Za a yi jana'izar Ebrahim Raisi ranar Talata - Rahoto

Wannan shafi ne da ke kawo muku abin da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar 20 ga watan Mayun, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Jiragen sama a Iran ba su da cikakkiyar lafiya saboda takunkumai - kamar yadda na gani da idona

      • Marubuci, Jeremy Bowen
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International Editor

    Kafofin yaɗa labarai na Iran ba su fiya maganar ko akwai hannun wani a cikin hatsarin jirgin ba, kawai dai akwai yanayi maras kyawu kuma sai ga hatsari ya auku.

    Sai dai kuma, Shugaba Raisi na da maƙiya da yawa kuma akwai mutane da yawa da za su yi murna da rasuwarsa.

    A shekarun 1980, ya saka hannu kan aiwatar da hukuncin kisa kan dubban masu adawa da gwamnati, waɗanda da yawansu masu neman kawo sauyi ne.

    Ya hau mulki a 2021 kuma tun daga lokacin ya jagoranci murƙushe mutane da yawa a cikin ƙasar. Kuma ma an neme shi ne ya tsaya takara ne, abin da zai iya ba shi damar cigaba da gamawa da masu adawa da shi. Amma kuma ba mu da wata hujja ko ɗaya a kan wannan.

    A Iran, duk abin da ya faru Isra'ila ake fara zarga, amma jami'an Isra'ila sun yi ta musanta hannu a hatsarin. Abu ne mai wuya a iya hasaso abin da Isra'ila za ta amfana da shi a irin wannan aikin da zai zama tsokanar yaƙi ce kawai.

    Game da rashin kyawun yanayi kuma, magana ta gaskiya, saboda tsawon shekaru na takunkumai da aka ƙaƙaba wa ƙasar, jiragen Iran ba su da cikakkiyar lafiya saboda ba su iya samun kayan gyara ko kuma sababbin jirage.

    A shekarun 1990 lokacin da nake ba da rahoto kan wata girgizar ƙasa a Iran, babu nisa daga inda Raisi ya rasu, ina cikin wani jirgin helikwafta na Amurka a lokacin Shah, sai da jirgin ya yi saukar gaggawa saboda ɗaya daga cikin injinansa ya samu matsala saboda rashin kulawa.

    'Yan makonni bayan haka, an faɗa min cewa wannan jirgin ya yi hatsari kuma ya kashe dukkan fasinjojinsa.

  2. An sanar da Mohammad Mokhbar a matsayin shugaban riƙon ƙwarya a Iran

  3. Labarai da dumi-dumi, Za a yi jana'izar Ebrahim Raisi ranar Talata - Tasnim

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ambato Hasan Haghigian, babban jami'in mulki na jihar Gabashin Azerbaijan, yana cewa za a gudanar da jana'izar Ebrahim Raisi da sauran abokan tafiyarsa a gobe Talata.

    Za a yi jana'izar ce a Tabriz, a cewar rahoton.

    Ya ce ana kan aikin kai gawar tasu zuwa Tabriz amma za a kai su cibiyar gwajin lafiya tukunna.

  4. Iran ta naɗa sabon ministan harkokin waje bayan mutuwar Abdollahian

    Ali Bagheri Kanias

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar ministoci ta Iran ta naɗa Mataimakin Ministan Harkokin Waje Ali Bagheri Kanias a matsayin muƙaddashin ministan harkokin waje bayan mutuwar Hossein Amir-Abdollahian.

    Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa an ɗauki matakin ne bayan ganawar da rassa uku na gwamnatin Iran suka yi - zartarwa, da majalisa, da ɓangaren shari'a.

    Ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasa na Ɗaya Mohammad Mokhber ne zai karɓi ragamar mulki a matsayin shugaban ƙasa.

    Kundin mulkin Iran ya ce mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya zai yi mulki ne na tsawon kwana 50 idan shugaban ƙasa ya mutu.

    Mokhber ya faɗa wa gidan talabijin na ƙasar cewa za su ci gaba da bin manufar Shugaba Raisi wajen "gudanar da ayyuka ba tare da wata matsala ba".

  5. Ebrahim Raisi: Alhinin da shugabannin duniya ke yi

    Raisi da Modi

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shugaba Ebrahim Raisi (hagu) kenan yake ganawa da Firaministan Indiya Narendra Modi (R) yayin taron ƙungiyar Brics karo na 15 a birnin Johannesburg ranar 24 ga Agustan 2023

    Shugabannin duniya na ci gaba da bayyana alhininsu game da rasuwar Shugaban Iran Ebrahim Raisi.

