Man Utd 0-1 Barcelona
Yadda kungiyoyin ke murza-leda a tsakaninsu.

Asalin hoton, BBC Sport
Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 125 a wasa 161 da ya yi a gasar Champions League.
Mohammed Abdu
Yadda kungiyoyin ke murza-leda a tsakaninsu.

Asalin hoton, BBC Sport
Wasan dai ya bude sosai sai yanzu ne United ke kai hare-hare domin ta farke kwallon da aka zura mata.
United ta kai hari mai kyau, inda Ashley Young ya buga kwallo zuwa wajen Marc-Andre ter Stegen.Amma sai Marcus Rashford,ya samu ya buga ta nufi raga amma ta bude da yawa.
Dakika 36 da komawa zagaye na biyu Ajax ta farke kwallo.
!David Neres, wanda a baya ya buga wa tawagar kwallon kafar Brzail shi ne ya buga kwallo, inda Wojciech Szczesny ya kasa tare ta.

Asalin hoton, Reuters
An fi Juventus taka -rawa.
Amma ana tsaka da kwallo sai Joao Cancelo ya buga wa Cristiano Ronaldois shi kuwa ya saka mata kai ta shiga raga, inda Andre Onana yaq kasa tare ta.

Asalin hoton, Reuters
De gea ya hana kwallo ta shiga raga, bayan da Luis Suarez ya bai wa Philippe Coutinho kwallo shi kuma ya buga zuwa raga, amma De Gea ya sa kafa ta je wajen Messi daga baya ta lalace.
Dama mai kyau da Juventus ta samu daga bangaren dama, Bernardeschi ya buga kwallo amma ta yi fadi. .
Za ku iya auna kwazon 'yan wasa latsa nan Manchester United da Barcelona

Asalin hoton, BBC Sport
Tabe-taben tamaula, Barcelona ce a hannun dama.

Asalin hoton, BBC Sport
Mai tsaron baya na Barcelona, Clement Lenglet ya kusan jan fenariti bayan da ya tare kwallo a kafar Scott McTominay shi kuwa ya fadi kasar wanwar, sai dai alkalin wasa Luca Rocchi ya ce babu komai.
Romelu Lukaku ya yi tafi, bayan da aka bugo masa kwallo ta haye kansa, kuma dan wasan na saka kwazo a karawar.
Yadda kungiyoyin biyu ke taka-leda

Asalin hoton, BBC Sport
Luke Shaw ba zai buga wasa na biyu a Barcelona ba, bayan da ya karbi katin gargadi sakamakon jan rigar Messi da ya yi ta baya.
An bai wa Sergio Busquets katin gargadi, bayan da ya yi wa Fred keta, United ta samu bugun tazara.
Kwallon da aka ci United an ce Luke Shaw ya ci gida.
Ajax na ta kai kora, inda Hakim Ziyech ya dan taba kwallo ta yi sama bayan dan tabe-taben da suka yi.
Barcelona sai taka rawa take yi har ma Philippe Coutinho da Luis Suarez sun yi bani in baka sun ci gaba da tafiya da kwallon.