Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 24 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Umar Mikail and Usman Minjibir

  1. An ƙaddamar sabon a-daidaita-sahu na mata zalla a Kano

    ..

    An ƙaddamar da babura masu ƙafa uku na a-daidaita-sahu guda 120 masu aiki da lantarki waɗanda aka ware wa mata a birnin Kano.

    Lokacin ƙaddamar da shirin na haɗin gwiwa tsakanin bankin Alternative Bank da Shirin bunƙasa ƙasashen ƙungiyar commonwealth na Birtaniya, shugaban bankin Garba Mohammed ya ce wannan zai sauya tsarin sufuri a birnin Kano.

    Ya ce an ɓullo da tsarin ne domin taimakawa wajen samar da tsaro ga mata da yara tare da bunƙasa rayuwarsu.

    Haka nan zai taimaka wajen kare muhalli ta hanyar rage yawan fitar da sanadarin Carbon mai gurɓata muhalli, wanda babura masu amfani da fetur ke fitarwa.

    Mata waɗanda aka bai wa horo kan tuƙi da gyaran baburan ne dai za su riƙa zirga-zirga da baburan a faɗin birnin na Kano.

  2. An ɗaura auren marayu fiye da 100 a jihar Neja

    ..

    An gudanar da ɗaurin auren marayu sama da ɗari a jihar Neja, waɗanda shugaban majalisar dokokin jihar ya ɗauki nauyi.

    Batun auren ya janyo cece-ku-ce a Najeriya bayan da ministar mata ta ƙasar Uju Kennedy-Ohanenye ta sha alwashin hana gudanar da auren tare da barazanar gurfanar da ɗan majalisar dokokin na jihar Neja a kotu.

    Sai dai daga baya ministar matan ta janye barazanar da ta yi tare da cewa ta samu tabbacin cewa waɗanda za a yi wa auren ba yara ne ƙanana ba.

    ...

    A yau Juma'a ne aka ɗaura auren wasu daga cikin marayun a fadar hakimin Mariga, yayin da aka gudanar da sauran ɗaurin auren a sauran gundumomin da ke ƙaramar hukumar ta Mariga.

    Daga bisani dai ɗan majalisar ya bayyana cewa ba za a gudanar da biki na bai-ɗaya na ɗaurin auren ba, sai dai ya miƙa wa iyalan amaren gudumawar da ya yi niyyar ba su.

  3. An kashe Turawan mishan uku a Haiti

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata ƙungiyar masu yaɗa addinin kirista ta Amurka ta ce an kashe wasu daga cikin mambobinta guda uku a Haiti ta hanyar harbi da bindiga.

    Ƙungiyar mai suna 'Mission in Haiti Inc" ta ce an kashe mutanen ne a wani gida wanda ƴan bindiga suka yi wa ruwan wuta.

    Ta ƙara da cewa biyu daga cikin waɗanda aka kashe ɗin mata da miji ne sabbin aure.

    Haiti na fama da matsalar ƙungiyoyin ƴan bindiga waɗanda suka jefar ƙasar cikin mummunan hali.

  4. Abu bakwai da Muhammadu Sanusi II ya faɗa lokacin karɓar takardar mulki

  5. Sojojin Najeriya sun kama 'masu kai wa' ƴan tawayen Kamaru man fetur

    ...

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Dakarun sojojin Najeriya sun ce sun kama wasu mutane 8 da suka ƙware wajen safarar man fetur daga Najeriya zuwa ga ƴan tawayen Ambazoniya a Jamhuriyar Kamaru.

    Rundunar sojin Najeriya ce ta bayyana hakan a ranar Juma'a inda ta ce an kama mutanen ne a kan hanyar Abong-Kurmi Baissa a jihar Taraba, a kan iyakar Najeriya da Kamaru.

    A yayin gudanar da bincike, waɗanda ake zargin sun amsa laifin safarar man fetur da kuma sayar da man ga ƴan tawayen Ambazoniya na Kamaru, waɗanda aka hana su shiga Najeriya don siyan kayan kai tsaye.

