Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ronaldo ya ci kwallo 125 a Champions League

Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 125 a wasa 161 da ya yi a gasar Champions League.

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. United ba ta kokari a wasan daf da na kusa da na karshe

    Manchester United ta yi nasara a karawa biyu daga 11 baya da ta yi a wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League, inda ta yi canjaras uku aka doke ta wasa shida.

    Sannan ta kasa cin wasa a daf da na kusa da na karshe gida da waje da Bayern Munich a kakar 2013-14 karkashin jagorancin David Moyes.

  2. Muhawarar da kuke yi a BBC Hausa Facebook

  3. Barcelona da Manchester United

  4. Ko Messi zai kawo kanfar kwallaye a wannan karon?

    Messi bai ci kwallo ba a wasa 11 da ya yi a karawar daf da na kusa da na karshe tun cin PSG da ya yi a Afirilun 2013.

    Dan kwallon na Argentina ya buga kwallo ta nufi raga sau 49.

  5. Ronaldo ya saba cin Ajax

  6. Ko Ole Gunnar zai ci Barcelona?

    Manchester United ta yi rashin nasara sau biyu a gida a Champions League din bana a hannun Juventus da kuma PSG.

    Kungiyar ta taba rashin nasara a gida sau uku a kakar 1996-97, kuma kocin United Ole Gunnar Solskjaer ya buga dukkan karawar da aka doke su a lokacin.

  7. Yadda kuke tafka muhawara a BBC Hausa Facebook

  8. Ko Messi zai taka rawar gani kuwa?

  9. Ajax da Juventus

    Wannan ne karo na tara da Ajax da Juventus ke karawa a gasar Zakarun Turai ta European Cup/Champions League, kuma karon farko tun Nuwambar 2004.

    Rabon da Ajax ta ci Juventus tun lashe Europen Cup da ta yi da ci 1-0 a Belgrade a 1973.

  10. Man United da Barcelona

    Wannan ne karon farko da Manchester United da Barcelona za su kara tun 2011, bayan da Barca ta yi nasara a wasan karshe da ci 3-1 a Wembley.

    Manchester United ba ta taba yin rashin nasara a gasar Zakarun Turai a karawa da Barcelona a gida ba, inda ta ci wasa biyu da canjaras biyu.

    Wannan ne karo na biyu da za su kara a Old Trafford tun wasan daf da karshe da United ta yi nasara da ci 1-0 a 2007-08.

  11. Mohammed Abdu ne ke muku barka da saduwa a shirin gasar cin Kocin Zakarun Turai ta Champions League tsakanin Manchester United da Barcelona da wasa tsakanin Ajax da Juventus.

    Za ku iya bayar da gudunmawa a lokacin shirin a Facebook a BBCHausa.com da kuma ta Twitter duk a @bbchausa.com