Dubban Iraniyawa na halartar jana'izar Ebrahim Raisi

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 20 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Muhammad Annur Muhammad

  1. Tinubu ya buƙaci a hukunta wanda ya cinna wa masallaci wuta a Kano

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci hukumomin tsaro su tabbatar an yi kyakkywan bincike tare da hukunta duk wanda ke da hannu a cinna wuta a masallaci wanda ya yi sanadiyyar hasarar rayuka a jihar Kano.

    A cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale, a yau Talata, Tinubu ya jajanta wa mutanen da suka rasa ƴan uwansu sanadiyyar lamarin da kuma yin addu'ar waraka ga waɗanda suka samu rauni.

    Wani matashi mai shekara 39 a makon da ya gabata ya cinna wa masallaci wuta a ƙauyen Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

    Lamarin ya yi sanadin rayukan mutum 17 yayin da dama ke ci gaba da jinya a asibiti.

    Tuni dai aka gurfanar da wanda ake zargi a wata kotun shari'ar musulunci da ke birnin Kano a ranar Litinin.

    Duk da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa, alƙalin kotun ya ɗage shari'a zuwa ƙarshen wannan wata na Mayu domin bai wa wanda ake zargi damar ɗaukar lauya da kuma bai wa masu ƙara damar agabatar da shaidu.

  2. Hotunan taron Majalisar ECOWAS da ke gudana a Kano

    A

    Asalin hoton, facebook/Barau Jibrin

    Majalisar ECOWAS ta shida, na gabatar da babban taronta karo na biyu a wannan shekarar, wanda zai mayar da hankali kan matsalolin al’ummar kasashen da suke mambobinta.

    Taron na kwana shida na gudana ne a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

    Kuma ya samu halartar wakilai daga kasashe mambobin ECOWAS sama da 100.

    Ga dai wasu daga cikin hotunan yadda taron ke gudana.

    A

    Asalin hoton, facebook/KAWU Sumaila

    A

    Asalin hoton, Instagram/Mr La

    a

    Asalin hoton, Facebook/Kawu Sumaila

    A

    Asalin hoton, facebook/Kawu Sumaila

    a

    Asalin hoton, Facebook/Kawu Sumaila

  3. Pakistan na shirya wa tunkarar yanayin zafi mai tsanani

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ai a lardin Sind da ke Pakistan sun ce an samar da sansanoni sama da dubu daya a fadin yankin, gabanin wani tsananin zafi da a yanzu haka aka fara fuskanta a wasu sassan Pakista da ma India baki daya.

    Hukumar agajin gaggawa ta yankin ta ce yanayi zai iya kaiwa gidiri 50 a ma'aunin Salshiyos a wasu yankunan.

    Ta ce an samar da ruwa da wasu kayan aiki a sansanonin domin taimakawa mutanen da zafin zai shafa. Pakistan dai ba bakuwa ba ce wajen fuskantar yanayi irin wannan.

    Ko a bayan nan, ta fuskanci wani ruwa sama da ya haifar da ambaliya a kasar.

  4. Bai kamata ƴan Najeriya su sake amince wa Atiku da Peter Obi ba - APC

    ...

    Asalin hoton, facebook/multiple

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce bai kamata al'ummar Najeriya su amince da mutanen da suka gaza warware matsalolin da ke fuskantar jam'iyyunsu ba, kamar Atiku Abubakar da Peter Obi, a matsayin wadanda za su magance matsalolin ƙasar ba.

    Hakan na zuwa ne bayan raɗe-raɗin da ake yi kan cewa akwai yiwuwar Atiku Abubakar na babbar jam'iyyar adawa ta PDP, da Peter Obi na jam'iyyar LP na iya haɗewa a ƙoƙarin tuntsurar da gwamnatin APC a babban zaɓen Najeriya mai zuwa.

    A cikin wata sanarwa da APC ta fitar, ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaru na jam'iyyar, Felix Morka, ta bayyana cewa duk wani haɗin kai tsakanin Atiku da Obi ba komai ba ne face "ci-da-zucin mutanen biyu na ganin sun zama shugaban ƙasa".

    Sanarwar ta ce mutanen da suka gaza warware matsalolin jam'iyyunsu ba za su iya warware matsalolin siyasa da tattalin arziƙi masu sarƙaƙiya ba irin na Najeriya.