    A lokacin da aka kama su, waɗanda ake zargin suna tafiya ne a cikin motoci ƙirar J5 guda uku, ɗauke da jarkoki 605, kowace jarka shaƙe da lita 40 kuma darajar man da suke dauke da shi ya kai naira 19,360,000.

    Binciken da aka yi ya kai ga gano wasu ƴan ƙungiyar masu safarar man fetur ɗin, ciki har da jagoransu.

    ...

    Asalin hoton, Nigerian Army

  6. Kotu ta tabbatar da nasarar Uzodimma a matsayin gwamnan Imo

    .

    Asalin hoton, Hope Uzodimma/X

    Bayanan hoto, A watan Nuwamba ne aka zaɓi Hope Uzodimma a matsayin gwamnan Imo

    Kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamnan jihar Imo, ta tabbatar da nasarar Hope Uzodimma a matsayin halastaccen gwamnan jihar.

    Kotun - wadda ta yanke hukuncin a Abuja, ta yi watsi da ƙorafin jam'iyyar LP da ɗan takararta, Athan Achonu da suka shigar da ƙara suna ƙalubalantar nasarar Uzodimma.

    A hukuncin da alƙalan kotun uku - ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Oluyemi Akintan-Osadebay - suka yanke, sun ce zaɓen da aka yi Uzodimma an yi shi ne bisa doron dokar zaɓen ƙasar.

    Haka kuma kotun ta ce jam'iyyar LP ta gaza gabatar da hujjoji kan zarge-zargen da ta yi na aringizon ƙuri'u da rashin bin ƙa'idar dokar zaɓen.

  7. Hotunan yadda sarki Muhammadu Sanusi II ya karɓi takardar kama aiki

  8. 'Babu alamar maƙarƙashiya a hatsarin jirgin shugaban Iran'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Kafafen yaɗa labaran Iran sun ce babu alamar wata maƙarƙashiya a hadarin jirgin saman da ya yi sanadiyyar mutuwar Shugaban ƙasar a ranar Lahadi, kamar yadda sakamakon binciken da ake yi ya nuna ya zuwa yanzu.

    Rahoton farko daga sojojin ƙasar ya ce, ''babu alamar hujin harsashi ko wani abu mai kama da haka a jikin jirgin, kuma babu wani abin zargi a tattaunawar da aka yi tsakanin matuƙa jirgin da masu kula da tashin jirgin''.

    Rahoton ya gano cewa jirgin ya kama da wuta ne bayan ya tokari wani wuri da hazo ya rufe.

    Amma har yanzu sojojin na ci gaba da gudanar binciken.

    A ranar Alhamis ne aka binne Shugaba Ibrahim Raisi a birnin Mashhad, inda nan ne mahaifarsa.

  9. Kotun duniya ta umarci Isra'ila ta daina kai hari a Gaza nan take

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya ta umarci Isra'ila ta dakatar da hare-haren da take kai wa a yankin Rafah na Gaza ba tare da ɓata lokaci ba.

    Afrika ta Kudu ce ta shigar da ƙarar gaban kotun duniya bisa zargin Isra'ila da take yarjejeniyar kisan kiyashi.

    Ta ce shiga tsakanin na da muhimmanci domin tseratarwa da kuma kare rayuwar Falasɗinawa.

    Kakakin gwamnatin Isra'ila ya ce babu wani mai iko a doron kasa da zai hana ta kare mutanenta da kuma murkushe Hamas a Gaza.

    Kotun ICJ ba ta da ikon tursasawa amma duk wani hukunci da ta yi da bai yi wa Isra'ila dadi ba yana da tasiri a idon duniya.

