Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An raba maki tsakanin Everton da Liverpool

Wannan shafi ne da ke dauke da labaran wasanni da ake gudanarwa a karshen mako don sanar da ku irin wainar da ake toyawa.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Nan na kawo karshen shirin da fatan za ku tara a wasan da Manchester City za ta buga ranar Litinin.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper ke muku fatan alheri.

    Ku kasance da BBC Hausa ta Radiyo a gobe Juma'a a labarin wasanni da safe da kuma Hantsi tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skeeper TW.

  2. Wane wasan ya fi kayatarwa ranar Lahadin?

  3. Real Madrid ta je za ta kara da Real Sociedad

  4. Everton 0-0 Liverpool

    Everton tana ta 12 a teburin Premier League bayan maki daya da ta samu a wasa da Liverpool.

    Amma za su ji ciwon kwallon da Tom Davies ya buga ta bugi turken Liverpool bai fada raga ba.

    Kawo yanzu Everton ta buga wasa 22 ba ta doke Liverpool ba.

  5. Everton 0-0 Liverpool

    Mai wannan sakamakon ke nufi?

    idan har Manchester City ta yar da maki a karawa da Burnley ranar Litinin. Liverpool za ta iya cin kofin Premier League na bana ranar Laraba idan har ta doke Crystal Palace a Anfield.

    Karon farko da za ta ci Premier League tun bayan shekara 30.

  6. An tashi wasa - Everton 0-0 Liverpool

  7. Ra'ayin da kuke aikowa ta BBC Hausa Twitter

  8. Everton 0-0 Liverpool

    Fabinho ya yi bugun tazara amma Jordan Pickford ya yi kokarin ya kama kwallo amma ya subece masa kwallon ya je kwana.

  9. Everton 0-0 Liverpool

    Mai kuma Richarlison ke son yin sakiyar da ba ruwa?

    Ya kayar da Alex Oxlade-Chamberlain daf da da'ira 18 ta Everton.

    Ketar da bai kamata ya yi ba - kuma Liverpool ta samu dama kenan mai kyau.

  10. Ra'ayin da kuke aikowa a BBC Hausa Twitter

  11. Canji - Everton 0-0 Liverpool

    Har yanzu Everton ba ta fitar da rai ba

    Bernard ya shiga ya canji Alex Iwobi.

  12. Katin gargadi - Everton 0-0 Liverpool

    An bai wa Divock Origi kati mai ruwan dorawa.

  13. Everton 0-0 Liverpool

    Shekara 10 a wasan hamayya na Merseyside ba tare da ta yi nasara ba, hakika kwallon da ya bugi turke da ya fada ragar Liverpool to da farinciki bai misaltuwa.

  14. Kwallo ya bugi turke - Everton 0-0 Liverpool

    Dama mai kyau da Everton ta samu.

    Dominic Calvert-Lewin ya samu kwallo ya buga sai Alisson ya yi kowa sannan ya fice daga hannunsa shi kuwa Tom Davies ya maka ta zuwa raga amma sai ta yi fadi ta bugi turke.

    Liverpool ta sha da kyar a wannan harin.

  15. Ra'ayin da kuke aikowa ta BBC Twiiter

  16. Everton 0-0 Liverpool

    Matip! Dejan ya gama wasan da Liverpool ke buga wa da Everton kuma an maye gurbinsa da Lovren hakan na nufin Mo Salah ba zai buga wasan ba, Ko dai Klopp ya ajiye shi ne saboda wasa da Crystal Palace ranar Laraba?

  17. Everton 0-0 Liverpool

    Joël Matip ya fadi ana duba lafiyarsa. In za ku tuna Liverpool ta yi canji hudu fa daga biyar da aka amince zuwa karshen kakar bana.

    .

  18. Everton 0-0 Liverpool

    Everton ta sa Gylfi Sigurdsso a fili ya canji matashin dan kwallo Anthony Gordon,

    Liverpool Naby Keita da Roberto Firmino inda Georginio Wijnaldum da Divock Origi suka maye gurbinsu.

  19. Canji - Everton 0-0 Liverpool

    Jurgen Kloop zai yi canji biyu.

    DIVOCK ORIGI ya shiga fili kuma Everton ta kula da shi sosai.

  20. Everton 0-0 Liverpool

    Bugun tazara da Trent Alexander-Arnold ya buga ya kuma bi kwallo da kallo ko za ta fada raga amma ta taba dan wasan Everton ta yi waje, kwana kenan.