Yadda Chelsea ta doke Manchester City

Chelsea ta doke Manchester City 2-0 a fafatawar da suka yi a gasar Firimiya mako na 16. Mun kawo Labarai da sharhi kai-tsaye game da dukkanin wasannin da aka fafata a ranar Asabar.

Rahoto kai-tsaye

Abdulwasiu Hassan and Awwal Ahmad Janyau

  1. Chelsea ta doke City, Chelsea 2-0 Man City

    Manchester City ta sha kaye a gasar Firimiya a karon farko a wannan kakar.

  2. An kara minti hudu, Chelsea 2-0 Man City

    An kara minti hudu kafin a hura karshen wasa. Man City ta saka Olivier Giroud wanda ya maye gurbin Eden Hazard.

    Shin City za ta iya ramawa?

  3. Man City ta yi canji, '86 Chelsea 2-0 Man City

    Phil Foden ya mayeo Riyad Mahrez.Shin matashin dan wasan zai iya sauya wasan ?

  4. Liverpool na murna, '82 Chelsea 2-0 Man City

    Idan wasan ya kare haka dai Liverpool za ta ci gaba da zama a saman teburin Firimiya. Wannan ya sa magoya bayan Liverpool suna murna game da yadda sakamakon wasannan ka iya kasancewa.

    Teburi
    Bayanan hoto, Haka teburin gasar Firimiya zai kasance idan har wasan ya kare a haka
  5. GOAL, '78 Chelsea 2-0 Man City

    David Luiz ya kara wa Manchester City. Hanya za su iya ramawa kuwa?

    Chelsea ta ci ta daya a damar farkon da ta samu. Yanzu kuma ta ci ta biyu a kwanar farko da ta samu.

    David Luiz ya tashi sama inda ya riga Ilkay Gundogan samun kwallo kusa da raga sannan ya tura ta ciki da kai.

  6. Man City ta yi canji, Chelsea 1-0 Man City

    An cireDavid Silva kuma aka saka Ilkay Gundogan .

  7. Har yanzu ana 1-0, Chelsea 1-0 Man City

    Tun bayan ana dawo daga hutun rabin lokaci Man City ta kasa rama ci dayan da Chelsea ta yi mata

  8. An tafi hutun rabin lokaci

    Shin Manchester City za ta iya ramawa bayan an dawo ne ko kuma za a kara mata?

  9. GOAL, '42 Chelsea 1-0 Man City

    Ngole Kante!

    Kante ne ya ci wa Chelsea kwallo a damar farko da suka samu. David Luiz ne ya bai wa Eden Hazard ta hannun hagu.

    Dan wasan na Belgium ya ja 'yan wasan bayan Man Ciity sannan ya tura kwallon ga N'Golo Kante, wanda ya shiga gidanj Man City da gudu.

    Kante

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Saura kiris!

    Riyad Mahrez ya tura wa Leroy Sane kwallo. Shi kuwa sai ya tsere wa Cesar Azpilicueta for pace. Sai dai kuam an ture dan Jamus, kuma gola ya tare kwallon da ya buga.

    Raheem Sterling ya sake buga kwallon da ta dawo, sai dai Antonio Rudiger buga kwallon waje kafin Sane ya sakew samun wata damar cin kwallo inda aka tura kwallonsa saman raga

    sane

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Pep ba ya jin dadi, '40 Chelsea 0-0 Man City

    Duk da cewa Manchester City ce ta fi rike kwallo, Pep Guardiola bai yi kama da wanda kecikin farin ciki ba. Sau biyu yana rufe fuskarsa da hannayensa cikin 'yan mintunan da suka wuce.

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, PA

  12. Sane, '36Chelsea 0-0 Man City

    Leroy Sane ya kwace kwallo daga hannun Antonio Rudiger . Ya tura kwallon tsakiya. Sai dai Chelsea dauke kwallon.

    Babu wani abin da ya faru kawo yanzu. sai dai kuma City tana kwankwasa kofa a hankali.

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

  13. Man City ce take wasa, '31 Chelsea 0-0 Man City

    Cikin minti 20 na farko 'yan wasan Man City sun bai wa junansu kwallo sau 29 a bangaren 'yan wasan gabansu dake gidan Chelsea. Chelsea fa? Ko sau daya.

    Konte

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Raheem Sterling, '23 Chelsea 0-0 Man City

    Raheem Sterling ya yi kokarin shigar da kwallo ta hannun dama, sai dai Marcos Alonso ya kayar da shi.

    Kuma an bai wa City bugu kan keta. David Silva buga kwallon da kyau. Sai dai kuma John Stones, bai sami kwallon ba. Lamarin da ya sa kwallon ya fita.

  15. Saura kiris!, '21 Chelsea 0-0 Man City

    Leroy Sane ya tsinke da gudu ta hannun hagu. Ya yanke 'yan wasa biyu kafin ya bai wa Bernardo Silva da David Silva kwallo.

    David ya mayar masa da kwallon a cikin da'irar Chelsea. sai dai kafin ya buga, an ture kwallon. Ya nemi ya sake kwato kwallon sai dai yunkurinsa ya sa an hura keta.

    Sane

    Asalin hoton, Reuters

  16. Yadda ake, Chelsea 0-0 Man City

    A halin yanzu dai kamar Chelsea ba ta san yadda za ta yi wasan ba. Ita kuwa City ba ta samu wata damar cin kwallo ba tukunna. Kokarin da ci da Raheem Sterling ya yi shio kadai ne damar da suka samu...

  17. Chlesea na fafatawa da Manchester City

    Chlesea ta fara fafatawa da Manchester City.

    Chelsea vs Man City

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Arsenal ce ta uku a teburin Firimiya

    Kungiyar kafa ta Arsenal ta zama ta uku a teburin gasar Firimiya bayan ta doke Huddersfield da ci daya da nema.

    Ita kuwa Manchester United ta zama ta shida a teburin bayan ta lallasa Fulham da 4-1.

    Table
  19. Sakamakon wasu wasannin Firimiyar yau

    Ga sakamakon wasu daga cikin wasannin gasar Firimiyar da aka buga a yau.

    Nan ba da jimawa ba za mu fara kawo muku sharhi da labarai kan wasan Manchester City da Chelsea da kuma na Leicester City da Tottenham.

    Premiere League
  20. Man U ta doke Fulham, Man U 4-1 Fulham

    Wasa ya kare! An koma samun nasara a Old Trafford. Manchester United ta samu gagarumar nasara kan Fulham.