Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Isra'ila ta ce ta gano hanyoyin cikin ƙasa 800 a Gaza
Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 47 a Tanzania
Mahukunta a Tanzania sun ce sama da mutane 47 suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewa kasa.
Kwamishina a yankin Hanang da ake arewecin kasar, Janet Mayanja ta ce akalla mutane 85 ne suka jikkata.
Sannan tace akwai gine-gine da gidajen da suka ruguje.
Shugabar Tanzania, Samia Hassan, ta umarci hukumomin tsaro su taimaka a aikin ceto.
Hukumar da ke kula da yanayi ta kasar ta yi hasashen cewa za a cigaba da fuskantar ruwan sama mai karfi a wannan watan a kasar.
Hamas ta nemi Birtaniya ta janye kalamanta na "goyon bayan Isra'ila"
Hamas ta yi Allah-wadai da abin da aka kira "atisayen sojin Birtaniya a waƙin ƙare dangi" kan mutanen Falaɗinawa da ke Zirin Gaza.
Matakin na nuni da yadda Birtaniya ta sanaar da niyyarta ta gudanar da leken sirri domin tattara bayanai kan rikicin da ake yi a Zirin Gaza da ya shafar Falasdinawa."
Hamas ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya ta janye hannunta cikin wannan rikici ta kuma daina bayar da kuɗi ana yaƙar Gaza maimaikon haka kamata ya yi ta rika taimakawa wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.
Dakarun ƙasashen gabashin Afirka sun soma janyewa daga DRC
Dakarun ƙasashen gabashin Afirka sun soma janyewa daga yankin gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo da ke fama da matsalolin tsaro.
An aike dakarun ne a karon farko cikin watan Nuwamban bara bayan gwamnatin Congo ta aike bukatar hakan a kokarin murkushe kungiyar 'yan tawayen M23.
Sai dai gwamnatin ta Kinshasa tana matukar sukar ayyukan dakarun, tare da kin yarda ta sabunta yarjejeniyarsu.
A ranar 20 ga watan Disamba ake shirin gudanar da babban zabe a kasar.
Wasa tsakanin Man City da Tottenham ya ci 'yan kallo
Manchester City da Tottenham sun tashi 3-3 a wasan mako na 14 a Premier League a Etihad ranar Lahadi.
Tottenham ce ta fara cin kwallo ta hannun kyaftin, Heung-min Son a minti na shida da fara wasa, minti uku tsakani City ta farke, bayan da Son ya ci gida.
Daga nan ne Phil Foden ya kara na biyu, haka suka je hutu City na cin 2-1.
Da suka koma zagaye na biyu Giovani Lo Celso ya farkewa Tottenham, sai dai Jack Grealish ya zura na uku a ragar Tottenham.
Daf da za a tashi wasan kungiyar Ange Posteglou ta farke ta hannun Dejan Kulusevski.
Da wannan sakamakon City ta koma mataki na uku a teburin Premier League da maki 30, Liverpool ce ta biyu mai maki 31, wadda ta doke Fulham 4-3 a Anfield ranar Lahadi.
Tottenham kuwa wadda aka doke wasa uku a jere kafin zuwanta Etihad ta yi kasa zuwa mataki na biyar da maki 27.
Arsenal ce ta daya a kan teburin Premier League da maki 33, bayan wasannin mako na 14.
Arsenal da Liverpool za su fafata a FA Cup zagaye na uku
Arsenal, wadda take jan ragamar teburin Premier League za ta fafata da Liverpool a zagaye na uku a FA Cup na bana.
Sunderland za ta karbi bakuncin Newcastle a wasan hamayya, yayin da mai rike da kofin Manchester City za ta kece raini da Huddersfield Town.
Ita kuwa Manchester United za ta kai ziyara ga Wigan Athletic, Tottenham za ta karbi bakuncin Burnley da wanda Everton za ta je gidan Crystal Palace.
Za a fara wasannin zagaye na uku daga 5 zuwa 8 ga watan Janairun 2024.
Amurka ta ce an kai wa jirgin yakinta na ruwa da wasu na kasuwanci hari a Red Sea
Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce an kai wa wani jirgin yaƙinta da wasu jiragen kasuwanci hari a ruwan maliya.
