Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda aka fafata a wasannin Lahadi na Premier

Muna kawo maku rahotanni da kuma sharhi kai-tsaye game da wasannin Premier mako na 11.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Shamsiyya Haruna

  1. Crystal Palace 0-1 Leicester, Benteke ya shigo

    Christian Benteke ya shigo domin murza leda ga Palace. Benteke ya ci kwallo biyu a kakar bana.

  2. Crystal Palace 0-1 Leicester, Zaha

    Zaha ya ja kwallo zuwa cikin yadi na 18 din Leicester kuma ya buga ta bayan ya yanka mutum daya, sai daiu ta daki jikin wani ta dawo.

  3. 'Yan wasan Palace a kwance, Crystal Palace 0-1 Leicester City

    Kouyaté da kuma Gary Cahill na kwance a kasa suna karbar kulawa daga masu agajin gaggawa bayan sun yi gware a yadi na 18 na gidansu.

  4. Crystal Palace 0-1 Leicester

    Yanzu haka dai Leicester City ta rike wa Crystal Palace wuta. kuma tana ci gaba da kaiwa kungiyar hari.

  5. Crystal Palace 0-1 Leicester

    Crystal Palace ta barar da dama biyu.

    Jeffrey Schlupp ya rike rigar Ricardo Pereira gab da yadi na 16 kuma a idon alkalin wasa Paul Tierney.

    Tuni aka bai wa Schluppi katin gargadi inda kuma aka bai wa Leicester bugun tazara, a wuri mai hadari.

  6. GOAL Crystal Palace 0-1 Leicester City, Crystal Palace 0-1 Leicester City

    Caglar Soyuncu ya ci wa Leicester City kwallon farko a wannan wasa.

    Wannan ita ce kwallon farko da Soyuncu ya ci wa kungiyarsa bayan 'yan bayan Palace sun kyale shi ba tare da ewani tsaro ba a tsakiyar yadi na 18. Shi kuma ba tare da wani bata loikaci ba ya yi tsallae ya goga mata kansa dahga bugun kwanar da James Maddison ya bugo.

    Leicester ta zama ta uku da wannan kwallon..

  7. Crystal Palace 0-0 Leicester City, Bugun tazara

    Maddison ya bugo wani bugun tazara daga bangaren dama zuwa cikin ragar Leicester amma 'yan baya sun yi aikinsu.

  8. Crystal Palace 0-0 Leicester, Katin gargadi

    Jonny Evans ya yi wa Cheikhou Kouyaté keta kuma tuni alkalin wasa Paul Tierney ya daga masa katin gargadi

  9. Firimiyar Najeriya, Kano Pillars vs Rivers United

    Kano Pillars ta take wasan mako na farko a Firimiyar Najeriya. Tana karbar bakuncin Rivers United a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano.

  10. Crystal Palace 0-0 Leicester City, James Maddison

    James Maddison ya samu damarmaki kusan sau bakwai kafin tafiya hutun rabin lokaci, babu mamaki ya amfana daga ta gaba ida ya samu.

  11. An dawo hutu, Crystal Palace 0-0 Leicester City

    Ba na jin Leicester za su so su fita daga wasan nan ba tare da maki ba saboda yadda suka yunkuro a kakar bana. Ko za su kuma ba mu mamaki a karo na biyu?

  12. Karen Carney, tsohon dan wasan Ingila ya ce, Crystal Palace 0-0 Leicester City

    "Wasan yana kayatarwa matuka ganin kungiyoyin biyu duka suna kan ganiya. Ina ganin Palace sun san kansu sosai sannan kuma sun wahalar da Leicester. Amma fa ba za ka iya cire masu rai ba domin kuwa suna da duk abin da ake bukata na cin wasa musamman ganin yadda 'yan wasan gabansu ke da sauri.

    "Ina ganin idan an dawo kashi na biyu za mu ga kayataccen wasa, ba mamaki ma mu ga kwallaye a raga.

  13. Crystal Palace 0-0 Leicester City, Hutun rabin lokaci

    Rawar da kowacce kungiya ta taka

    An tafi hutun rabin lokaci kuma duka kungiyoyin ba su iya samun cin kwallo ba.

    Zuwa yanzu a iya cewa Leicester ta fi taka rawa kamar yadda jadawalin da ke kasa ke nunawa:

    Leicester ta buga shot har 8, Palace ta buga shiga

    Leicester ta rike kwallo har kashi 60%, Palace ta rike kashi 40%

    Leicester ta buga kwana 4, Palace ta buga 2

    Leicester ta yi laifi sau 6, Palace ta yi 5.

  14. Crystal Palace 0-0 Leicester City

    An yi wa Zaha laifi, inda aka kayar da shi a gaban ragar Leicester. Bugun tazara ne mai hadari Palace ta buga, sai dai ba su amfana ba

  15. Firimiyar Najeriya, Kano Pillars vs Rivers United

    Nan gaba kadan Kano Pillars za ta karbi bakuncin Rivers United a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano.

    Wannan shi ne makon farko a gasar Firimiyar Najeriya

  16. Crystal Palace 0-0 Leicester City '27

    Kowacce kungiya ba ta nuna wata gajiyawa ba duk da cewa ko minti 30 ba a yi ba.

  17. Crystal Palace 0-0 Leicester City

    Leicester fa da kwarinsu sosai a wannan wasan domin kuwa har yanzu suna cike da shaukin kwallo 9 da suka dura wa Southampton a karshen makon da ya gabata, abin da ya tilasta wa 'yan wasan Southampton din sadaukar da albashinsu ga mabukata.

  18. Crystal Palace 0-0 Leicester City, Jamie Vardyyyyy

    Jamie Vardy ya kai hari daga shi sai gola, ya buga ta ga golan sai dai babu nasara, inda ya dawo da ita ga 'yan bayan Palace.

  19. Crystal Palace 0-0 Leicester City

    Wilfred Zaha ya fitar da wata kwallo mai kyau kuma ya bai wa Schlupp wanda shi kuma ya dadata, sai dai ta yi saman raga ba tare da wani hadari ba ga golan Leicester.

  20. Crystal Palace 0-0 Leicester City

    Palce ta kai yunkuri cikin ragar Leicester amma 'yan bayanta sun kokarta matuka.