Sarki Muhammadu Sanusi II ya shiga fadarsa
Khalifa Muhammadu Sanusi ll ya shiga gidan Rumfa watau fadar Sarkin Kano da tsakar dare saɓanin yadda aka tsara tun farko.Sarkin Kano ya koma fadarsa ne tare da rakiyar gwamnan jihar da mataimakin gwamna da waɗansu ƙusoshin gwamnatin jihar.
A ranar Juma'a ne dai Gwamna Abba Kabir ya ce Khalifa Muhammadu Sanusi zai zauna a masaukinsa da ke gidan gwamnatin jihar Kano kafin ya koma fadarsa, bayan Aminu Ado Bayero ya kammala kwashe kayayyakinsa da iyalansa.
A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga Sarkin Kanon tare da rakiyar gwamnan da muƙarraban gwamnati suna isa fadar sarkin cikin dare, inda bayanai suka ce har wayewar gari gwamnan da muƙarrabansa suna fadar sarkin.
Mataimakin gwamnan jihar ya ce jami'an gwamnatin za su ci gaba da kasancewa a fadar sarkin har sai abin da hali ya yi.