Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 22/05/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 22 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza, Usman Minjibir, Umar Mikail and Haruna Kakangi

  1. Ma'aikatar wajen Falasɗinawa ta yi maraba da matakin ƙasashe uku

    Ma'aikatar harkokin wajen Falasɗinawa ta yi maraba da matakin ƙasashen Spain, Norway da Ireland suka ɗauka na amincewa da yankin Falasɗinawa a matsayin ƙasa mai cin gashin kai.

    Cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce ''wannan muhimmin mataki ne, kuma abin as yaba ne, ƙasashenn Norway da Ireland da kuma Spain sun nuna buƙatarsu na samun kafuwar ƙasashe biyu a matsayin hanyar masalaha domin yi wa Falasɗinawa adalci''.

    "Haka kuma ,matakin da ƙasashen uku suka ɗauka ya yi daidai da dokokin duniya da na Majalisar Dinkin Duniya, wanda kuma hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen mamayar da Isra'ila ke yi wa yankunan Falasɗinawa domin wanzar da zaman lafiya a yankin.''

    Sanarwar ta kuma buƙaci ƙasashen uku da su gaggauta ɗaukar wannan mataki da suka amince da shi.

  2. Firaiministan Chadi ya ajiye aikinsa bayan tabbatar da nasarar Deby

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaiministan Chadi, Success Masra ya miƙa takardar murabus bayan da aka tabbatar da nasarar sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Mahamat Idriss Deby a zaɓen da aka yi na ranar 6 ga watan Mayun 2024.

    An dai naɗa Masra ne a matsayin firaiminista a gwamnatin rikon kwarya domin kyautatawa masu hamayya da juyin mulkin da aka yi a 2021.

    A watan Maris ne dai hukumar zaɓen ƙasar ta amince da takarar mista Masra a matsayin ɗan takarar shugabancin ƙasar da zai fafata da Mahamat Deby.

    To sai dai tun dai kafin sanar da sakamakon zaɓen na farko-farko, Masra ya ce shi ne ya lashe zaɓen, inda ya ce an tafka maguɗi.

    Hukumar Zaɓen Chadi ta ce Deby ya lashe zaɓen ne da kaso 61 na dukkan ƙuri'un da aka kaɗa saboda shi ne ya yi nasara.

    Sai dai kuma Masra wanda ya yi takarar da Deby ya yarda abin da hukumar ta ayyana bisa cewa babu wata damar da ta rage masa da kin amince wa da sakamakon.

    " Bisa tsarin kundin mulki, yau na miƙa takardar murabus da kuma ta gwamnatin rikon kwarya wadda ta zama tamkar ba ta d amfani bayan zaɓen ranar 6 ga watan Mayu". In ji Masra, a shafinsa na X.

  3. Gwamnati ta gargaɗi 'yan Najeriya kan shan gishiri fiye da ƙima

    ..

    Asalin hoton, Ministry of Health

    Gwamnatin Najeriya ta ja hankalin 'yan ƙasar da su rage yawan shan gishiri a abincinsu na yau da kullum domin kariya daga cutuka da ke saurin kisa.

    Ministan lafiyar ƙasar, Farfesa Muhammad Ali Pate ne ya yi gargaɗin a ranar Talata lokacin bikin makon taƙayta shan gishiri a Abuja.

    Ministan ya ce "shan gishiri fiye da ƙima gishiri na da illa a rayuwarmu inda yake ta'azzara cutar hawan jini wadda ke haddasa bugun zuciya da shanyewar ɓrin jiki".

    Ya ƙara da cewa shan gishiri fiye da ƙima a Najeriya babban abu ne da ke taimakawa da kaso 10 na mace-macen da ake yi a ƙasar.

  4. Fubara ya rantsar da sabbin kwamishinoni takwas

    ..

    Asalin hoton, Siminalayi Fubara/X

    Bayanan hoto, Sabbin kwamishinonin da Fubara ya rantsar

    Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya rantsar da sabbin kwamishinoni takwas da majalisar dokokin jihar ta tantance ranar Talata.

    An gudanar da bikin rantsar da sabbin kwamishinonin a gidan gwamnatin jihar da ke birnin Fatakwal cikin daren jiya, sa'o'i bayan tantacewar majalisar.

