Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 26 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza and Aisha Shariff Bappa

  1. Tinubu zai fara bikin cika shekara guda a mulki da buɗe ayyuka a Legas

    ..

    Asalin hoton, Bayo Onanuga/X

    Bayanan hoto, Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

    Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai fara bikin murnar cikarsa shekara guda a kan karagar mulkin ƙasar da buɗe wasu muhimman ayyukan gwamnatin Tarayya a Legas da aka kammala a lokacin mulkinsa.

    Cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban kan kafofin yaɗa labarai na zamani, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a yau Lahadi shugaba Tinubu zai buɗe wani babban titin da aka yi da kankare zuwa manyan tasoshin jiragen ruwa na Apapa da Tin Can a birnin na Legas.

    Sanarwar ta ce an fara muhimmin aikin titin ne a zamanin tsohuwar gwamnati Muhammadu Buhari da ta gabata, inda kamfanin Dangote ya ɗauki nauyi gudanar da aikin ta hanyar harajin da yake tara wa gwamnati.

    ''Haka kuma shugaba Tinubu zai buɗe fitacciyar gadar nan ta 'Third Mainland' da ta ɗauki hankali sakamakon yadda aka zamanantar da ita'', in ji Sanarwar.

    ''Shugaban ƙasar zai kuma ƙaddamar da katafaren aikin titin da ya tashi daga Legas zuwa Calaba da aka yi ƙiyasin cewa zai laƙume kusan naira tiriliyan 15, muhimmin titi ne da zai ratsa jihohin kudancin ƙasar aƙalla tara'', kamar yadda Bayo Onanuga ya bayyana.

    Haka kuma sanarwar ta ce shugaban ƙasar zai ƙaddamar da aikin sake gina tituna har 330 a duka faɗin ƙasar.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewa a ranar Talata shugaban ƙasar zai koma koma Abuja babban birnin ƙasar, inda a nan ma ya tsara ƙaddamar da ayyuka ciki har da fara jigilar jirgin ƙasan fasinja da zai riƙa zagaya birnin Abuja.

  2. Marabanku

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da hutun ƙarshen mako.

    Fatan kun wayi gari lafiya, Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa a sassan duniya.

    Ka da mu manta kuma akwai shafukanmu na sada zumunta, inda za ku iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.

    Ku biyo mu...