  10. Kotu ta bayar da umarnin ƙwace kuɗi da wasu kadarori mallakin Emefiele

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata babbar kotun tarayya da ke zama a birnin Legas ta bayar da umarnin ƙwace kuɗi samada naira miliyan 800 da kuma wasu kadarori wadanda ke da jiɓi da tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

    Mai shari'a Yellim Bogoro ne ta bayar da umarnin a ranar Alhamis, bayan buƙatar da lauyar hukumar EFCC, Bilkisu Buhari ta shigar.

    Bayan sauraron ƙorafin da EFCC ta shigar, mai shari'a Bogoro ta ce: "Na saurari bayanin da mai shigar da ƙorafi ta yi kuma na amince.

    "Akwai ƙwararan hujjo game da buƙatar da ta gabatar, saboda haka na amince da buƙatar.

    Kuɗin da kotun ta umarci EFCC ta ƙwace sun kai dalar Amurka 4,719,054.

  11. Barcelona ta kori Xavi

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona ta sallami kocinta Xavi Hernandez bayan kammala kakar wasar bana ba tare da lashe kofi ba.

    Xavi zai bar Barcelona ne bayan wasan da ƙungiyar za ta yi da Seviilla a ranar Lahadi.

    Wanda ake sa ran zai maye gurbin Xavi a matsayin kocin Barcelona shi ne tsohon kocin Bayern Munich da Jamus, Hansi Flick.

  12. 'Sarki zai zauna a gidan gwamnati kafin shiga fadarsa'

    .

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce idan sarki ya kammala sallar juma'a, zai koma masaukinsa da ke gidan gwamnatin jihar inda hakimai za su ci gaba da kai gaisuwa ga sarki.

    Tuni manyan hakimai da sauran manyan masu riƙe da sarauta a masarautar Kano sun yi mubaya'a ga Sarki Muhammadu Sanusi II.

    Cikin jawabin sanar da naɗin sarkin da gwmanan jihar ya gabatar ranar Alhamis, ya ce ya bai wa duka sarakunan da aka rushe wa'adin sa'o'i 48 da su kwashe kayansu su fice daga fadojinsu, domin bai wa sabon sarki damar shiga fadar.

  13. Gwamanti da majalisa sun ceto tarihin Kano - Muhammadu Sanusi ll

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Muhammadu Sanusi ll ya ce da an bar batun rarraba masarautu a Kano, to da an ci gaba da rarraba masarautu a jihar kenan.

    ''Da an bar wannan lamari na rarraba masarautu to da wata rana sai an naɗa Sarkin Fagge, ko Kunci ko Kumbotso'', in ji shi.

    Dan haka sabon sarkin ya ce 'yan majalisa da gwamnatin sun ceto tarihi babba wanda yake haɗa kan al'umma.

    Muhammad Sanusi II ya ce sarki ba ya fadanci ba ya kirari amma yana faɗar gaskiya, yana mai cewa lalle gwamnan jihar ya cika gwarzo.

    Sarkin ya kuma gode wa gwamna da al'ummar Kano.

    Muhammadu Sanusi II ya ce babu wani wanda yake da wani gida a masarautar Kano duk zuri'ar Dabo ɗaya ce wanda shi ne ya kafa masarautar Kano.

    Haka kuma sabon sarkin ya ce ba zai tofa komai ba a kan waɗanda suka cire shi saboda a cewarsa ba su isa komai ba.

  14. A kan ƙa'ida ba ma tsoron kowa - Abba Gida-gida

    ..

    Asalin hoton, Abba Kabir/X

    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce sun bi duka ƙa'idojin da suka dace wajen soke dokar masarautun jihar.

    Yayin da yake gabatar da jawabi a gidan gwamnati lokacin miƙa takardar kama aiki ga sabon sarki, Gwamna Abba Kabir ya ce inda akan bin ƙa'ida ne to ba sa jin tsoron kowa.

    A jiya ne dai wata kotun tarayya ta bayar da umarnin dakatar da soke masarautun, bayan da Alhaji AMinu Babba Dan Agundi ya shigar da ƙara a gabanta, yana neman a soke sabuwar dokar.

