Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 25/05/2024
Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 25 ga watan Mayun, 2024.
Rahoto kai-tsaye
Abdullahi Bello Diginza and Aisha Shariff Bappa
Ukraine ta yi tir da harin da Rasha ta kai kan shagon sayar da kaya
Shugaba Zelensky ya yi tir da mummunan hari ta sama da Rasha ta kai kan wani babban shagon sayar da kayayyaki da ke cike da jama'a.
Hukumomi sun ce aƙalla mutum biyu ne suka rasu yayin da sama da talatin suka jikkata a harin da aka kai a ranar Asabar.
Shugaba Zelensky ya buƙaci kawayensa na Turai da su ƙara aika wa Ukraine jiragen yaƙin da za su riƙa amfani da su wajen kare sararin samaniyar ƙasarsu.
Isra'ila ta amince da ci gaba da tattaunawa a kan batun sako 'yan kasarta
Rahotanni na cewa Isra'ila ta amince da sabon tsarin ci gaba da tattaunawa domin cimma yarjejeniyar sako 'yan ƙasarta da aka yi garkuwa da su a Gaza.
Kafar yaɗa labaran Isra'ila ta ce hakan na zuwa ne bayan tattaunawar da aka yi tsakanin babban jami'in leƙen asiri na isra'ila da shugaban hukumar leƙen asiri ta Amurka da Firaiministan Qatar a birnin Paris.
An samu tsaiko kan tattaunawar da ake yi domin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta sakamakon hare-haren Isra'ila a Rafah duk da rashin amincewar da ƙasashen duniya suka nuna kan matakin.
Malaman Kano na son Tinubu ya sa baki a rikicin masarautar Kano
Asalin hoton, Sani Maikatanga
Bayanan hoto, Masarautar Kano
Malaman Musulunci a jihar Kano sun bayyana damuwarsu kan cewa za a iya samun barkewar rikici idan har ba a yi taka tsantsan wajen warware dambarwar da ake fuskanta kan sarauta a jihar ba.
A cikin wata takardar sanarwa da ta samu sa hannun wasu daga cikin manyan malaman Musulunci na jihar, sun yi kira ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, da ya tsoma baki cikin lamarin don samun maslaha.
Malaman sun bayyana cewa Kano jiha ce mai cike da zaman lafiya da lumana duk da irin harkalla ta siyasa da ake samu.
Sanarwar ta kara da cewa “Ya shugaban kasa, a matsayinka na jagora bai kamata ka bari gwagwarmayar neman kujerar mulki ta rikide zuwa tashin hankali ba”.
Muna kuma kira ga shugaban kasa da ya bari al’ummar Kano su warware wannan matsala ba tare da an yi amfani da karfi ko rasa rai ba.
Tsananin zafi ya sa an rufe makarantu a Pakistan
Ana fama da tsananin zafi a Pakistan.
Yawancin sassan kasar tsananin zafin ya kai digiri 50 a ma'aunin celcius.
Tsananin zafin ya sa an rufe makarantu a Punjab.
Tuni aka shawarci al'ummar kasar da su takaita dukkan ayyukansu da suke yi a waje ma'ana cikin rana.
Mahukunta a kasar sun samar da wuraren da za a rinka taimak awa mutanen da tsananin zafin ya yi wa illa.
Sanya sojoji cikin rikicin masarautar Kano kuskure ne - Atiku
Asalin hoton, GETTY IMAGES
Bayanan hoto, Atiku
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce matakin gwamnatin tarayyar ya sabawa kundin tsarin mulki.
Ya ce matakin gwamnatin tarayya na tura jami'an tsaro Kano kan tirka tirkar da ake a game da batun nadin sarki abu ne da zai iya janyo matsala ga zaman lafiya a jihar, sannan kuma ya sabawa kundin tsarin mulki na 1999.
Atiku ya ce, a kokarin aiwatar da aikin da doka ta amince musu na samar da doka, majalisar dokokin jihar Kano ta amince da dokar masarautar Kano ta 2024, daidai da sashe na hudu na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, yayin da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar.
Ya ce a don haka tura sojoji Kano a kan lamari irin wannan ya na rage wa sojoji kima.
Atiku Abubakar, ya ce ya kamata mu tunatar da Tinubu cewa Kano jiha ce da ta kwashe dubban shekaru tana cikin zaman lafiya kuma duk wani yunkuri na kawo fitina ba zai samu karbuwa ba.