    A wata tattaunawa da BBC cikin makon da ya gabata, Atiku Abubakar bai fito ƙarara ya bayyana cewa za a sake haɗewa tsakanin sa da Peter Obi ba ko kuma a'a, domin tunkarar zaɓe mai ƙaratowa ba.

    Sai dai ya ce za su haɗa kai domin ci gaba da adawa da "rashin adalci da ake yi a ƙasar".

    Atiku Abubakar ne ya zo na biyu a zaɓen shugaban Najeriya na 2023 yayin da Peter Obi na jam'iyyar LP ya zo a matsayi na uku a zaɓen da Bola Ahmed Tinubu ya lashe.

    Atiku Abubakar da Peter Obi sun taɓa yin takarar shugaban ƙasa da mataimaki ƙarƙashin jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban Najeriya na 2019, sai dai ba su yi nasara ba, inda shugaban ƙasa mai ci a wancan lokacin Muhammadu Buhari ya lashe zaɓen da tazarar ƙuri'a sama da miliyan uku.

  5. An tsinci gawar mutum 12 a gefen kasuwa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    An tsinci gwawwaki aƙalla 12 a birnin Acapulco na ƙasar Mexico.

    Uku daga cikin gawawwakin an kashe ne lokacin musayar wuta yayin da aka gano wasu gawawwakin shida a kusa da wata kasuwa: inda wata mota ta jibge su.

    Gawa ta goma kuwa na wani mutum ne da aka harbe a wata unguwar da ke jan hankalin masu yawon shaƙatawa . An kuma gano wasu mutanen biyu na daban da aka kashe.

    Acapulco, ɗaya daga cikin wuraren yawon shakatawa mafi shahara a Mexico na fuskantar ƙaruwar matsalar kashe-kashen gilla waɗanda ake alaƙantawa da ƙungiyoyin ƴan daba.

    Garin na a jihar Guerrero ce wadda matsalar masu safara ƙwaya ta addaba.

  6. Rasha ta fara atisayen amfani da makamin nukiliya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Rasha ta ce ta fara atisayen amfani da makaman nukiliya kamar yadda ta sanar a farkon wannan wata.

    Kashi na farko na atisayen ya ƙunshi na makaman Iskander da kuma na makaman Kinzhal masu tafiyar fitar hankali.

    Rasha ta bayyana atisayen a matsayin martani kan abin da ta kira barazana daga ƙasashen yamma.

    Rashar ta fara atisayen ne bayan Birtaniya ta bayyana cewa Ukraine za ta iya amfani da makamanta domin kai hari a wasu yankuna cikin Rasha, sannan Faransa ta ƙi kawar da batun yiwuwar tura dakaru zuwa Ukraine.

    Ukraine dai ta yi watsi da atisayen na Rasha.

  7. Abin da ya sa muka rufe rukunin shagunan Banex a Abuja - Sojoji

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Najeriya ta ce ta rufe rukunin shagunan Banex da ke Abuja ne domin gudanar da bincike kan ayyukan da ta bayyana a matsayin na masu aikata ɓarna.

    A farkon makon nan ne aka ga wani faifan bidiyo na yawo a shafukan sada zumunta na wasu mutane da suka far wa wasu sojoji a kusa da rukunin shagunan.

    Bidiyon ya nuna yadda wasu jami'an ƴansanda suka shiga tsakani domin ceton jami'an sojin da mutane suka riƙa kai wa duka da jifa.

    A cikin wata sanarwa da ta fitar, wadda ta samu sa hannun daraktan hulɗa da jama'a na rundunar sojin ƙasa ta Najeriya, Onyema Nwachukwu, ta bayyana cewa "wasu maɓarnata ne da ba a san ko su wane ne ba suka kai mummunan hari kan wasu jami'an sojojin Najeriya, wadanda da ƙyar ƴansanda suka ceto su daga hannun mutanen".

    Sanarwar ta ci gaba da cewa "a dalilin haka ne hukumomin sojin suka yi wata ganawa da shugabannin rukunin shagunan na Banex domin ganin yadda za a zaƙulo waɗanda suka aikata ta'asar, wanda a dalilin haka ne aka rufe tare da dakatar da duk wata hada-hada a rukunin shagunan na Banex".

    Sanarwar ta ƙara da cewa "an ɗauki matakin ne domin tabbatar da tsaro a yankin birnin tarayya tare da daƙile duk wani yunƙuri na ƙaddamar da irin wannan hari a kan jami'an soji da sauran jami'an tsaro."