    Yayin da yake jawabai bayan rantsar da kwamishinonin, Gwamna Fubara ya yi kira a gare su su riƙa adana ayyukan da suka gudanar a ma'aikatunsu.

    Gwamnan ya ce adana ayyukansu zai taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati a kowane mataki, musamman saboda hakan zai taimaka wa waɗanda za su gaje su a nan gaba, su san inda za su ɗora.

    Fubara ya bayyana damuwarsa kan yadda ya ce tsoffin kwamoshinonin da suka ajiye aiki musamansu, suka kasa adana tarihin ayyukan da suka gudanar a ma'aikatunsu.

    A cikin mako biyu da suka gabata ne wasu kwamishinoni jihar masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike suka ajiye muƙamansu sakamakon abin da wasunsu suka kira da rashin kyawun yanayin aiki.

    Jihar Rivers da ke kudu maso kudancin Najeriya, mai arzikin man fetur ta faɗa rikicin siyasa ne bayan taƙun saƙar da ta kunno kai tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da ministan Abuja, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike.

    Wike da Fubara dai dukansu 'yan jam'iyyar adawa ta PDP ne.

  5. Ƙasashen Spain, Ireland da Norway za su amince da ƙasar Falasɗinawa

    .

    Asalin hoton, ..

    Ƙasashen Sifaniya da Norway da kuma Ireland na shirin amincewa da ƙasar Falasɗinawa cikin mako mai zuwa.

    Ƙasashen uku sun ce a ranar 28 ga watan Mayun da muke ciki za su amince da matakin.

    Minista harkokin wajen Ireland, Micheál Martin, ya ce ''a yau mun bayyana ƙarara ba tare da ƙumbiya-ƙumbiya ba za mu nuna goyon bayanmu game da 'yancin tsaro da na mutuntawa da gashin kai ga mutanen ƙasashen Falasɗinu da Isra'ila''.

    Firaministan Madrid, Pedro Sanchez, ya ce firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ''yayi ƙunnen ƙashi, inda yake ci gaba da kai hare-haren boma-bomai kan asibitoci da makarantu tare da azabtar da mata da ƙananan yara da yunwa da kuma tsananin sanyi''.

    A nasa ɓangare firaministan Irelan, ya ce ''samun yancin ƙasashen biyu shi ne kawai mafita a ƙoƙarin samar da zaman lafiya''.

    Ƙasashen duniya da dama sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa.

    A farkon wannan watan ƙasashe 143 daga cikin ƙasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya 193, sun kaɗa ƙuri'ar amince da da Falasɗinu ta shiga cikin MDD, wani abu da ƙasa mai zaman kanta ne kawai ke samun damar haka.

  6. Hayaƙin janareta ya kashe mutum bakwai a Bayelsa

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Mutum bakwai sun mutu sakamakon hayaƙin injin janareto da ya mamaye ɗakin da suke kwace a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

    Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa an samu gawarwakin mutanen galibinsu ɗaliban Jami'ar Niger Delta a cikin dakin kiɗe-kiɗe watau 'studio' ranar Talata da safe, bayan sun shaƙi hayaƙin injin.

    Jaridar ta ce sutudiyan na ɗaya daga cikin mutanen da suka mutun ne.

    An ce a ranar Litinin da daddare ne marigayan suka fara aiki a sutudiyan, sai barci ya ɗauek su sakamakon gajiyar da suka yi, ba tare da sun kashe injin ba.

    Jaridar ta ce ko da gari ya waye ranar Talata, sai aka samu gawar mutum shida daga cikinsu, yayin da ɗayan ke cikin mawuyacin hali inda nan take aka garzaya da shi asibiti, kafin shi ma ya rasu a asibitin.

    Hayaƙin janareta dai na ɗauke da wani sinadari da ke toshe hanyoyin shaƙar iska, lamarin da ke barazana ga rayukan mutane.

  7. Jirgin da ya gamu da mummunar gargada a samaniya ya sauka a Singapore

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    Fiye da fasinjoji da ma'aikatan jirgi 140 - da ke cikin jirgin da ya gamu da mummunar gargada a sararin samaniya - ne suka sauka a filin jirgin saman Singapore da safiyar yau.

    Fasinjojin jirgin wanda ya taso daga London zuwa Singapore, sun ce sun shiga mummanan firgici a lokacin da lamarin ya faru.