CISLAC ta yi kira a wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano
Asalin hoton, others
Bayanan hoto, Auwal Rafsanjani
Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaƙi da Rashawa a Najeriyar wato CISLAC, ta bayyana matukar damuwa a game da abubuwan da ke faruwa a Kano dangane da batun sauya sarki a jihar.
CISLAC ta yi gargadin cewa irin abubuwan da ke faruwa a jihar ta Kano na barazana ga zaman lafiyar jihar.
Babban darakta a cibiyar, Auwal Musa Rafsanjani, ya fitar da tsattsauran gargadi a kan duk wani yunkuri na amfani da yanayin da ake ciki a jihar domin ayyana dokar ta baci.
Ya ce, " Irin wadannan ayyuka ana kallonsu ne a matsayin ganganci da kuma takalar fada na babu gaira babu dalili da janyo bata shekara 1000 na tarihin siyasar jihar".
CISLAC, ta lura cikin fargaba cewa matsayin kotun wanda hukumomin tsaro suka dogara dashi shi ne ya janyo dawowar sarki Aminu Ado Bayero mai cike da takaddama a ciki.
Sanarwar cibiyar ta ce gwamnatin jiha ce kundin tsarin mulki ya bawa damar nadi da kuma tabbatar da sarakunan gargajiya ciki har da Sarki.
Abin da hukuncin kotu kan rushe masarautun Kano ya ƙunsa
Lafiya Zinariya: Yadda ya kamata iyaye su kula da 'ya'yansu mata
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin saurarin shirin
Ra'ayi Riga: Kan rushe masarautun Kano
Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Babu hannuna a komawar Aminu Ado zuwa Kano - Ribadu
Asalin hoton, Nuhu Ribadu/X
Bayanan hoto, Mallam Nuhu Ribadu
Ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ya musanta zargin hannun Nuhu Ribadu a komawar da Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi zuwa Kano.
Mataimakin gwamnan jihar kano Kwamared Aminu Abdussalam ne ya zargi Nuhu Ribadu da kitsa komawar Aminu Ado Bayero zuwa Kano ta hanyar ba shi jami'an tsaro da jirgin sama domin mayar da shi jihar.
''Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro ne ya bayar da jirage guda biyu domin ɗauko tsohon sarki domin su kawo shi Kano'', in ji mataimakin gwamnan.
To sai dai kakakin Nuhu Ribadun, Zakari Mijinyawa ya shaida wa BBC cewa babu hannun mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro a komawar tsohon sarkin.
''Ba gaskiya ba ne, babu wanda ya bayar da jirgi domin mayar da shi, saboda wannan ba aikinmu ba ne'', in ji Mijinyawa.
Dangane da zargin da mataimakin gwamnan ya yi cewa har da jami'an tsaro ofishin Ribadun ya aika Kano, Zakari ya ce ba haka batun yake ba.
''Babu wani jami'in tsaro da muka tura Kano, ai suma suna da jami'an tsaro, ai kwamishinan 'yan sandan jihar ya gabatar da taron manema labarai, kuma kowa ya ji yana cewa aikinsa yake yi, ba wanda ya saka shi''.
Ya ce bai kamata a riƙa sanya siyasa a cikin kowane irin batu ba.
Muna kira ga mutane su kwantar da hankula - Aminu Ado Bayero
Asalin hoton, HRH AMINU ADO BAYERO/INSTAGRAM
Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira ga al'ummar jihar su kwantar da hankula, yana mai cewa jami'an tsaro na aiki domin tabbatar da tsaron lafiyar jihar.
Yayin da yake jawabi ga taron manema labarai a ƙaramar fadar sarki da ke Nassarawa, Alhaji Aminu Ado ya ce mutane su yi addu'ar samun zaman lafiya.
''Jama'a a kwantar da hankula, jami'an tsaro na aiki, domin tabbatar da tsaron lafiya''.
Da asubahin yau ne Alhaji Aminu Ado ya koma Kano, kwana biyu bayan gwamnan jihar ya tuɓe shi.
Shi ma kwamishinan 'yan sandan jihar cikin wani jawabi da ya yi a shalkwatar 'yan sanda da ke Bompai ya yi kira ga mazauna birnin su kwantar da hankula tare da bai wa jami'an tsaro hadin kai.