    Rukunin shagunan Banex ɗaya ne daga cikin wauraren hada-hadar kasuwanci mafiya shahara a Abuja, babban birnin Najeriya.

    Wuri ne wanda ya shahara a harkar saye da sayar da wayoyin hannu da sauran na'urorin amfani na yau da kullum.

  8. Kotun Girka ta yi watsi da ƙarar jirgin ƴangudun hijira

    ,,,,,,

    Asalin hoton, Greek Coast Guard

    Wata kotu a ƙasar Girka ta yi watsi da ƙarar da aka shigar da wasu Misirawa tara da ake zargi da haddasa hatsarin jirgi ƴangudun hijira mafi girman a tekun Bahar rum a cikin shekaru goma.

    Alƙalai a birnin Kalamata mai tashar jiragen ruwa sun yanke hukuncin cewa ba su da hurumin sauraron ƙarar saboda jirgin ruwa ya nutse ne a tekun ƙasa da ƙasa.

    Ana fargabar fiye da ƴangudun hijira 600 ne suka mutu a cikin jirgin a watan Yunin shekarar da ta gabata sakamakon cikar kwari da mutane suka yi a jirgin na masunta, a kan hanyarsu ta zuwa Turai daga Libya.

    Waɗanda ake zargin na fuskantar hukuncin ɗaurin rai-da-rai idan da an kama su da laifin safarar mutane tare da haddasa nutsewar jirgin.

    Sai dai masu zanga-zanga da ke wajen kotun sun ɓuge da shewa a sa'ilin da suka ji hukuncin kotun.

    Ƙungiyoyin kare hakkin bil'adama ciki har da Amnesty International da Human Rights Watch sun ce suna da shakku matuƙa game da gaskiyar binciken da kuma hujjojinsu.

  9. Ƴan bindiga sun afkawa sansanin sojin Nijar

    ,,,

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga jahar Tillabery da ke jamhuriyar Nijar na cewa wasu mahara sun afkawa wani sansanin sojin ƙasar.

    Maharan ɗauke da miyagun makamai sun isa sansanin sojin da ke yankin kan iyakoki uku a Boni, yankin Makalandine a kan babura da motoci.

    Bayanai sun nuna cewa an kwashe sa'o'i ana musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

    A ranar Litinin da daddare ne ƴanbindigan suka kai harin, inda aka yi ta artabun zuwa ranar Talata.

    Kuma kawo yanzu babu cikakken bayani kan yawan mutanen da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata a lokacin harin.

    Sai dai wasu rahotanin na cewa maharan sun kwace iko da sansanin.

    Ko a jiya a garin Diambala na Sakoira a jahar ta Tillabery farar hula da dama sun rasa rayukansu ta dalilin wani hari da ƴanbindiga suka kai, inda rahotanni ke cewa kawo yanzu an yi wa gawawwaki 22 sutura.

  10. Yajin aiki ya yi sanadin mace-macen marasa lafiya a Mozambique

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Ɗaruruwan marasa lafiya sun rasa ransu a Mozambique cikin wannan wata sanadiyyar yajin aikin wani ɓangare na ma'aikatan lafiyar ƙasar, kamar yadda wani jagoran ƙungiyar ƴan ƙwadago ya shaida wa BBC.

    Malaman jinya da masu kula da na'urorin aikin asibiti ne suka tsunduma yajin aiki a ƙarshen watan Afrilu bayan watsewar tattaunawa da ake yi tsakaninsu da gwamnati kan bunƙasa yanayin aiki.

    Ma'aikatan lafiya sun shiga yajin aiki sau da dama a cikin watanni 18 da suka gabata.

    Kimanin ma'aikata 50,000 ne suke yajin aiki a faɗin Mozambique, lamarin da ke haifar da dogon layin ganin likita yayin da wasu da dama ba su samun damar ganin likitan kwata-kwata.

    Wani jagoran ƙungiyar ma'aikatan lafiya, Anselmo Muchave ya shaida wa BBC cewa sama da mutum 1000 ne suka mutu sanadiyyar yajin aikin.

    Ma'aikatan lafiya a Mozambique na neman gwamnati ta bunƙasa yanayin aiki - da biyan su alawus ɗin aiki da kuma samar da ingantattun kayan aiki.