    • Firaministan Indiya Narendra Modi ya wallafa a shafinsa na X cewa "ya gigiza da kuma kaɗuwa da mummunan labarin rasuwar" Shugaba Raisi kuma ƙasarsa "tana tare da Iran" yayin wannan "lokaci na alhini"
    • Firaministan Pakistan Shehbaz Sharifhas ya ce mutuwar Raisi "babban rashi ne" kuma ƙasarsa za ta yi alhinin kwana ɗaya
    • Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa Mohammed bin Zayed Al Nahyan ya ce ƙasarsa na tare da Iran a irin wannan lokaci, a cewar rahoton Reuters
    • Shi kuma Shugaban Venezuela Nicolás Maduro ya yabi Shugaba Raisi a matsayin babban aboki kuma shugaba na musamman
  6. Hotunan ɓaraguzan jirgin Raisi da ya yi hastari

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ɓaraguzan jirgin helikwaftan da ya yi hatsari

    Wani hoto da aka cira daga bidiyo ya nuna wurin da ɓaraguzan jirgin helikwaftan da ke ɗauke da Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya faɗi.

    Wani jirgi maras matuƙi ne ya hango ɓaraguzan a yanki mai cike da tsaunika da ke kusa da iyakar ƙasar da Azerbaijan a ranar Litinin.

    Sai dai an samu rahotonnin hatsarin ne tun tsakar ranar Lahadi.

    Shugaban yana kan hanyar komawa gida ne daga aikin ƙaddamar da wata madatsar ruwa tare da Shugaban Azerbaijan Ilham Aliyev a gundumar Jabrayil ranar Lahadin.

  7. Mene ne mataki na gaba bayan mutuwar Ebrahim Raisi?

    Mataimakin Shugaban Iran Mohammad Mokhber

    Asalin hoton, Reuters

    Kundin tsarin mulkin Iran ya fayyace kai-tsaye game da matakin da za a ɗauka da zarar an tabbatar cewa shugaban ƙasa ba zai iya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata ba saboda rashin lafiya, ko mutuwa, ko tsigewa.

    Alhakin zai koma kan mataimakin shugaban ƙasa na ɗaya - a wannan karon ana maganar Mohammad Mokhtar - don ya ci gaba da jagorantar ƙasar tare da haɗin gwiwar shugabannin majalisa.

    Sai kuma ɓangaren shari'a da zai jagoranci zaɓen sabon shugaban ƙasa cikin kwana 50.

    Amma za a yi hakan ne kawai bisa umarnin jagoran addini, wanda shi ne ke da iko sama da kowa a sha'anin mulkin Iran.

    Bayan tabbatar da rasuwarsa da gidan talabijin ɗin ƙasar ya yi, yanzu ƙasar za ta gudanar da zaɓen.

    A zaɓen da ya gabata, an hana masu adawa da Raisi yin takara, abin da ya share masa hanyar zama shugaban ƙasa da ƙuri'u mafiya ƙaranci (kusan kashi 30 cikin 100), kuma hakan ya sa mafiya yawan masu zaɓe suka ƙaurace wa kaɗa ƙuri'ar.

  8. Wane ne Ebrahim Raisi?

    Ebrahim Raisi

    Asalin hoton, Reuters

    Ana kallonsa a matsayin wanda zai iya gadon jagoran addinin ƙasar Ayatollah Khamenei, a matsayinsa na mai tsattsauran ra'ayin siyasa.

    An haife shi a shekarar 1960 a Mashhad inda masallacin 'yan shi'a mafi tsarki yake, kuma ya bi sawun mahaifinsa ne wanda shi ma malamin addinin musulunci ne.

    Ya bi sawun masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Shah wacce aka kifar a shekarar 1979.

    Raisi, mai shekara 63, ya zama mataimakin mai shigar da ƙara a Tehran a lokacin yana da shekara 25.

    Raisi ya bai wa masu hasashe mamaki a lokacin da ya tsaya takarar shugaban ƙasar a zaɓen 2017, inda ya zo na biyu a zaɓen.

    A shekarar 2019, jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Khamenei ya bayyana sunansa a matsayin wanda zai jagoranci ɓangaren shari'ar ƙasar.

    A watan Yunin 2021 ne aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar inda ya maye gurbin Hassan Rouhani.

  9. Assalamu Alaikum

    Ma'abota BBC Hausa barkanmu da hantsin Litinin - tushen aiki.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan shafi na rahotanni kai-tsaye, wanda zai kawo labarai daga sassan duniya.

    Amma za mu fi mayar da hankali kan rasuwar Shugaban Iran Ebrahim Raisi, da kuma Najeriya da maƙwabtanta.

    Ku biyo mu.