CP Gumel ya ce jami'an 'yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro kamar yadda kundin tsarin Najeriya ya tanadar.
Muhammadu Sanusi ll ya kammala zaman fada
Sabon sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll ya kammala zaman fadancin da ya gudanar a fadarsa da ke Ƙofar Kudu.
Da hantsi ne dai sarkin ya fito daga gidansa a kan doki ya tafi fadar waje, inda ya karɓi gaisuwa daga wajen hakimansa da sauran jami'an gwamnatin Kano.
A jiya daddare ne dai sarkin ya koma gidan sarki tare da rakiyar gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, da sauran jami'an gwamnati.
Bayan kammala zaman fadancin, Sarki Muhammadu Sanusi ll ya sake hawa dokinsa zuwa cikin gidan sarki.
A ranar Juma'a ne Gwamna Abba Kabir ya miƙa wa Muhammadu Sanusi ll takardar shaidar naɗi a gidan gwamnatin jihar, bayan ya sake naɗa shi a matsayin sarkin Kano ranar Alhamis, jim kaɗan bayan majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautun Kano kwaskwarima
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kira taron manema labarai
Bayanan hoto, Alhaji Aminu Ado Bayero a gidan sarki na Nassarawa
Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu ado Bayero da gwaman jihar, Abba Kabir ya sanar da tuɓe shi, zai gabatar da taron manema labarai.
Da safiyar yau ne Alhaji Aminu Ado ya koma Kano tun bayan da aka sauke shi daga kan karagar.
Sai dai ya koma gidan sarki na Nassarawa ne, bayan da sarki Muhammadu Sanasi ll ya koma babbar fadar sarki da ke Ƙofar Kudu.
A yau ɗin ne kuma gwamnan jihar ya umarci kwamishinan 'yan sandan jihar ya kama Alhaji Aminu Ado kan abin ya kira 'ƙoƙarin tayar da tarzoma''.
To sai a taron manema labarai da kwamishinan 'yan sandan ya ce jami'an tsaro sun karɓi umarnin kotu kuma za su yi amfani da shi tare da samar da cikakken tsaro a faɗin jihar Kano.
Kotun tarayyar dai ta bayar da umarnin dakatar da soke masarautun jihar bayan shigar mata da ƙorafi kan hakan, sannan ta saka ranar 3 ga watan Yuni domin fara sauraron ƙasar.
CP Usaini Gumel ya ce jami'an tsaron suna biyayya ne da umarnin da kotun tarayyar da ke Kano ta bayar.
Don haka CP Gumel ya ce jami'an 'yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro kamar yadda kundin tsarin Najeriya ya tanadar.
Yadda Man United ta dauki FA Cup na 13 jimilla
Sarki Muhammadu Sanusi II ya fara zaman fada
Sarki Muhammadu Sanusi II ya fito daga gidan sarki a kan doki inda ya zarce fada domin fara zaman fadanci.
Magoya bayan sarkin da dama ne suka taru a lokacin da ya fito, inda suke miƙa caffa da gaisuwa ga sarkin.
Da shigarsa, sarkin Muhammadu Sanusi ll ya hau kan karagar mulki, inda hakimai suka riƙa kai gaisuwa tare da mubaya'a ga sabon sarkin.
Wasu kwamishinoni da muƙarraban gwamnatin Kano na daga cikin mutanen da ke kai gaisuwa ga sabon sarkin a fadarsa.
Za mu tabbatar da umurnin kotu a Kano - Kwamishinan ‘yansanda
Asalin hoton, Kano State Police Command
Jami'an tsaro a Kano sun ce sun karbi umarnin kotu kuma za su yi amfani da shi tare da samar da cikakken tsaro a faɗin jihar Kano.
Cikin wani jawabin hadin gwiwa da jami'an tsaron suka gabatar wa manema labarai a shalkwatar 'yan sanda da ke Bompai, kwamishinan 'yan sanda na jihar, CP Usaini Gumel ya ce jami'an tsaron suna biyayya ne da umarnin da kotun tarayyar da ke Kano ta bayar.
Kotun tarayyar dai ta bayar da umarnin dakatar da soke masarautun jihar bayan shigar mata da ƙorafi kan hakan, sannan ta saka ranar 3 ga watan Yuni domin fara sauraron ƙasar.