    To sai dai cikin martanin da ya mayar game da hukuncin kotun, Abba Gida-gida ya ce dama tun da farko abin da ya hana su rushe masarautun da wuri shi ne nazari da kuma tuntubar ƙwararru don tabbatar da bin ƙa'ida.

    ''Kuma haka siddan ba za mu lamunci wani alkali yana can wata ƙasar ya bayar da umarnin a kan abin da muka bi ƙa'ida ba'', in Abba Kabir Yusuf.

    Sarki Muhammadu Sanusi II zai jagoranci sallar Juma'a a masallacin gidan gwamnatin jihar, ba kamar yadda aka tsara a baya cewa a masallacin kofar kudu ba

  15. Hotunan Muhammadu Sanusi ll lokacin bikin karɓar takardar naɗinsa

    .

    Asalin hoton, Kano State Govt

    Bayanan hoto, Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya miƙa wa Muhammadu Sanusi ll takarda naɗa shi a matsayin sabon sarkin Kano, bayan rushe masarautun jihar biyar.
    .

    Asalin hoton, Kano State Govt

    Bayanan hoto, Da hantsi ne Muhammadu Sanusi ll ya isa gidan gwamnatin Kano domin karɓar takardar kama aiki a hukumance a matsayin sabon sarkin masarautar Kano ɗaya tilo.
    .

    Asalin hoton, Kano State Govt

    Bayanan hoto, Manyan hakiman Kano da dama ne suka ɗakin taron, domin shaida bikin.
    .

    Asalin hoton, Kano State Govt

    Bayanan hoto, Ana sa ran sabon sarkin ne zai jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin sarki da ke Ƙofar Kudu.
  16. An sake samun gawarwakin Isra'ilawa uku da ake garkuwa da su a Gaza

    ..

    Asalin hoton, HANDOUT

    Dakarun sojin Isra'ila sun ce sun sake samun gawarwakin Isra'ilawa uku da ake garkuwa da su a Gaza.

    Cikin wata sanarwar da rundunar sojin ƙasar, IDF ta fitar, ta bayyana sunayen mutanen uku da Hanan Yablonka da Michel Nisenbaum da kuma Orion Hernandez.

    IDF ta ce an samu gawawarkin mutanen a garin Jabalia da ke arewacin Gaza cikin daren da ya gabata a wani samame da suka yi tare da haɗin gwiwar jami'an leƙen asirin ƙasar.

    Lamarin na zuwa ne mako uku bayan gano gawarwakin wasu Isra'ilawan uku a Gaza.

    Mutanen uku na daga cikin mutum 252 da mayaƙan Hamas ta yi garkuwa da su a harin 7 ga watan Oktoba, bayan da suka kashe kusan mutum 1,200.

    Har yanzu akwai kusa mutum 130 da mayaƙan Hamas ke tsare da su a Gaza, kamar yadda Isra'ila ta bayyana.

  17. Shugaban ƙasar Czech ya ji rauni a lokacin da yake tuƙa babur

    .

    Asalin hoton, PETR PAVEL/FACEBOOK

    Fadar shugaban Czech, ta ce an garzaya da shugaban ƙasar, Petr Pavel zuwa asibiti bayan da ya ji wa kansa rauni a lokacin da yake tuƙa babur.

    Fadar ta ce raunukan da shugaba Pavel ya ji, ba masu muni ba ne, sai dai ba ta yi ƙarin bayani ba.

    'Yan sandan Czech sun ce ba sa bincike kan lamarin, saboda hatsarin ya faru ne a wani killataccen wuri, ba a kan titi ba.

    Mista Pavel, mai shekara 62, na da sha'awar hawa babura.

    Ba wannan ne karo na farko da shugaban ya ji wa kansa rauni sakamakon hawa babur ɗin ba.

    A shekarar da ta gabata, ya fito bainar jama'a ya nemi afuwa sakamakon ganinsa da aka yi yana tuƙa babur ba tare da sanya hular kwano ba.

