Hotunan ɗakin taron da za a miƙa wa Sarki Muhammadu Sanusi ll takarda

Shirye-shirye sun yi nisa a Kano dangane da miƙa wa Muhammadu Sanausi ll takardar kama aiki a matsayin sabon sarki.

Tuni dai ɗakin taro na Afirka da ke cikin gidan gwamnatin jihar, ya ɗauki harama, inda ake tsara kujeru da sauran shirye-shirye domin gudanar da taron.

Nan gaba a yau ne dai ake sa ran sabon sarkin zai isa Kano a shirye-shiryen karɓar mulki.
A ranar Alhamis ne dai gwamnan jihar Abba Kabir ya sanar da naɗin Muhammadu Sanusi ll a matsayin sabon sakin Kanon bayan ya sanya hannu kan dokar rushe masarautun jihar da majalisar dokokin jihar ta miƙa masa.






