Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Real Madrid ta doke Valencia da ci 3-0

Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni kai tsaye a karawar La Liga tsakanin Real Madrid da Valencia da wainar da ake toyawa a fannin wasanni a duniya

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. An take kwallo Real Madrid 0-0 Valencia

    A filin wasa na Alfredo di Stefano Stadium.

  2. Ra'ayinku a Twitter a BBC Hausa

  3. Yadda teburi yake kawo yanzu

  4. Real Madrid da Valencia

  5. Real Madrid v Valencia

  6. Ra'ayinku da kuke aikowa a BBC Hausa Facebook

  7. Messi ya ci kwallo na 699 a karawa da Leganes

    Barcelona ta ci gaba da zama ta daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Leganes da ci 2-0 a wasan mako na 29 da suka kara ranar Talata a Camp Nou.

    Matashin dan wasa dan kasar Guinea-Bissau Ansu Fati shi ne ya fara cin kwallo daga baya Messi ya kara na biyu a bugun fenariri.

    Kyaftin din Barcelona ya ci kwallo na 699 a Barca da tawagar Argentina a bugun fenariti, bayan da Ruben Perez ya yi masa keta a cikin da'irar Leganes.

  8. Werner ya amince da kunshin yarjejeniyar Chelsea

    Chelsea ta amince ta dauko dan kwallon RB Leipzig, Timo Werner kan yarjejeniyar shekara biyar.

    Dan wasan mai shekara 24 ya amince da kunshin kwantiragin da Chelsea ta gabatar masa, zai koma Stamford Bridge a watan Yuli idan an kammala Bundesliga.

  9. Bashir - Mai goyon bayan Real Madrid

  10. Wadanda za su buga wa Real Madrid

  11. Wadanda za su buga wa Valencia

  12. Surajo Sira - Mai goyon baya Real Madrid

  13. Jama'a barkanmu da saduwa cikin shirin labarin wasanni kai tsaye a fafatawa tsakanin Real Madrid a gasar cin kofin La Liga.

    Za ku iya bayar da gudunmuwarku a lokacin da nake gabatar da shirin ta BBC Hausa Facebook ko ta Twitter.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper zan gabatar da shirin.