Kwamatin Tsaro na MDD zai yi zaman gaggawa kan harin Isra'ila a Rafah

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 28 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail, Haruna Kakangi and A'isha Babangida

  1. An kashe Falasɗinawa 46 cikin awa 24, a cewar ma'aikatar lafiyar Gaza

    Rafah

    Asalin hoton, Reuters

    Ma'aikatar lafiya ƙarƙashin ikon Hamas ta ce an kashe Falasɗinawa aƙalla 46 cikin awa 24 da suka wuce a Zirin Gaza.

    Hakan ya sa adadin mutanen da aka kashe a zirin tun daga ranar 7 ga watan Oktoba sun zama 36,096, in ji ta - sakamakon hare-haren Isra'ila.

    Haka nan, an jikkata ƙarin mutum 110 tun daga Litinin ɗin.

    Isra'ila ta ƙaddamar da hare-haren ne a masayin ramuwar gayya kan harin da mayaƙan Hamas suka kai mata, inda suka kashe mutum 1,200 da kuma sace sama da 250.

    Yanzu haka Isra'ila ta mayar da hankali ne kan birnin Rafah da ke kudancin Gaza, inda take iƙirarin cewa nan ce tungar Hamas ta ƙarshe da take so ta tarwatsa.

  2. Siyasar ubangida ce babbar illar mulkin farar hula na shekara 25 a Najeriya - Bafarawa

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

    Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana siyasar ubangida da babbar illar mulkin dimokraɗiyya a tsawon shekaru 25 a Najeriya

    Attahiru Bafarawa ya shaida wa BBC hakan ne a wata hira da ya yi dangane da cikar mulkin dimokraɗiyya 25 ba tare da katsewa ba.

    " Mu da muka zo ba mu da 'kingmaker' wato ubangida, kowane gwamna zaman kansa yake amma bayanmu sai aka mayar da abin ubangida. Wasu gwamnoni ba su da kuɗin takara sai wasu su ba su saboda haka idan suka samu kujerar dole ne su biya. Wannan ya sa siyasa ta lalace saboda ta zama kamar zuba jari."

    Wani ƙalubalen da tsohon gwamnan ya ce shi ma ya yi wa dimokraɗiyya dabaibayi, shi ne yadda aka talauta 'yan Najeriya amma idan lokacin zaɓe ya yi sai a fito musu da kuɗi.

  3. Cutar Ebola ce ta kama gonakin tumatur, in ji gwamnatin Najeriya

    Tumatur

    Asalin hoton, EPA-EFE/REX/Shutterstock

    Gwamnatin Najeriya ta ce annobar Ebola ce ta kama gonakin tumatur, wadda ta jawo ƙaranci da kuma tsadar amfanin gonar a faɗin ƙasar.

    Ministan Noma da Samar da Abinci Abubakar Kyari ya ce suna ɗaukar matakin gaggawa kan cutar da ake kira Tomato Ebola ko kuma Leaf Miner.

    "Mun tura ƙwararru kan harkokin noma zuwa yankunan da abin ya shafa don shawo kan matsalar," in ji ministan cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin X, wanda aka sani da Twitter a baya.

    Ya ƙara da cewa suna kuma bai wa manoma shawarawarin yadda za su farfaɗo da irinsu "cikin sauri ta hanyar aiwatar da tsarin Ginger Blight Control Taskforce".

    Tuni farashin tumatirin ya yi tashin gwauron zabi har a karkara, yayin da mazauna biranen Abuja da Legas ke sayan abin da bai wuce ƙwaya shida ba a kan N1,000.

    Matsalar ta auku ne yayin da hauhawar farashi ta kai kashi 33.69 cikin 100 a watan Afrilu na bana idan aka kwatanta da kashi 22.22 da aka samu a Afrilun 2023.

  4. Tinubu zai yi wa 'yan majalisa jawabi a bikin dimokuraɗiyya

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai yi wa zaman haɗin gwiwa na majalisar ƙasar jawabi gobe Laraba a wani ɓangare na bikin cika shekara 25 da ɗorewar mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba.

    Akawun Majalisa Sani Tambawal ya ce shugaban zai kuma ƙaddamar da wani sabon ɗakin karatu da aka gina a farfajiyar ginin majalisar.

    "Ana sanar da sanatoci da wakilai cewa a wani ɓangare na bikin cika shekara 25 na mulkin dimokuraɗiyya da wakilci a majalisa, za a yi zaman haɗin gwiwa tsakanin majalisar wakilai da ta dattawa ranar Laraba," a cewar wata sanarwa.

    A ranar 29 ga watan Mayun 1999 aka rantsar da Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa zaɓaɓɓe, wanda ke nufin an shiga jamhuriya ta huɗu a siyasar Najeriya, kuma tun daga lokacin mulkin dimokuraɗiyya bai sake gamuwa da tangarɗa ba.

    Sai dai a yanzu ana bikin Ranar Dimokuraɗiyya ne ranar 12 ga watan Yuni tun daga 2018 - lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauya ta daga 29 ga watan Mayu.

  5. 'Yansandan jihar Ribas sun kama soja huɗu da zargin fashi da sata

    Mutanen da ake zargi da fashi

    Asalin hoton, RIvers State Police Command

    Rundunar 'yansandan Najeriya reshen jihar Ribas ta kama mutum 13 da zargin fashi da makami, da kuma satar kayan abinci.

    Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta fitar ranar Litinin ta ce cikin waɗanda ake zargin akwai soja huɗu, da jami'in rundunar tsaro ta Civil Defence.

