn Liverpool. Everton ta kasa doke shi a wasan Premier League a wasan hamayya na Merseyside derbies a kuma Goodison Park.
Ko wannan karon za su ci wasan?
Liverpool ta samu bugun tazara a wuri mai kyau. Trent Alexander-Arnold da kuma Jordan Henderson suna tsaye kusa da kwallon an kuma buga amma ba ta yi kyau ba .
Wuri fayau ba kowa Dominic Calvert-Lewin na jan kwallo zuwa gaba har sai da Liverpool ta taka masa burki.
Har yanzu Liverpool ba su fara sa kwazo ba kamar yadda aka san suna yi a kakar bana.
Wannan ne wasansu na farko tun bayan kwana 102.
Everton na sa kaimi.
suna amfani da kwallon yadda ya kamata suna kuma rike ta kamar yadda suka tsara tun fara wasa.
Lallai Richarlison ya shirya wa karawar nan sai motsa wa yake a cikin fili.
Trent Alexander-Arnold ya kai kro ta farko mai kyau amma kwallon da ya buga sai ta je wajen Jordan Pickford wanda ya rike cikin sauki.
Everton nan da nan itama ta kai kora ta bangaren Richarlison wanda ya yi kokari ya kai kwallo cikin hatsari amma babu abinda ya faru.
Ruwa ake ta yi a Goodison Park
Har yanzu wasan bai zauna ba a karon farko Jordan Pickford ya taba kallo.
Sai da aka yi minti daya tsam kan a take wasa don tunawa da wadanda cutar korona ta kashe da kuma goyon bayan zanga-zanga da ake yi a Amurka ta kashe bakar fata.
Wannan ne karo na 236 da Everton da Liverpool za su fafata a wasan hamayya da ake kira Merseyside derby kuma ba tare da 'yan kallo ba.
Everton ta yi wasan Premier League uku ba tare da yin nasara ba, amma ba a doke ta ba a wasa bakwai da ta yi a gida ta ci hudu da canjaras uku.
Ko za ka tuna kana ina ko mai kake yi kwana 3,535 da suka wuce?
A wancan lokacin ne Tim Carhill da Mikel Arteta suka ci Liverpool 2-0 a wasan hamayya a Goodison Park, shi ne karo na karshe da Everton ta ci Liverpool a karawar hamayya ta Merseyside.
Tun daga 17 ga watan Oktoban 2010 sun fafata a tsakaninsu sau 21, Everton ta yi rashin nasara a karawa 11 da canjaras 10.
Salah na benchi
Liverpool za ta je gidan Everton a ci gaba da gasar Premier League sai dai Mohamed Salah na benci tare da Georginio Wijnaldum.
A karon farko matashin dan wasa mai shekara 19, Anthony Gordon wanda aka haifa a Liverpool zai yi Everton wasa.
Jama'a barkanmu da kasancewa a labaran wasanni kai tsaye don sanar da ku wainar da ake toyawa a karshen mako.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW zan gabatar muku da shirin.
Za ku iya bayar da gudunmawa ko tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko a Twitter a BBC Hausa.