    Wata mata ta shaida wa BBC cewa kakarta ta kwashe sama da sa'a 15 tana kan layin ganin likita a wani asibitin gwamnati a makon da ya gabata.

    Hukumomin ƙasar ba su ce uffan ba game da lamarin a lokacin da BBC ta tuntuɓe su, sai dai a baya sun sha zargin ƙungiyoyin ma'aikatan da zuzuta matsalolin da ake fuskanta.

  11. Ronaldo zai buga wa Portugal Euro 2024

  12. Ƴaƙi ya ƙara cabewa a yankin Darfur ta Arewa a Sudan

    'ƴan gudun hijira a Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Rahotanni daga yammacin Sudan na cewa ana ta samun artabu a yankin El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa.

    Wakilin BBC ya ce wasu majiyoyi sun shaida masa cewa rikicin ya munana a jiya Litinin, kuma ko ta ina hare-hare ake kaiwa.

    Ƙungiyar bayar da agaji ta likitoci ta Medicins sans Frontiere ta ce an kashe akalla mutum 85 kuma sama da 60 sun ji rauni.

    Ƙungiyar likitocin ta ce dakarun RSF, da ke yaƙar sojojin ƙasar sun yi ta harba makamai yankin fararen hula.

    Sai dai RSF din ta ce harin da sojin Sudan suka kai ta sama ne ya yi sanadin mutuwar fararen hular, inda ta ce ya lalata hanyoyin samar da lantarki a birnin baki daya.

  13. Kotun Rasha ta ɗaure ƙwarren masanin kimiyya kan cin amanar ƙasar

    Hotunan masana kimiyya

    Asalin hoton, OTHERS

    Wata kotun Rasha da ta yi zamanta a sirrance ta samu masanin kimiyyar nan Anatoly Maslov da laifin cin amanar ƙasa, kuma ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekara 14.

    An zargi Maslov mai shekara 77 da fitar da wasu bayanai masu muhimmanci game da shirin Rasha na makamai masu linzami

    Rahotanni sun ce lauyoyin Maslov sun soki hukuncin da aka yanke masa, suna cewa tsaurin hukuncin ya yi daidai da hukuncin kisa.

    Ƙwararren yana ɗaya daga cikin masana kimiyya uku da aka tuhuma, waɗanda suka fito daga cibiyar ilimi ta Sabiya.

    A bara ne wasu abokan karatunsa suka wallafa wata wasiƙa da ke cewa mutane ukun da aka kama ba su yi laifi ba, kuma ana son hukunta su kan abin da suka yi da bai taɓa zama laifi ba tsakanin masana kimiyya.

  14. Kroos zai yi ritaya daga taka leda bayan Euro 2024

  15. Tarayyar Turai ta amince a yi amfani da kuɗin Rasha wajen saya wa Ukraine makamai

    Igwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Tarayyar Turai ta amince a yi amfani da ribar kadarorin babban bankin Rasha, da aka dakatar wajen saya wa Ukraine makamai.

    Za a tura ribar wadda ta haura dala biliyan uku zuwa Kyiv, a wannan shekarar, inda za a kashe mafi yawanta a bangaren tsaro.

    Tarayyar Turai ta dakatar da kudin Rasha da suka haura dala biliyan 200, a matsayin wani bangare na takunkumi da aka sanya wa Moscow a 2022 bayan mamayar da ta yi wa Ukraine.

    Ministan harkokin wajen Czech ya ce lokaci ya yi da Rasha za ta biya bashin da ta ci na lalata Ukraine.

    A baya Rasha ta yi barazanar za ta mayar da martani matukar aka ɗauki wannan matakin a kanta.

  16. Majalisar dokokin Kano za ta gyara dokar da ta kafa sabbin masarautu

  17. An ɗaure malamin jami'a a Mali saboda sukar gwamnatin sojan ƙasar

    Mali

    Asalin hoton, AFP

    An yanke wa wani fitaccen masanin tattalin arziki kuma malamin jami'a hukuncin ɗaurin shekara biyu a gidan yari, a Mali saboda sukar gwamnatin mulkin sojin ƙasar.

    Bayan hukuncin ɗaurin, Farfesa Étienne Fakaba Sissoko zai kuma biya tarar kuɗi ta CFA miliyan uku kwatankwacin dala 4,900.

    Sai dai ɗaya daga cikin hukuncin na je-ka-ka-gyara-halinka ne - wato ba zai yi zaman gidan yarin ba na shekara, har sai idan ya ƙara laifi.