    Grace Iringe-Koko ta ce sun yi nasarar kama mutanen ne sakamakon wani "bincike na tsanaki" bayan kama wani da ake zargi da haura gidan ajiyar abinci a ƙaramar hukumar Ohio/Akpor ta jihar.

    Biyu daga cikin mutanen farko da aka kama kofur-kofur ne a rundunar sojin Najeriya da ke aiki a jihar Delta, da kuma jami'i a rundunar tsaro ta Civil Defence mai aiki a Kabba da ke jihar Kogi, in ji ta.

    Ta ƙara da cewa daga baya ne suka gano wani babban gungu na masu aikata fashi da kuma karkatar da kayayyakin mutane, ciki har da manyan motoci.

    A cewarta, rundunar ta ƙwace mota ƙirar Toyota Hilux da gungun mutanen ke amfani da ita.

  6. Hare-haren Isra'ila na ragargazar yammacin Rafah

    Rafah

    Asalin hoton, Reuters

    Yanzu haka jiragen yaƙin Isra'ila na ragargazar yammacin yankin Rafah ta sama da kuma makaman atilare.

    Shaidu sun ce yanzu tankokin yaƙin Isra'ila ne ke iko da tsaunin Zoroub Hill, dutse mafi girma da ke kallon iyakar Gaza da Masar.

    Rundunar sojin Isra'ila ta faɗaɗa hare-harenta a yammacin birnin inda dakarunta ke iko da faɗin kilomita tara na Philadelphia Corridor, kamar yadda shaidu suka tabbatar wa BBC.

    Hukumomin Falasɗinu sun ce an kashe aƙalla 16 da tsakar dare, amma ma'aikatar lafiya ba ta tabbatar da adadin ba.

    Hare-haren sun tilasta wa iyalai da yawa guduwa zuwa asibitoci da ke kusa, yayin da su kuma ma'aikatan ceto ke fama wajen kaiwa ga waɗanda aka raunata.

  7. 'Yanbindiga sun kashe biyu cikin ɗaliban jami'ar Kogi da suka sace

    Rundunar ‘yansandan jihar Kogi a tsakiyar Najeriya ta tabbatar da mutuwar biyu daga cikin ɗaliban nan da ‘yanbindga suka yi garkuwa da su a Jami’ar Kimiyya ta Osare.

    Rundunar ta bayyana kisan daliban a matsayin abin takaici, ta kuma sha alwashin tabbatar da ceto sauran ɗaliban da maharan ke ci gaba da garkuwa da su.

    A ranar 13 ga watan Mayu ne maharan suka sace ɗaliban bayan da suka yi wa jami’ar tasu dirar mikiya a lokacin da suke tsaka da karatun fara jarabawa.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Zubairu Ahmad:

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Zubairu Ahmad:
  8. 'Mun yi asarar biliyoyin naira saboda rushe kasuwar Alaba Rago'

    Alaba Rago

    Asalin hoton, @HGbodurin

    ‘Yan kasuwa a shahararriyar kasuwar Alaba rago da ke jihar Legas a kudancin Najeriya na kirga asarar da suka tafka bayan gwamnatin jihar ta rushe shaguna a wani mataki na ba-zata.

    An rushe kaso mai yawa na kasuwar musanman wuraren ‘yan kasuwar cimaka a babbar kasuwar da ake sayar da dabbobi da hatsi da ke wajen birnin Legas.

    'Yan kasuwar waɗanda da yawansu 'yan asalin arewacin Najeriya ne, sun faɗa wa wakilin BBC Umar Shehu Elleman cewa rushe-rushen sun haddasa musu asarar sama da naira biliyan 200.

    Gwamnatin jihar na zargin cewa yankin ya kasance wani wuri da masu aikata laifuka daban-daban ke samun mafaka, zargin da ‘yan kasuwar suka musanta suna masu cewa suna kiyaye doka da oda a faɗin kasuwar.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Umar Shehu Elleman:

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Umar Shehu Elleman:
  9. Kwamatin Tsaro na MDD zai yi zaman gaggawa kan harin Isra'ila a Rafah

    Kwamatin Tsaro na MDD

    Asalin hoton, Reuters

    Kwamatin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya kira ganawar gaggawa a yau Talata domin tattauna harin da Isra'ila ta kai da ya kashe Falasɗinawa kusan 50 a yankin Rafah ranar Lahadi.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya siffanta harin da "mummunan kuskure," amma ƙasashen duniya na ci gaba da yin tir da harin.

    Ƙasar Aljeriya ce ta buƙci a yi ganawar jim kaɗan Babban Sakataren MDD Antonio Guterres ya bi sawun masu yin tir da lamarin.

    Ya ce halin da ake ciki a Rafah "tashin hankali ne da ya kamata a dakatar" kuma "babu wani wurin ɓuya a baki ɗayan Zirin Gaza".

    Ma'aikatar lafiya ta Gaza ƙarƙashin ikon Hamas ta ce mutum 45 hare-haren na Isra'ila suka kashe ranar Lahadi, yayin da ɗaruruwa suka ji raunukan ƙuna, da karaya, da sauransu.

  10. Barka

    Ma'abota BBC Hausa barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye.

    Za mu kawo muku rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da maƙwabtanta.

    Ku biyo mu Umar Mikail, da Haruna Ibrahim Kakangi, da kuma Aisha Babangida a wannan rana ta Talata.