Nan muka kawo karshen shirin
Da fatan kun ji dadin yadda muka gabatar muku da shirin, sannan ku ci gaba da bibiyar BBC Hausa domin sanin labaran wasanni da dumiduminsu.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper nake muku sai anjima.
Wannan shafi na kawo muku bayanai da rahotanni kai tsaye kuma da dumi-duminsu dangane da harkokin wasanni kan yadda suke wakana a fadin duniya.
Mohammed Abdu
Da fatan kun ji dadin yadda muka gabatar muku da shirin, sannan ku ci gaba da bibiyar BBC Hausa domin sanin labaran wasanni da dumiduminsu.
Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper nake muku sai anjima.
Lahadi 17 Maris 2020.
Borussia Dortmund 4-0 Schalke
Augsburg 1-2 Wolfsburg
Fortuna Dusseldorf 0-0 Paderborn
RB Leipzig 1-1 Freiburg
Hoffenheim 0-3 Hertha Berlin

Asalin hoton, BBC Sport
A karon farko a tarihin Bundeslioga an sauya 'yan wasa biyar a wasa, na biyar din shi ne Timo Becker wanda ya canji Jonjoe Kenny a Schalke.
Raphael Guerreiro na fatan zama dan wasan Dortmund da ya ci kwallo uku rigis a raga a wasa da Schalke tun bayan 1966.
Dortmund make ta saka 'yan wasa biyu, inda Marcel Schmelzer da Mario Gotze suka maye gurbin Raphael Guerreiro da kuma Mahmoud Dahoud.
Jadon Sancho ya canji Thorgan Hazard wanda ya ci wa Dortmund kwallo a karawa da Schalke.
RB Leipzig wadda ke fatan lashe kofin bana ta farke kwallo ta hannun Yussuf Poulsen, bayan da ya samu kwallo a Kevin Kamp.
Schalke ta yi canji na hudu kenan inda Juan Miranda da ke buga wasa aro dan Barcelona ya maye gurbin Daniel Caligiuri.
Felix Uduokhai ne ya ci kwallo na biyu amma an ce ya yi satar gida.
Augsburg ta ci kwallo na biyu da ka
Dortmund ta saka Leonardo Balerdi, mai shekara 21 dan kasar Argentina ya canji Thomas Delaney.
Karon farko
Our first yellow card as Dortmund midfielder Thomas Delaney clatters a Schalke man in the air.
Thorgan Hazard bai kamata ya buga karawar ba, sai gashi ya ci kwallo ya kuma taimaka aka zura a raga.
Schalke na ta kai hare-hare, amma Dortmund ta san lagwan abokiyar karawar.
Dukkan wasannin da ake yi babu ‘yan kallo
Da akwai jami’an tsaro a bayan filin wasa don kada wasu su kawo tsaiko a lokacin da ake ci gaba da fafatawa, sannan ga dokar hana fita na aiki.
Saboda gudun yada cutar korona an hana ‘yan kallo zuwa kusa da filin da ake taka leda. Kimanin mutum 300 da ya hada da ‘yan wasa da alkalai da jami’ai ne za suyi hulda da filin wasa.
An kuma gwada ‘yan wasa cutar korona ana kuma sa ran su dunga bayar da tazara bayan an tashi wasa.
Tun kan fara wasa sai da aka killace ‘yan kwallo da wurin da suke motsa jiki.
Za ka iya jin tafin 'yan wasan Borussia Dortmund da ke zaman benci.
Ga yadda kungiyoyin biyu suka murza leda.

Asalin hoton, BBC Sport