    Wata daga cikin fasinjojin ta ce ta ga wata mata da mummunan rauni a kanta, yayin da ta ce mutanen jirgin sun yi ta kururuwa sakamakon firgicin da suka shiga.

    Geoff Kitchen, ɗan asalin Birtaniya mai shekara 73, ya mutu sakamakon bugun zuciya da ake tunanin ya kamu da shi, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka.

    Rahotoni na cewa mista Kitchen na kan hanyarsa ne ta zuwa Singapore domin fara hutun mako shida tare da matarsa wadda ita ma ke cikin jirgin.

    Jirgin - wanda da farko ya nufi Singapore- ya sauya akalarsa inda ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Bangkok, bayan faruwar lamarin a lokacin da yake tsaka da keta hazo.

    Har yanzu akwai fasinjoji 79 da ma'aikatan jirgin da ke samun kulawar likitoci a Bangkok sakamakon raunukan da suka samu.

  8. NLC ta sake yin fatali da N54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

    ..

    Asalin hoton, NLC

    Gamayyar ƙungiyoyin ƙwadago na Najeriya sun sake yin fatali da tayin mafi ƙarancin albashi na naira 54,000 da gwamnatin ƙasar ta amince za ta biya.

    A tataunawar da ƙungiyar ta yi da kwamitin ƙarin albashi da gwamnatin Najeriya ta kafa, kwamitin ya yi tayin biyan naira 54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan ƙasar.

    Hakan ƙari ne a kan naira 48,000 da kwamitin gwamnatin tarayyar ya yi tayin biya a zaman da ɓangarorin biyu suka yi cikin makon da ya gabata.

    NLC ta ce ta yi watsi da tayin ne sakamakon halin matsin rayuwa da ake fuskanta a ƙasar.

    Ɓangarorin biyu za su sake zama a yau Laraba domin ci gaba da tattaunawar kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar.

    Tun da farko dai NLC ta ce tana so gwamnatin ƙasar ta biya naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, la'akari da halin da ake ciki a ƙasar na ƙaruwar hauhawar farashi da karyewar darajar kudin ƙasar.

  9. An saki 'ya jaridar da ta fitar da labarin ɓullar annobar Korona

    .

    Asalin hoton, YouTube/Screenshot

    Kungiyar 'yan jarida ta duniya, RSF ta ce 'yar Jaridar Chinar nan da aka garkame a gidan yari shekaru huɗu yanzu bayan rahotan da ta fitar kan ɓarkewar annobar Korona a Wuhan ta shaki iskar yanci, bayan sakinta daga gidan yari.

    Tun a makon da ya gabata ne ake sa rai da sakin Zhanga Zhan tun, sai dai an fuskanci tsaikon da ya haifar da fargaba tsakanin 'yan jarida.

    Sai dai daga baya Kungiyar RSF ta wallafa wani bidiyo da ya nuna 'yar jaridar na cewa an saketa bisa yada aka tsara, tare da gode wa duk waɗanda suka nuna mata goyon-baya.

    RSF ta ce har yanzu akwai sauran damuwa kan 'yancin yan jarida.

  10. Amurka na zargin Rasha da yi wa taurarin ɗan-adam na duniya kutse

    .

    Asalin hoton, ISRO

    Amurka ta ce Rasha ta harba wani tauraron ɗan adam a makon da ya gabata wanda take da yaƙinin zai rinka kutse ga sauran taurarin ɗan-adam.

    Kakakin ma'aikatar tsaro ta Pentagon, Janar Pat Ryder ya ce wannan wani makami ne da zai riƙa haifar da cikas ga taurarinsu, kuma kusan wuri ɗaya suke da taurarin gwamnatin Amurka.

    Mista Ryder ya ce Amurka na sa ido sosai kan lamarin kuma dole ta kasance a cikin shirin kare kanta.

    Rasha da Amurka dai sun yi ta jayayya kan makaman sararin samaniya a taron MDD, inda Moscow ta zargi Washington da ƙoƙari yi mata kane-kane a sararin samaniyarta.

  11. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkamu da safiyar ranar Talata, ta Bawa ranar samu kamar yadda Hausawa ke yi mata kirari.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku a dai dai wannan lokaci domin kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya, musamman Najeriya da sauran ƙasashe.

    Kuna kuma iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafawar a shafukanmu na sada zumunta.