Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 27 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Umar Mikail and Haruna Kakangi

  1. Masarautar Kano: Mataimakin gwamna ya nemi afuwar Nuhu Ribadu

    Aminu Gwarzo

    Asalin hoton, Kano State Government

    Mataimakin gwamnan jihar Kano ya janye kalaman da yi na zargin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro da hannu a rikicin masarautun jihar da ya jawo samun sarki biyu a Kano.

    Yayin wani taron manema labarai ranar Lahadi da dare, Aminu Abdussalam Gwarzo ya nemi afuwar Nuhu Ribaɗu yana mai cewa "bai fahimci abin da kyau ba ne".

    "Ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara ya musanta zarge-zargen da muka yi. Na gani a gidajen jarida uku kuma yau [Lahadi] na ga maganar cewa za su kai ƙara kotu," a cewar mataimakin gwamnan.

    "Ya kamata mu bayyana cewa wasu ne suka faɗa mana cewa Nuhu Ribadu ne ke goyon bayan wannan abu tuntuni. Muna neman afuwarsa da ofishinsa game da duk wani abin kunya da hakan ya jawo masa."

    "Dole ne mu amince cewa an fada mana abin da ba haka yake ba game da cewa mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro na da hannu a cikin wannan al'amari", in ji kwamared Adbulsalam.

    A ranar Asabar ne mataimakin gwamnan na Kano, Aminu Abdulsalam ya yi zargin cewa ofishin mai taimaka wa shugaban Najeriya kan tsaro ne ya samar wa sarkin Kano da aka tuɓe wa rawani, Aminu Ado Bayero jiragen sama biyu da suka kai shi birnin Kano tare da samar masa da tsaro.

    Lokacin da ya yi bayani ga manema labaru a fadar sarkin Kano da safiyar Asabar, ya ce "Mai ba wa Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ya ba da jirage guda biyu, su dakko tsohon Sarki su kawo shi Kano, kuma su kawo shi nan gidan".

    An shiga ruɗani a Kano tun bayan da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya koma birnin bayan sanarwar tsige shi tare kuma da mayar da sarkin na 14, Muhammadu Sanusi II kan karaga a ranar Juma'a,

    Wata kotun tarayya ce ta bayar da umurnin dakatar da aiwatar da dokar masarautar Kano ta 2024, wadda gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

    Kotun ta ce a tsaya a matsayin da ake har sai lokacin da ta saurari ƙarar da aka shigar wadda ke ƙalubalantar dokar masarautar ta 2024.

    • Abubuwan da sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024 ta ƙunsa
    • Abin da hukuncin kotu kan rushe masarautun Kano ya ƙunsa
  2. Aikin Hajji: Sama da maniyyatan Kaduna 1,600 sun isa Saudiyya

    ...

    Asalin hoton, NAHCON

    Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta ce ta yi nasarar jigilar maniyyata sama da 1,600 zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.

    Ayari na baya-bayan nan, wanda ya kunshi maniyyata 515, sun tashi ne a jiya Lahadi ta kamfanin jirgin Max Air.

    Yunusa Muhammad, jami’in hulda da jama’a na hukumar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa.

    Ya ce hakan ya kawo adadin maniyyatan da aka dauka daga jihar zuwa Saudiyya sun kai 1,612.

    Ya ce a halin yanzu an fara tantance maniyyatan da aka shirya dauka a jirgi na hudu kuma a yau ne ake sa ran za su tashi.

    • Dalilin Najeriya na ƙara kusan naira miliyan biyu ga maniyyatan Hajji
    • Malamai sun roƙi gwamnatin Najeriya ta taimaka wa maniyyata hajji
  3. Ba mu da hannu a rikicin Masarautar Kano – Sojoji

    ...

    Asalin hoton, @DefenceInfoNG/X

    Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa tana da hannu a rikicin masarautu da ke faruwa a jihar Kano.

    Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan hulda da jama’a na rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu a ranar Lahadin da rundunar ta wallafa a shafin sada zumuntarta naX.

    A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umurnin hana Gwamna Abba Yusuf mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan karagar mulki.

    Kotun ta kuma dakatar da aiwatar da sabuwar dokar da ta soke masarautun Bichi da Gaya da Karaye da kuma Rano.

    Duk da umarnin kotun, gwamnan jihar, Abba Yusuf, ya mayar da Sanusi a matsayin sarkin Kano, yana mai cewa "alkalin da ya bayar da wannan umarni ba ya cikin Najeriya a lokacin ba ya bayar da umarnin".

    “Saɓanin ra'ayin kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Kano kamar yadda jaridar Premium Times ta buga a ranar 26 ga Mayu 2024, sojojin Najeriya ba su da hannu a rikicin masarautar Kano kuma ba su da hannu wajen aiwatar da wani umarnin kotu. Sun dauki matakin ne kawai don duba duk wata matsala ko zagon kasa da za a iya samu a rikicin masarautar Kano." in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ƙara da cewa, "Batun da ya fi ɗaukar hankalin sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaro shi ne hana tabarbarewar doka da oda a jihar"

    Rundunar sojin ta ce za ta shiga tsakani ba tare da ɓata lokaci ba idan aikin tabbatar da tsaro na neman ya fi ƙarfin ‘yan sanda.

    “Duk abin da Sojoji ke yi a wannan mataki shi ne sanya ido kan lamarin da kuma kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana idan lamarin ya ta’azzara da zai kawo barazana ga tsaron jihar da ma yankin baki daya." in ji sanarwar.

    An sake nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 14 bayan sauke shi daga karagar mulki da tsohuwar gwamnatin jihar ta yi.

    Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da sake nada shi a makon da ya gabata, bayan amincewa da kudurin dokar masarautar jihar Kano na 2024 wanda aka gyara da majalisar ta amince a kai.

    Tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje dai ya sauke Sanusi daga muƙaminsa a ranar 9 ga Maris, 2020 bayan zargin sa da almundahana da kuɗain masarauta da kuma rashin biyayya.

    • Ba ni da hannu a rushe sababbin masarautun Kano - Rabiu Kwankwaso
    • Abin da hukuncin kotu kan rushe masarautun Kano ya ƙunsa
  4. Muna bincike kan harin da ya kashe fararen hula a Rafah - Isra'ila

    Rafah

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana bincike kan wani hari da aka kai ta sama a kusa da Rafah da ke kudancin Gaza, wanda jami'an Falasdinawa suka ce ya kashe mutane da dama a wani sansanin ƴan gudun hijira.

    Wakilin BBC ya ce rundunar sojan ta IDF ta tabbatar da cewa ta kai hari kan mayaƙan Hamas a yankin.

    Ma'aikatar lafiya a Gaza ƙarƙashin ikon Hamas ta ce 'yan gudun hijira aƙalla 35 aka kashe a wani harin daban kan wuraren gudun hijira bayan wannan da ake magana a kai.

    Kazalika, ta ce ta yi la’akari da rahotannin da ke cewa harin ya yi sanadin tashin gobara da ta shafi fararen hula kuma tana gudanar da bincike kan lamarin.

    Jami’an Falasɗinawa a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye sun bayyana harin a matsayin kisan ƙare-dangi tare da zargin Isra'ila da kai wa tantunan ƴan gudun hijira hari da gangan.

    • Al-Nakba: 'Ibtila'in' da ya faru da Falasɗinawa a 1948
    • Me umarnin ICC na kama Netanyahu da shugabannin Hamas ke nufi?
  5. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da hantsin Litinin, barkanmu kuma da sake haɗewa a shafin labarai kai-tsaye.

    Za mu kawo muku rahotonni na abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da kuma maƙwabtansu.