    An tuhumi malamin mai shekara 41, wanda yake tsare tun watan Maris, da laifin ɓata sunan ƙasar ta hanyar yaɗa labaran ƙarya.

    Tuhumar ta danganci wani littafi da ya rubuta ne a bara, tuhumar da ya kare a kotu, yana mai cewa littafin ya dogara ne ga bayanai na gaskiya ba shaci-fadi-ba.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'Adam sun ce hukuncin nasa shi ne na baya-bayan nan a kan ƙoƙarin rufe bakin masu suka da aboka hamayya na siyasa da sojojin masu mulki ke yi.

    Sojojin sun hau mulki ne a watan Agusta na 2020 bayan sun hamɓarar da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta bayan gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnai a kan yadda gwamnatinsa ke tunkarar matsalar masu iƙirarin jihadi.

  18. Ko Jonathan zai iya sasanta rikicin Wike da Fubara?

  19. Majalisar Wakilan Najeriya za ta yi bincike kan yawan lalacewar jiragen saman shugaban ƙasar

    Shugaba Tinubu zai hau jirgin sama

    Asalin hoton, STATE HOUSE

    Kwamitin tsaron ƙasa da bayanan sirri na majalisar wakilan Najeriya ya yanke shawarar kafa kwamitin ƙawararru don maganace matsalar da ke janyo yawan lalacewar jiragen sama na fadar shugaban kasar.

    A jiya Litinin ne ƴan kwamitin suka yi wata ganawar sirri da kwamandan da ke kula da jiragen saman shugaban ƙasar, Air Vice Marshal Olayinka Olusola, a majalisar, a Abuja, domin tattaunawa a kan abin da ya kai ga Shugaba Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima suka yi amfani da jiragen haya a kwanan nan.

    A watan Afirilu ne Shugaban ya yi amfani da jirgin haya daga Netherlands zuwa Saudiyya domin halartar taron koli na duniya kan tattalin arziƙ.

    Haka kuma mako biyu da ya gabata aka soke tafiyar da Mataimakin Shugaban Ƙasar Kashim Shettima zai yi inda zai wakilci Shugaba Tinubu a taron koli na hadin gwiwa tsakanin Amurka da Afirka kan kasuwanci saboda matsalar da jirgin da zai hau ya gamu da ita.

    Shugaban kwamitin tsaro na majalisar Ahmad Satomi ya ce a muhawarar da suka yi kan batun, ƴan majalisar sun yanke shawarar gayyatar mai bai wa shugaban kasar shawara kan tsaro Nuhu Ribadu da kuma kwamandan da ke kula da jiragen fadar shugaban kasar da su je su yi bayani kan yawan lalacewar jiragen saman duk da maƙudan kuɗaɗen da ake ware musu a kasafin kuɗin duk shekara don kula da su.

  20. Ƴanbindiga sun kashe sama da mutum 40 da jikkata da dama a jihar Plateau

    Hoton ƴanbindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu ƴanbindiga sun kai hari ƙauyen Zurak da ke gundumar Bashar, a ƙaramara hukumar Wase, ta jihar Filato, inda suka kashe sama da mutum 40 da suka haɗa da 'yan sa-kai.

    Rahotanni na cewa gungun ƴanbindigar ya kai harin ne da yamma wajen ƙarfe biyar ranar Litinin a lokacin jama'a na gudanar da harkokinsu.

    Al'ummar ƙauyen sun ce ba su iya bayar da rahoton harin ba saboda rashin kyakkyawar hanyar sadarwa a yankin.

    Wani daga cikin mutanen garin ya ce ƴanbindigar sun yi musu dirar-mikiya ne a kan babura ɗauke da manyan makamai inda nan da nan suka riƙa harbin kan mai-uwa-da-wabi.

    Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigar sun kashe mutum sama da 40, yayin da suka raunata wasu da dama, kuma suka rika cinna wa gidaje wuta.

    Mutane sun gudu zuwa cikin daji da wasu garuruwan da ke maƙwabtaka da su domin tsira.

    Kakakin gwamnan jihar ta Filato, Mr. Gyang Bere, ya tabbatar wa da BBC lamarin, sai dai bai bayyana yawan mutanen da lamarin da rutsa da su ba.

    Hukumomi sun ce an tura jami'an tsaro domin bin sawun ƴanbindigar.