Ma'aikatar ta ce tana bincike kan lamarin kuma da sannu za ta saki ƙarin bayani a kusa kan hare-haren.
Sa'o'i da suka gaba ne sojojin Birtaniya suka sanar da cewa an kai harin jirgi maras matuƙi sannan kuma an ji fashewar wasu abubuwan a tekun.
Ma'aikatar ba ta bayyana takamaiman inda hare-haren suka faru ba.
Amma a waɗannan makonnin da ake ta fama da yaƙin Isra'ila da Gaza, 'yan tawayen Houthi na Yeman da ke samun goyon bayan Iran an ta rawaito suna kai hare-hare kan jirage a ruwan na maliya, wasu rahotannin kuma sun ce sukan kai hari da makami mai linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila.
Mun kai hare-hare kimanin dubu 10 daga fara yaƙin nan - Isra'ila
Cikin wata da sojojin Isra'ila suka fitar, ta bayyana sun kai a kimanin dubu goma tun daga farkon fara yaƙin.
Sanarwar ta ƙara da cewa hare-haren sun haɗa da na ƙasa da na sama da ake kai wa.
Ma'akatar lafiya ta Gaza ta ce ya zuwa yanzu mutanen da aka kashe sun zarce dubu goma sha biyar.
Me jirgin leen asirin Birtaniya ke nema a Gaza?
Ma'aikaatar tsaron Birtaniya ta aike wani jirgin leen asiri domin samo mata bayanai kan inda Hamas ke tsare da fursunonin da suka yi garkuwa da su.
Sakatariyar Lafiya Victoria Atkins ta shaida wa BBC a ranar Lahadi cewa "jiragen ba ma su makamai ba ne" kuma BBC ta tabbatar da haka daga Ma'aikatar tsaro.
Ta ce : "Suna neman waɗanda aka yi garkuwa da su ne, duk da cewa an saki wasunsu amma har yanzu akwai waɗanda ke hannu da ake buƙatar su kubuta suma."
Akwai 'yan Birtaniya biyar da suka ɓata tun bayan fara rikicin Hamas da Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
Mutum 15,500 aka kashe a Gaza daga fara yaƙin Isra'ila da Hamas
Ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce an kashe mutum 15,500 a Gaza daga lokacin da aka fara yakin tsakanin Isra'ila da Hamas.
Dr Ashraf al-Qadara ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai, inda ya ce akwai Falasdinawa 41,316 da aka jikkata ya zuwa yanzu.
Tsohon Firaiministan Rwanda ya mutu a gudun hijira
Tsohon Firaiministan Rwanda kuma fitaccen mai sukar gwamnatin shugaba Paul Kagame ya rasu a lokacin da yake gudun hijira a Belgium
Yan uwan Faustin Twagiramungu ne suka tabbatar da rasuwarsa a ranar Asabar, inda suka ce ya mutu yana da shekara 78 bayan fama da rashin lafiya.
Mista Twangiramungu ɗan hutu ne mai tsaka-tsakin ra'ayi, kuma shi ne ya riƙe firaiminista lokacin da aka kafa gwamnatin haɗin gwiwa bayan kammala kisan kiyashin Rwanda a 1994.
Ya ce bai amince da mamaye gwamnati da 'yan ƙabilar Tutsi suka yi ba lokacin da yake magana kan kisan da aka yi wa 'yan Hutu.
Ya ajiye mukaminsa ne a 1995 lokacin da ya yi gudun hijira zuwa Belgium.
A 2003 ya koma Rwanda na ɗan lokaci inda da ya yi takarar shugaban ƙasar na yanzu Mista Kagame ya kada shi.
Isra'ila ta ce ta gano hanyoyin cikin ƙasa 800 a Gaza
Gwamnatin Isra'ila ta ce sojojinta sun gano hanyoyin cikin ƙarƙashin ƙasa 800 a Gaza,
"Tun farkon fara wannan yaƙi, sojojin Isra'ila sun gano hanyoyin ƙasa 800 sun kuma lalata 500 daga ciki," kamar yadda kakakin gwamnatin Isra'ila Elon Levy ya bayyana a wani taron manema labarai da Isra'ila ta yi domin bayyana halin da sojojinta ke ciki a Gaza.