Don haka CP Gumel ya ce jami'an 'yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami'an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro kamar yadda kundin tsarin Najeriya ya tanadar.
Kwamishinan 'yan sandan ya kuma yi kira ga mazauna birnin Kano da su kwantar da hankula tare da bai wa jami'an tsaro hadin kai, musamman yadda ya ce an san al'ummar jihar wajen bin doka da oda, kafin kotu ta yanke hukunci kan batun ranar 3 ga watan Yuni.
CP Usaini Gumel ya kuma gargaɗi duk wanda ya yi yunƙurin karya doka a jihar da cewa zai fuskanci fushin jami'an tsaro.
Yana mai cewa jami'an tsaron sun baza komarsu a faɗin birnin domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka.
Watakila Rooney ya koma Plymouth
Abin da ya kamata ku sani kan batun sarauta a Kano
Asalin hoton, INSTAGRAM/MAIKATANGA PHOTOGRAPHY
A ranar Alhamis ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir ya sanya hannu kan dokar da ta rusa masarautun Kano, bayan majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar gyara.
Sannan Gwamna Abba Kabir ya sanar da naɗin Muhammadu Sanusi ll a matsayin sabon sarkin Kano.
Gwamnan ya kuma bai wa duka sarakunan da aka rushe wa'adin sa'ao'i 48 daga ranar Alhamis da yamma da su fice daga fadojinsu tare da miƙa ragamarsu ga kwamishinan ƙananan hukumomin jihar.
To sai dai wata kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin dakatar da matakin rushe sarakunan, bayan da Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da ƙara a gabanta.
A ranar Juma'a kuma gwamnan ya miƙa wa sabon sarkin takardar kama aiki a wani ƙwarya-ƙwaryar biki da aka shirya a gidan gwamnatin jihar.
Sarki Muhammadu Sanusi ll ya kuma jagoranci sallar Juma'a a masallacin gidan gwamnatin jihar.
A lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen bikin miƙa takardar, gwamnan jihar ya ce sabon sarkin zai ci gaba da zama a masaukinsa da ke gidan gwamnatin jihar, har zuwa lokacin da zai shiga fadarsa, bayan tsohon sarki ya kammala kwashe kaya da iyalansa.
To sai dai cikin dare sabon sarkin tare da rakiyar gwamna ya koma fadarsa, daga bisani kuma tsohon sarki alhaji Aminu Ado Bayero ya koma birnin.
Da safiyar yau ne kuma gwamnan jihar ya bai wa kwamishinan 'yan sanda na jihar umarnin kama tsohon sarkin, wanda ya koma fadar sarki da ke Nassarawa.
Bayanan da ke fitowa daga birnin Kano na cewa an jibge tarin jami'an sojoji a fadar sarki ta Nassarawa inda nan ne Alhaji Aminu Ado Bayero ya shiga.
Matakin na zuwa ne bayan da gwamnan jihar ya bayar da umarnin kama tsohon sarkin da safiyar yau Asabar.
Da asubahin yau ne Alhaji Aminu Ado Bayero ya isa Kano kwana biyu bayan sanar da matakin tuɓe shi daga sarauta da gwamna jihar ya yi.
Tuni dai sabon sarkin da gwamnan ya naɗa Muhammadu Sanusi ll ya shigar fadar sarkin tare da rakiyar gwamna.
Aminu Ado Bayero ya shiga fadar sarki ta Nassarawa
Asalin hoton, Instagram
Tsohon sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya shigar wata fadar sarki da ke unguwar Nassarawa a birnin Kano.
Da asubahin yau ne dai tsohon sarkin ya koma birnin tun bayan sanar da matakin tuɓe shi da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya yi ranar Alhamis.
Tun a cikin daren ne dai sarki Muhammadu Sanusi ll ya koma babbar fadar sarkin da ke cikin birni, tare da rakiyar gwamnan da sauran muƙarraban gwamnati.
To sai dai bayan komawar Aminu Ado birnin, bayanai sun ce ya koma wata ƙaramar fadar sarki da ke unguwar Nassarawa.
Tuni dai gwamnan jihar ya bai wa kwamishinan 'yan sanda na jihar umarnin kama Alhaji Aminu Ado, kan abin da ya kira ''yunƙurin tayar da tarzoma'' a birnin.