Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda Manchester United ta doke Tottenham

Mancheser United ta doke Tottenham ci 0-1 a fafatawar da suka yi a gasar Firimiya a Wembley. Ole Gunnar Solskjaer yanzu ya buga wasa biyar a jere ba a doke shi ba.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau

  1. 'Yan wasan Manchester United 11, Tottenham da Manchester United

    Paul Pogba zai buga wa Manchester United wasa bayan bai buga gasar FA ba saboda rauni a kafarsa.

    Eric Bailly ba ya cikin wadanda za su buga wa Manchester United saboda dakatar da shi da aka yi.

  2. 'Yan wasan Tottenham 11, Tottenham da Manchester United

    Jan Vertonghen yana cikin tawagar Tottenham bayan jinya da ya yi. Amma babu Eric Dier da Lucas Moura da Mousa Dembele da ke ci gaba da jinya.

  3. Muna maku maraba, Tottenham da Manchester United

    Muna maku maraba a daidai wannan lokaci da za mu kawo maku sharhi da bayanai kan fafatawa tsakanin Tottenham da Manchester United a gasar Firimiya ta Ingila.

    Tottenham ce ke karbar bakuncin Manchester United a Wembley.