Ya ci gaba da cewa sojoji da dama sun jikkata "sun ji munanan raunuka" sakamakon wata fashewar tankar mai da aka samu a arewacin Isra'ila kan motar sojojinsu.
'Gwanda na ƙara lafiyar ido'
Likitoci sun yi bayanin cewa gwanda na ƙunshe da sinadaran da ke ƙara wa ɗan'adam lafiyar jiki, musamman ma ido.
Bugu da ƙari, likitar ido Aisha Shariff Kalambe ta ce gwanda na da sinadarin vitamin C mai yawa.
"Idan mutum ya ci yankan gwanda sau ɗaya a rana ya ishe shi ya samu vitamin C da yake buƙata," in ji ta.
Haka nan, tana taimakawa wajen rage hawan jini, da ciwon zuciya, da kare kumburin cikin jiki, da kuma rage kaifin cutukan da tsufa ke jawowa.
Ƙasashen Nijar, Mali, Burkina Faso na son zama ƙasa ɗaya
Gwamnatocin soji a ƙasashen Nijar, da Burkina Faso, da Mali sun bayar da shawarar kafa ƙasa ta tarayya da za ta haɗa ƙasashen uku na Afirka ta Yamma kuma maƙwabtan juna.
Sun bayyana shawarar ce bayan ganawar da ministocin harkokin wajensu suka yi a birnin Bamako na Mali a ƙarshen makon nan.
Lamarin na zuwa ne yayin da Nijar da Burkina Faso ke son bin sawun Mali na ficewa daga ƙungiyar ƙasashen G5, wadda aka kafa don yaƙar masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.
Wata sanarwar bayan taron ministocin ta ce ƙasashen sun bayyana "babban yunƙurinsu na zaman lafiya, da cigaba, da kuma difilomasiyya" da kafa ƙasar zai samar.
"Ministocin...da ke da burin haɗe Burkina Faso, da Mali, da Nijar sun bai wa shugabannin ƙasashen shawarar kafa ƙasa ta tarayya mai suna Alliance of Sahel States," a cewar sanarwar. Alliance of Sahel States na nufin Ƙasashen Ƙawance na Sahel.
Ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma Ecowas ta dakatar da ƙasashen uku daga cikinta bayan sojoji sun hamɓarar da gwamnatocin farar hula a ƙasashensu.
MDD ta ce mutum ɗaya cikin huɗu na gudun hijira a Zirin Gaza
Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi ƙiyasin cewa duk mutum ɗaya cikin biyar a Zirin Gaza an raba shi da gidansa sakamakon yaƙin da Isra'ila ke cewa tana yi da Hamas.
Ofishin tattara kayan agaji ya ce kusan mutum miliyan 1.8 ne ke gudun hijira a cikin Gaza daga cikin miliyan 2.2 da ke zaune a zirin.
Sai dai kuma MDD ta ce "samun cikakkun alƙaluma abu ne mai wuya" saboda akwai wuya wajen bin sawun waɗanda suka gudu da kuma waɗanda suka koma gida bayan ƙulla yarjejeniyar tsgaita wuta da ta ƙare ranar Juma'a.
Tun a farkon yaƙi Isra'ila ta umarci mazauna Gaza su koma kudancin, kuma dubun dubata ne suka yi hakan. Tun bayan ƙarrwaer tsagaita wutar, Isra'ila ta sake umartar mazauna kudancin a Khan Younis su ƙara matsawa.
Isra'ila ta ce an raunata sojojinta sakamakon makaman da aka harba daga Lebanon
Rundunar sojin Isra'ila ta ce an jikkata sojojin da dama sakamakon harin makami mai linzami da aka harba daga Lebanon.
Ta ce harin ya lalata aya daga cikin motocinta da ke yankin Beit Hillel a arewacin Isra'ila, 'yan kilomitoci daga iyakarta da Lebanon.
sai dai ba ta fai adadin sojojin da aka raunata ba da kuma wanda ya kai musu harin.
Rundunar ta ce tana kai wa yankin da makaman suka fito hare-hare da makaman atilare.
