Gwamnatin Amurka na matsa wa Isra'ila kan kiyaye rayukan Falasɗinawa
Wasu manyan masu faɗa-a-ji a gwamnatin Shugaba Biden na Amurka na ƙara matsa lamba a kan Isra'ila, yayin da sojojinta ke mayar da hankali kan zafafa hare-haren a kudancin Zirin Gaza.
Mataimakiyar Shugaban Amurkan Kamala Harris ta nuna damuwa kan irin kashe-kashen farar hula na Falasɗinawa da ake yi.
Ta ce yayin da Isra'ila ke da 'yancin kare kanta, ana kuma kashe Falasdinawan da ba su ji ba su gani ba. Da take jawabi ga manema labarai a Dubai ranar Asabar, Ms Harris ta bayyana irin asarar rayukan da ake.
Shi kuwa Sakataren Tsaron Amurka Lloyd Austin, cewa ya yi akwai bukatar Isra'ila ta dinga kare fararen hula, "idan kuma ba haka ba to goyon bayan da take samu zai koma ƙiyayya a faɗin duniya".