    A watan Maris ɗin shekarar da ta gabata ne, aka zaɓi mista Pavel a matsayin sabon shugaban ƙasar.

    Makonni bayan rantsar da shi ne ya tuƙa babur zuwa jihar Bavaria da ke kusa da kan iyakar ƙasar da Jamus.

  18. Jirgin ƙasan birnin Abuja zai ɗauki fasinjoji kyauta tsawon wata biyu - Wike

    Jirgin ƙasa na birnin Abuja

    Asalin hoton, Bashir Ahmad

    Ministan babban birnin Najeriya Abuja, Nyesom Wike, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da fara ɗiban fasinjoji kyauta a jirgi na ƙasa na birnin tsawon wata biyu.

    Wike ya bayyana haka ne yayin taron bayyana ayyukan da ma'aikatu ke yi shekara ɗaya da kafa gwamnatin ta Tinubu.

    A makon gobe ne dai ake sa ran ƙaddamar da jigilar fasinjoji ƙwaryar birnin tarayyar.

    ''Shugaban ƙasa zai ƙaddamar da layin dogon ranar 27 ga watan Mayu, sannan a fara jigilar mutane kyauta tsawon wata biyu'', in ji Wike.

    Sai dai hukumar kula da birnin Abuja ta ce yanzu an mayar da ranar ƙaddamarwar zuwa 29 ga wata.

    "Mutane da yawa na cewa gwamnatin baya ta ƙaddamar da shi. Mu ba maganar ƙaddamar da gine-gine muke yi ba, fara aikin jigilar mutane za mu ƙaddamar," in ji ministan.

  19. Sarki Muhammadu Sanusi ll ya isa gidan gwamnatin Kano

    b

    Muhammadu Sanusi ll ya isa gidan gwamnatin Kano domin karɓar takardar kama aiki a hukumance a matsayin sabon sarkin masarautar Kano ɗaya tilo.

    Rahotonni sun ce tun a cikin dare sabon sarkin ya isa Kano daga Legas inda ya zauna tun lokacin da aka tuɓe shi a shekarar 2020.

    Za a gudanar da ƙwarya-ƙwaryan biki a lokacin miƙa masa takardar da za a yi a gidan gwamnatin jihar.

    Ana sa ran sabon sarkin ne zai jagoranci sallar Juma'a a babban masallacin sarki da ke Ƙofar Kudu.

    Manyan hakiman Kano irin su Madakin Kano da Walin Kano da Sarkin Dawaki Mai Tuta da Sarkin Bai da Turaki duk sun hallara a ɗakin taron, domin shaida bikin.

    ..
  20. Mahamat Deby ya naɗa sabon firaminista

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Mahamat Idriss Deby

    Shugaban ƙasar Chadi Mahamat Deby ya sanar da naɗin tsohon jakadan ƙasar a China, Allamaye Halina a matsayin sabon firaministan ƙasar.

    Matakin na zuwa ne sa'o'i bayan shugaban ƙasar ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin sabon shugaban ƙasar mai cikakken iko.

    Tun da farko, Allamaye Halina ya yi aiki a matsayin babban daraktan kula da ɓaki a fadar gwamnatin ƙasar na tsawon shekara 13, kafin a naɗa shi jakadan ƙasar a China.

    Ana sa ran Mista Halina zai kafa sabuwar gwamnatin da za ta jagoranci jamhuriya ta biyar a ƙasar.

    A ranar Alhamis ne shugaba Deby ya karɓi takardar ajiye aiki daga tsohon firaministan ƙasar, Succes Masra, wanda ya kasance babba abokin hamayyarsa a zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a farkon wannan Mayun da muke ciki.

    To sai dai Mista Deby ya umarci duka sauran jami'an gwamnatinsa su ci gaba da riƙe muƙamansu har zuwa lokacin da zai sanar da naɗin sabbin ministocin sabuwar gwamnatin.

    Tuni dai Mista Masra ya shigar da ƙara domin ƙalubalantar nasarar tsohon mai gidan nasa a zaɓen.