Mutum ɗaya ya mutu, 30 sun ji rauni bayan jirginsu ya haɗu da gargada a sama

Asalin hoton, Getty Images
Fasinja ɗaya ya mutu wasu sama da 30 sun ji rauni a cikin wani jirgin sama na ƙasar Singapore da zai koma ƙasar daga London bayan da ya gamu da mummunar gargada a sama.
Sakamakon lamarin an karkatar da jirgin ƙirar Boeing 777-300ER zuwa Bangkok, inda ya sauƙa a can.
Jirgin mai lamba SQ 321 yana ɗauke da fasinja 211 da ma'aikatansa 18 kamar yadda wata sanarwa da kamfanin jirgin ya fitar.
Ana can ana ci gaba da kula da wadanda suka ji raunin da taimakon hukumomin Thailand, inda aka tashi wata tawaga ta musamman ta ma'aikatan lafiya daga Singapore din domin ba su kulawa.
Zuwa yanzu ba a san takamaimai abin da ya faru a cikin jirgin ba bayan da ya gamu da gargadar a sama.
Abu ne da aka saba jirgi ya gamu da gargada a sama, to amma irin wannan mai tsanani ba kasafai ake haduwa da ita ba.
Wani lokaci akan iya hasashen gargadar - kuma matuka jirgin sama sukan aika da sako ga takwarorinsu da ke hanya domin gargaɗinsu, to amma kuma matsalar kan faru kwatsam - kuma za ta iya faruwa a ko'ina kuma a kodayaushe.







