Borussia Dortmund ta casa Schalke da ci 4-0

Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da harkokin wasanni kan yadda suke wakana a fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. GOAL - Borussia Dortmund 2-0 Schalke, Raphael Guerreiro

    Schalke ta bai wa Dortmund kwallo a kyauta

    Mai tsaron ragar Schalke ne ya buga kwallo kai tsaye ta je wajen dan wasan Dortmund Julian Brandt shi kuwa ya bai wa Raphael Guerreiro wanda bai jira ba ya buga kwallo ta fada ragar Schalke.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Augsburg 0-1 Wolfsburg, Renato Steffen

    Mutumin da yafi kowa karamin jiki a filin ne ya ci wa Wolfsburg kwallo wato Augsburg.Renato Steffen,wanda yake da tsawon kafa 5 da inci 7.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Borussia Dortmund 1-0 Schalke

    Borussia Dortmund ta samu damar kara kwallo na biyu a raga, bayan daAchraf Hakimi ya buga tamaula koda yake Raphael Guerreiro ya hana kwallon ya shiga raga.

  4. RB Leizpig 0-1 Freiburg, Manuel Gulde

    A lokacin da aka kwaso kwana ne Manuel Guide ya ci wa Freiburg kwallo.

  5. Borussia Dortmund 1-0 Schalke, Erling Braut Haaland

    Dortmund ta ci kwallo kuma a karon farko da aka ci gaba da kakar bana.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Ana goge kwallo saboda cutar korona

    Cikin matakan kariya don kada a yada cutar korona za a dinga goge kwallo a lokacin da ake wasa, kuma dukkan 'yan zaman benci sai ya sa takunkumin kare fuska.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  7. Borussia Dortmund da Schalke 04

    Wannan karawar ta hamayya ce tana daga cikin wadda ke jan hankalin masu bibiyar wasanni sau da kafa.

    Kai tsaye

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Har yanzu ba a ci kwallo ba a wasannin da ake yi

    Bundesliga

    Asalin hoton, BBC Sport

  9. Wadanda ke kasan teburi kuwa

    Bundesliga

    Asalin hoton, BBC Sport

  10. Wadanda suke saman tebur

    Bayan da aka buga wasannin mako na 25 Bayern Munich ke kan gaba a teburi

    Bundesliga

    Asalin hoton, BBC Sport

  11. Ita ma karamar gasar Bundesliga za a ci gaba da ita, An tsaya a karawar mako na 25

    • DSC Arminia Bielefeld da VfL Osnabruck
    • Hannover 96 da FC Dynamo Dresden e.V
    • FC St. Pauli da FC Nuremberg
    • SpVgg Greuther Furth da Hamburg SVWeek
    • SV Wehen Wiesbaden II da VfB Stuttgart
  12. Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye

    • Robert Lewandowski Bayern Munich 25
    • Timo Werner RB Leipzig 21
    • Jadon Sancho BV Borussia Dortmund 14
    • Robin Quaison FSV Mainz12
    • Rouwen Hennings Fortuna Dusseldorf 11
    • Marco ReusBV Borussia Dortmund 11
    • Serge Gnabry Bayern Munich 11
    • Florian Niederlechner FC Augsburg 11
    • Sebastian Andersson FC Union Berlin 11
    • Wout Weghorst VfL Wolfsburg 11
    • Jhon Cordoba FC Koln 10
    Bundesliga

    Asalin hoton, Getty Images

  13. Union Berlin za ta koma buga gasar Bundesliga ba koci

    Ranar Asabar 16 ga watan Mayu za a ci gaba da gasar Bundesliga karawar mako na 26 ba tare da 'yan kallo ba.

    Sai dai kuma Union Berlin za ta ci gaba da kakar bana ta 2019-20 ba tare da mai horas da ita ba, bayan da Urs Fischer ya bar sansanin horon kungiyar ranar Laraba

    Bundesliga

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Mutum 300 aka amince a lokacin buga Bundesliga a fili

    Za a ci gaba da gasar Bundesliga karawar mako na 26 ba tare da 'yan kallo ba, bayan da aka dakatar da wasanni saboda bullar cutar korona.

    Yayin da ake shirin ci gaba da wasannin ba 'yan kallo, an kuma tanadi tsare-tsare da matakai da kungiyoyin za su bi a lokacin gasa.

    Mutum 300 aka amince a filin wasa a lokacin da ake gudanar da wasanni.

    Bundesliga

    Asalin hoton, Getty Images

  15. Za a iya sauya 'yan wasa biyar a Bundesliga

    An amince wa kungiyoyin Bundesliga su sauya 'yan kwallo biyar, idan aka ci gaba da wasannin bana, bayan da cutar korona ta haddasa tsaiko.

    Haka kuma hukumar da ke kula da wasannin Bundesliga ta cimma yarjejeniya da kungiyoyin cewar wadanda suka yi na karshe bayan kammala kakar 2019-20 za su fadi zuwa karamar gasar.

    Bundesliga

    Asalin hoton, Getty Images

  16. An tsaya ne a wasannin mako na 25, An kuma buga su a cikin watan Maris

    Asabar 7 Maris 2020

    • Bayer 04 Leverkusen 4 : 0 Eintracht FrankfurtWeek # 25
    • Hertha Berlin 2 : 2 SV Werder Bremen
    • Schalke 04 1 : 1 TSG 1899 Hoffenheim
    • VfL Wolfsburg 0 : 0 RB Leipzig
    • SC Freiburg 3 : 1 FC Union Berlin
    • Borussia Monchengladbach 1 : 2 BV Borussia Dortmund

    Lahadi 8 Maris 2020

    • Bayern Munich 2 : 0 FC Augsburg
    • FSV Mainz 05 1 : 1 Fortuna Dusseldorf

    Kwantan wasan mako na 21 Laraba 11 Maris 2020

    • Borussia Monchengladbach 2 : 1 FC Koln
  17. Idan anjima ne za a ci gaba da gasar Bundesliga, An tsaya a karawar mako na 25 tun cikin watan Maris.

    • BV Borussia Dortmund da Schalke 04
    • Hoffenheim da Hertha Berlin
    • FC Augsburg da VfL Wolfsburg
    • Fortuna Dusseldorf da SC Paderborn 07
    • RB Leipzig da SC Freiburg
    • Eintracht Frankfurt da Borussia Monchengladbach
  18. Barkanmu da wannan lokacin

    Lokaci ya yi da zan gabatar muku da sharhi da bayanai kan harkokin wasanni a fadin duniya da zan dunga kawo muku su kai tsaye.

    Sunana Mohammed Abdu, Mamman Skeeper zan gabatar muku da shirin.

    Da fatan za ku kasance a BBCHausa.com za kuma ku iya bayar da gudunmawa a BBC Hausa Facebook da Instagram da Twitter duk a BBC Hausa.