Ministocin harkokin waje na Larabawa za su taru a Ƙatar kan yaƙin Isra'ila a Gaza
Ministocin harkokin waje na ƙasashen Larabawa za su gana a birnin Doha na Ƙatar ranar Talata, inda ake sa ran za su yi muhawara kan yaƙin Isra'ila a Zirin Gaza.
Haɗuwar na zuwa ne mako uku bayan shugabannin ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun tattauna a Saudiyya kuma suka nemi tsagaita wuta nan take a Gaza.
Mazauna ƙasashen nasu na goyon bayan Falasɗinawa sosai a wannan rikici kuma shugabannin na shan matsi daga 'yan ƙasar tasu don su ɗauki tsattsauran mataki kan Isra'ila.
Kusan dukkan ƙasahen Larabawa da suka gyara alaƙa da Isra'ila sun janye jakadunsu daga ƙasar bayan luguden wutar da ta fara a kan Gaza ranar 7 ga watan Oktoba - bayan harin Hamas da ya kashe mutum 1,200 da kuma yin garkuwa da wasu fiye da 200.
Zuwa yanzu Isra'ila ta kashe sama da mutum 15,200 a hare-haren da take kaiwa a Gaza tun daga ranar, 6,000 daga cikinsu yara ne ƙanana, kamar yadda ma'aikatar lafiya a Gaza ta bayyana.
Fashewa ta kashe mutum huɗu a wurin ibadar Kiristoci a Philippines
Mutum huɗu sun mutu sakamakon wata fashewa a taron ibadar Kiristocin Katolika a kudancin ƙasar Philippines da safiyar yau Lahadi.
Lamarin ya faru ne a Jami'ar Jihar Mindanao da ke Marawi, garin Musulmai mafi girma a ƙasar.
Wasu 42 sun ji ƙananan raunika, a cewar hukumomi, suna masu cewa "an shawo kan lamarin".
A 2017, an fafata yaƙi tsawon wata biyar a Marawi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan bindigar da ke da alaƙa da ƙungiyar Islamic State.
A cewar Kwamandan 'Yan Sanda Birgediya Janar Allan Nobleza, babu mamaki ƙungiyar Daulah Islamiyah-Maute ce ta kai harin.
Ya ce sojojin ƙasar sun kashe mambobin ƙungiyar 11 ranar Juma'a da wuce a garin Datu Hoffer Ampatuan mai maƙwabtaka, inda yake nuna cewa harin na ranar Lahadi kamar ramuwar gayya ce.
Mahari ya kashe mutum ɗaya da wuƙa a Paris
Mutum ɗaya ya rasa ransa wasu biyu kuma sun ji raunika a wani harin wuƙa da guduma da aka kai a tsakiyar birnin Paris na Faransa.
Lamarin ya faru ne a kusa da Effiel Tower, inda rahotonni suka ce wanda aka kashe ɗan Jamus ne mai yawon buɗe-ido.
Rahotanni sun ce maharin ya dinga kabbara lokacin da yake kai harin.
Ministan harkokin cikin gida na Faransa cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X , ya ce 'yan sanda sun kama mutumin.
Wata majiya daga rundunar 'yan sandan birnin ta ce mutumin da ake zargi ɗan asalin ƙasar ne sannan kuma an san shi da tsantsar kishin Musulunci da kuma taɓin hankali.
Birtaniya za ta tura jiragen neman Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su
Birtaniya ta ce za ta aika jiragen leƙen asirinta sararin samaniyar Gaza da Isra'ila don taimakawa wajen gano inda Hamas ke riƙe da Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su.
Wata sanarwa daga ma'aikatar tsaron ƙasar ta ce jiragen ba masu ɗauke da makamai ba ne kuma za su mayar da hankali ne kawai kan tattara bayanai.
"Bayanan aikin ceto mutanen kawai za a miƙa wa hukumomin da suka dace, waɗanda ke da alhakin ceton," in ji ta.
'Yan Birtaniya biyar ne suka ɓace bayan harin Hamas a Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba, bayan an kashe wasu 'yan Birtaniyar 12 a harin, a cewar gwamnatin ƙasar.