Chelsea ta doke City, Chelsea 2-0 Man City
Manchester City ta sha kaye a gasar Firimiya a karon farko a wannan kakar.
Chelsea ta doke Manchester City 2-0 a fafatawar da suka yi a gasar Firimiya mako na 16. Mun kawo Labarai da sharhi kai-tsaye game da dukkanin wasannin da aka fafata a ranar Asabar.
Abdulwasiu Hassan and Awwal Ahmad Janyau
Manchester City ta sha kaye a gasar Firimiya a karon farko a wannan kakar.
An kara minti hudu kafin a hura karshen wasa. Man City ta saka Olivier Giroud wanda ya maye gurbin Eden Hazard.
Shin City za ta iya ramawa?
Phil Foden ya mayeo Riyad Mahrez.Shin matashin dan wasan zai iya sauya wasan ?
Idan wasan ya kare haka dai Liverpool za ta ci gaba da zama a saman teburin Firimiya. Wannan ya sa magoya bayan Liverpool suna murna game da yadda sakamakon wasannan ka iya kasancewa.

David Luiz ya kara wa Manchester City. Hanya za su iya ramawa kuwa?
Chelsea ta ci ta daya a damar farkon da ta samu. Yanzu kuma ta ci ta biyu a kwanar farko da ta samu.
David Luiz ya tashi sama inda ya riga Ilkay Gundogan samun kwallo kusa da raga sannan ya tura ta ciki da kai.
An cireDavid Silva kuma aka saka Ilkay Gundogan .
Tun bayan ana dawo daga hutun rabin lokaci Man City ta kasa rama ci dayan da Chelsea ta yi mata
Shin Manchester City za ta iya ramawa bayan an dawo ne ko kuma za a kara mata?
Ngole Kante!
Kante ne ya ci wa Chelsea kwallo a damar farko da suka samu. David Luiz ne ya bai wa Eden Hazard ta hannun hagu.
Dan wasan na Belgium ya ja 'yan wasan bayan Man Ciity sannan ya tura kwallon ga N'Golo Kante, wanda ya shiga gidanj Man City da gudu.

Asalin hoton, Getty Images
Riyad Mahrez ya tura wa Leroy Sane kwallo. Shi kuwa sai ya tsere wa Cesar Azpilicueta for pace. Sai dai kuam an ture dan Jamus, kuma gola ya tare kwallon da ya buga.
Raheem Sterling ya sake buga kwallon da ta dawo, sai dai Antonio Rudiger buga kwallon waje kafin Sane ya sakew samun wata damar cin kwallo inda aka tura kwallonsa saman raga

Asalin hoton, Getty Images
Duk da cewa Manchester City ce ta fi rike kwallo, Pep Guardiola bai yi kama da wanda kecikin farin ciki ba. Sau biyu yana rufe fuskarsa da hannayensa cikin 'yan mintunan da suka wuce.

Asalin hoton, PA
Leroy Sane ya kwace kwallo daga hannun Antonio Rudiger . Ya tura kwallon tsakiya. Sai dai Chelsea dauke kwallon.
Babu wani abin da ya faru kawo yanzu. sai dai kuma City tana kwankwasa kofa a hankali.

Asalin hoton, Reuters
Cikin minti 20 na farko 'yan wasan Man City sun bai wa junansu kwallo sau 29 a bangaren 'yan wasan gabansu dake gidan Chelsea. Chelsea fa? Ko sau daya.

Asalin hoton, Getty Images
Raheem Sterling ya yi kokarin shigar da kwallo ta hannun dama, sai dai Marcos Alonso ya kayar da shi.
Kuma an bai wa City bugu kan keta. David Silva buga kwallon da kyau. Sai dai kuma John Stones, bai sami kwallon ba. Lamarin da ya sa kwallon ya fita.
Leroy Sane ya tsinke da gudu ta hannun hagu. Ya yanke 'yan wasa biyu kafin ya bai wa Bernardo Silva da David Silva kwallo.
David ya mayar masa da kwallon a cikin da'irar Chelsea. sai dai kafin ya buga, an ture kwallon. Ya nemi ya sake kwato kwallon sai dai yunkurinsa ya sa an hura keta.

Asalin hoton, Reuters
A halin yanzu dai kamar Chelsea ba ta san yadda za ta yi wasan ba. Ita kuwa City ba ta samu wata damar cin kwallo ba tukunna. Kokarin da ci da Raheem Sterling ya yi shio kadai ne damar da suka samu...
Chlesea ta fara fafatawa da Manchester City.

Asalin hoton, Getty Images
Kungiyar kafa ta Arsenal ta zama ta uku a teburin gasar Firimiya bayan ta doke Huddersfield da ci daya da nema.
Ita kuwa Manchester United ta zama ta shida a teburin bayan ta lallasa Fulham da 4-1.

Ga sakamakon wasu daga cikin wasannin gasar Firimiyar da aka buga a yau.
Nan ba da jimawa ba za mu fara kawo muku sharhi da labarai kan wasan Manchester City da Chelsea da kuma na Leicester City da Tottenham.

Wasa ya kare! An koma samun nasara a Old Trafford. Manchester United ta samu gagarumar nasara kan Fulham.