Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Real Madrid ta doke Valencia da ci 3-0

Wannan shafi ne da ke dauke da labarin wasanni kai tsaye a karawar La Liga tsakanin Real Madrid da Valencia da wainar da ake toyawa a fannin wasanni a duniya

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Real Madrid 0-0 Valencia

    An je hutu.

  2. Real Madrid 0-0 Valencia

    An yi karin minti uku.

    Real Madrid na bukatar cin wasan nan domin kada Barcelona ta yi mata nisa don ranar Juma'a Barca za ta je gidan Sevilla a wasa a zafi.

  3. Real Madrid 0-0 Valencia

    Tare kwallo na takwas da golan Valencia ya yi da ake buga masa, kuma Hazard ne ya yi nasa kokarin.

  4. Real Madrid 0-0 Valencia

    Real Madrid ta samu bugun kwana daf da za je hutu.

  5. Real Madrid 0-0 Valencia

    Yawanci damar Real daga waje suke buga kwallo ita ma Valencia abin da ta yi kenan inda Geoffrey Kondogbia ya daga ido ya maka kwallo daga yadi na 30 kuma ta yi kyau matuka.

    Hakan ne ya sa Thibaut Courtois ya yi fadi ya ture kwallon ya yi waje.

  6. Real Madrid 0-0 Valencia

    Karim Benzema bai yi abin da ya da ce ba.

    Kallo aka bugo daga wajen Dani Carvajal shi kuwa Benzema ya yi tsalle ya sa kai maimakon ya kwantar da kansa sai ya yi kokari ya bai wa Eden Hazard sai dai ba abun da ya faru.

  7. Real Madrid 0-0 Valencia

    Ba tabbas ko alkalin nan ya ga abin da ya faru.

    Ya kamata Valencia na da ci daya kam.

  8. Real Madrid 0-0 Valencia

    Mai tsaron bayan Real, Dani Carvajal ya samu ya ratsa cikin 'yan wasa uku na Valencia ya kuma yi gaba da gaba da mai tsaron raga Jasper Cillessen.

    sai dai kuma kallon da ya buga ta yi fadi ta kuma fita waje.

  9. Real Madrid 0-0 Valencia

    Kocin Valencia, Albert Celades bai ji dadin hukuncin da aka dauka ba.

    Ya kuma mike daga kan kujera ya je bakin filin wasa yana gyad kansa.

  10. An soke kallon - Real Madrid 0-0 Valencia

    WOWWW!

    Alkalin wasa Jose María Sanchez Martinez ya ce Rodrigo ya yi satar gida duk da yadda ya samu kwallon yana cikin gudu ya ratsa ya ci za a yi ta takaddamar wannan kwallon.

  11. VAR - Real Madrid 0-1 Valencia

    Za a duba ko da satar gida daga Rodrigo a gudun da ya yi.

    Alkalin ya sa ya je ya duba akwatin talabijin don tabbatar da sakamako.

  12. Real Madrid 0-1 Valencia, Rodrigo

  13. Kwallo ya bugi turke - Real Madrid 0-0 Valencia

    Wannan karon Valencia ce ta kusan cin kwallo.

    Tsohon dan kwallon Bolton Wanderers mai wasan aro Rodrigo ya yi guda aka sa masa kwallo mai kyau sai ya daga ta sama ta haura golan Madrid, Thibaut Courtois wanda ya yi kokari ya sa mata kafa ta bugi turke.

  14. Real Madrid 0-0 Valencia

    Kadan ya rage Real ta ci kallo

    Karim Benzema, ba tare da ya so kansa ba zai fadi ya tura wa Eden Hazard wanda k gudu a lokacin.

    Dan kwallon tawagar Belgium ya yi gaba da gaba da golan Valencia Jasper Cillessen, wanda ya banke ko ina hakan ya sa Hazard ya buga kwallo amma ta yi fadi ta fita waje.

  15. Ra'ayin da kuke aiko mana ta Twitter

  16. Real Madrid 0-0 Valencia

    Magoya bayan Manchester United da na Liverpool ya kamata su kalli rawar da dan wasan Valencia, Ferran Torres wanda ake alakanta cewar zai koma buga gasar Premier League a kakar badi.

  17. Real Madrid 0-0 Valencia

    Real ta kai kora ta hannun Casemiro inda ya buga kwallo daga yadi na 30 amma golan Valencia, Jasper Cillessen ya rike ta.

  18. Real Madrid 0-0 Valencia

    Wadanda ba su sani ba....

    Kocin Valencia, Albert Celades ya ci kwallo daya a wasan la Liga da ya buga wa Real Madrid tskanin da 2005.

    Ya fara buga mata wasa a karawar da ta ci a 2-1 a gida da Valencia ranar 9 ga watan Satumbar 2000.

    Tsohon dan kwallon mai wasan tsakiya zai so ya ci tsohuwar kungiyarsa domin ya nuna kansa a idon duniya.

  19. Real Madrid 0-0 Valencia

    Real Madrid na buga sauran wasanninta a filin da take atisaye, bayan da ake gyaran Santiago Bernabeu.

  20. Real Madrid 0-0 Valencia

    Kungiyoyin sun karya doka inda suke gaisawa har da rungumar zuna.