Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yadda Roma ta yi kaca-kaca da Barcelona

AS Roma ta yi waje rot da Barcelona yayin da Liverpool ta fitar da Manchester City daga gasar cin kofin Zakarun Turai ta bana.

Rahoto kai-tsaye

Naziru Mikailu

  1. 'Yan wasan Man City da za su taka leda

  2. 'Yan wasan Liverpool da za su taka leda, Man City da Liverpool

  3. Yadda ta ka ya a wasan farko, Man City da Liverpool

    Liverpool ta casa Man City da ci 3-0. Sun zura kwallo uku a minti 30 na farko ta hannun Mohammed Salah, Alex Oxlade-Chamberlain da Sadio Mane.

    City za ta yi kokarin rama amma ana ganin sai ta yi da gaske musamman ganin yadda ta sake shan kashi a hannun Man United da ci 3-2 a ranar Asabar.

    Wannan na nufin an zura wa City kwallo shida a wasa biyu a jere.

  4. Jama'a barkanmu da war haka, Man City da Liverpool, Roma da Barca

    Jama'a barkanmu da yammaci da kuma sake saduwa a wani filin na sharhin gasar Zakarun Turai.

    A yau za a fafata tsakanin Manchester City da Liverpool, da kuma AS Roma da Barcelona.