Everton 0-0 Tottenham
To fa! Saura kiris Tottenham ta zura wa Everton kwallo a raga, amma abin mamaki mai tsaron raga Jordan Pickford ya samu sa'ar tare kwallon.

Asalin hoton, @premierleague
Muna kawo maku rahotanni da kuma sharhi kai-tsaye game da wasannin Premier mako na 11.
Umar Mikail and Shamsiyya Haruna
To fa! Saura kiris Tottenham ta zura wa Everton kwallo a raga, amma abin mamaki mai tsaron raga Jordan Pickford ya samu sa'ar tare kwallon.

Asalin hoton, @premierleague
Warri da Akwa United sun yi 1-1
An tashi daga wasa babu ci tsakanin Kano Pillars da Rivers United a wasan Firimiya mako na farko.
Yanzu kungiyoytin sun kasance a mataki na 10 da na 11 da maki dai-dai kowaccensu.
To fa! Tottenham na neman kai kura gidan Everton, sai dai mai tsaron raga ya yi saurin rike kwallon. Yanzu haka dai Spurs ta rike wuta.
Wikki Tourist ta zura kwallo ta biyu a ragar Jigawa Golden Stars - ma'ana ta farke ta kara.
Wannan new karon farko cikin shekaru da Jigawa ta take buga gasar. Wajibi ne su dage domin kada su koma inda suka fito.
Dan wasan Plateau United Nenrot S. ya zura kwallo ta uku a ragar Lobi Stars
Yayin da Everton za ta yi wasa da Tottenham anjima kadan, Tottenham din za ta yi wasan ba tare da Harry Kane ba bayan da aka fitar da jerin 'yan wasan da za su taka leda a wasan na yau.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, BBC Sport
Ben Davies shi ya jagoranci Spurs zuwa filin wasa. A 'yan kwanakin nan ba a gano shi cikin tawagar 'yan wasan...
Wannan ne karo na biyu a wasanni 95 da Tottenham ta fito ba tare da kyaftin din ta Harry Kane ko Hugo Lloris.
Wikki Tourist farke kwallon da Jigawa Golden Stars ta zura mata a minti na 47.
Wikki Tourist ta farke kwallo 1 bayan 'yan mintina da dawo wa daga hutun rabin lokaci.
Yanzu haka dai Abia Worriors ta zura wa Katsina United kwallo biyu a raga, minti 66 kenan da fara wasan.
Plateau United ta zura wa Lobi Stars kwallon farko cikin minti na 12 da fara wasan, sai Lobi din ta ci kanta da kanta a minti na 28.
Sai Sikiru A. ya farke wa Lobi Stars din kwallo daya cikin minti na 33 a bugun finareti.
Kalu S ne ya samu nasarar zura wa Adamawa United kwallo daya a raga cikin minti na 40 da fara wasan.
Wasa tsakanin Kano Pillars da Rivers United har yanzu kowannensu na nema, yayin da aka tafi hutun rabin lokaci.
Pillars take karbar bakuncin Rivers a Kano.
Leicester City ta samu mnakinta uku ba tare da wani ji ba.
Soyuncu da Jamie Vardy ne suka taimaka wa Leicester City yayin da ta casa Cerystal Palace har gida da ci 0-2.
Jamie |vardy ya zira kwallonsa ta 10 ne a kakar bana ana saura minti biyu a tashi daga wasa bayan sun yi musayar fasin da Garay a cikin yadi na 18 din Palace.
Kafin haka, Caglar Soyuncu ne ya fara jefa kwallo a ragar Palace a minti na 57, inda ya saka wa kwallo kai daga wani bugun kwana da james Maddison ya bugo.
Wannan nasarar ta daga Leicesetr zuwa mataki na uku a teburi, inda ita kuma Crystal palace ta gangaro zuwa mnataki na tara.

Asalin hoton, Getty Images
Kash! Ya ya aka yi ta kasa shiga raga?
saura kiris Ben Chilwell ya zira kwallo ta uku bayan da aka ba shi damar bugun tazara.
Jamie Vardy yana ci da wuta!!!
Kwallo mai kyau Youri Tielemans ya bai wa Vardy sai shi kuma ya yi musayar fasin tsakaninsa da Gray, inda daga baya ya cilla ta raga kawai abinsa.
Kwallonsa ta 10 kenan. Wuta kawai
Kocin Everton Marco Silva ya yi sauye-sauyen guda biyu farawa daga wasan Premier makon da ya gabata, lamarin da ya bai wa kungiyar damar doke Brighton.

Asalin hoton, BBC Sport
Yayin da Everton za ta yi wasa da Tottenham anjima kadan, Tottenham din za ta yi wasan ba tare da Harry Kane ba bayan da aka fitar da jerin 'yan wasan da za su taka leda a wasan na yau.

Asalin hoton, BBC Sport
Max Mayer na Palace ya karbi Cheikhou Kouyaté, yayin da shi kuma Demarai Gray na Leicester ya karbi Ayoz Perez.