A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya sanya hannu kan dokar da ta rusa masarautun Kano, bayan majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar gyara.
Sannan Gwamna Abba Kabir ya sanar da naɗin Muhammadu Sanusi ll a matsayin sabon sarkin Kano.
Gwamnan ya kuma bai wa duka sarakunan da aka rushe wa'adin sa'ao'i 48 daga ranar Alhamis da yamma da su fice daga fadojinsu tare da miƙa ragamarsu ga kwamishinan ƙananan hukumomin jihar.
To sai dai wata kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin dakatar da matakin rushe sarakunan, bayan da Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da ƙara a gabanta.
A ranar Juma'a kuma gwamnan ya miƙa wa sabon sarkin takardar kama aiki a wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka shirya a gidan gwamnatin jihar.
Sarki Muhammadu Sanusi ll ya kuma jagoranci sallar Juma'a a masallacin gidan gwamnatin jihar.
A lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin miƙa takardar, gwamnan jihar ya ce sabon sarkin zai ci gaba da zama a masaukinsa da ke gidan gwamnatin jihar, har zuwa lokacin da zai shiga fadarsa, bayan tsohon sarki ya kammala kwashe kaya da iyalansa.
To sai dai cikin dare sabon sarkin tare da rakiyar gwamna ya koma fadarsa, daga bisani kuma tsohon sarki alhaji Aminu Ado Bayero ya koma birnin.
Da safiyar yau ne kuma gwamnan jihar ya bai wa kwamishinan 'yan sanda na jihar umarnin kama tsohon sarkin, wanda ya koma fadar sarki da ke Nassarawa.