Ajax 0-0 Juventus
Dama mai kyau da Ajax ta samu, Hakim Ziyech ya yi bani in baka da Dusan Tadic sannan ya buga kwallon daga yadi na 25.
Sai dai mai tsaron ragar Juventus, Wojciech Szczesny ya yi iya kokarinsa. .
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cristiano Ronaldo ya ci kwallo 125 a wasa 161 da ya yi a gasar Champions League.
Mohammed Abdu
Dama mai kyau da Ajax ta samu, Hakim Ziyech ya yi bani in baka da Dusan Tadic sannan ya buga kwallon daga yadi na 25.
Sai dai mai tsaron ragar Juventus, Wojciech Szczesny ya yi iya kokarinsa. .
Da ka ci kwallon mataimakin alkalin wasa ya ce an yi satar gida, daga baya alkali ya amince aka bai wa Barcelona kwallon.
Kuma 'yan bayan United ne suka yi sakaci
Sai yanzu ne Messi ya nuna kansa, inda ya yi kan mutum biyu da kwallo amma Scott McTominay ya matse shi daga baya ta yi fadi.
Barca tana da kaso 88% a wasan.
Har yanzu ba a kai wani gagarumin hari ba tsakanin Ajax da Juventus, kowa yana yi a hanakli don kar a yi masa sakiyar da ba ruwa tun da sanyin safiya.
Sergio Busquets, ya yi wa Scott McTominay keta, kuma magoya bayan United na ihun a yi masa katin gargadi.
Kwanar da Barca ta kwaso ba ta yi kyau ba.
Dare bai yi ba a Manchester sai dai Jordi Alba ya samu kwana.
Messi ya ci kwallo 22 a wasa 30 da ya fafata da kungiyoyin Ingila a gasar ta Zakarun Turai.
Filin wasa na Old Trafford da zai karbi bakuncin Manchester United da Barcelona
Shekara 20 kenan tun lokcin da Ole Gunnar Solskjaer ya lashe kofin Champions League a Manchester United, kuma a kakar sai da su kara da Barcelona gida da waje a karawar cikin rukuni..
Moise Kean ya cio wa Juventus kwallo na biyu da ta doke AC Milan, jumulla ya zura bakwai a raga a karawa takwas da ya yi wa klub dinsa da kasarsa.
Barcelona ta kai zagayen gaba a karawa 23 daga 29 idan ta fara buga wasa a waje, idan ka kwatanta da sau hudu ta kai zagayen gaba daga 12 da ta yi idan ta fara wasa a gida.
Ajax ce ke da matasa a Champions League ta bana masu karancin shekara daga 24 da kwana 202 a kakar bana.
Wannan ne karo na 17 da Barcelona za ta buga wasan daf da na kusa da na karshe a Champions League ta yi kan-kan-kan da Bayern Munich, kuma karo na 12 a jere tana kai wa wannan matakin.
Ajax ce ta fitar da Real Madrid a wasan zagaye na biyu, kungiyar farko da ta yi waje da mai rike da kofi tun wanda Atletico Madrid ta ci Barcelona a wasan daf da na kusa da na karshe a 2015-16.
Kuma Ajax ce ta farko daga Netherlands da ta kai wannan matakin tun bayan PSV A 2006-07.
Sai dai rabon da Ajax ta samu kanta a wannan matsayin tun 2002-03, inda AC Milan ta fitar da ita.