Ma'aikatar lafiya a Gaza ta ce an kashe ƙarin Falasɗinawa 193 daga Juma'a

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ruwan wutar Isra'ila ya shiga rana ta biyu a Gaza bayan ƙarewar tsagaita wuta

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Isra'ila ta shiga rana ta biyu wajen kai sabbin hare-haren a Zirin Gaza, inda rahotanni ke cewa ana ganin baƙin hayaki a sararin samaniyar yankin.

    Mai magana da yawun rundunar sojin Isra'ila ya ce a yanzu suna kai wa Hamas hari ta ko'ina a zirin Gaza.

    Wasu rahotanni da suka fito a daren jiya Juma'a daga Khan Yunis a kudancin Gaza na cewa munanan hare-hare sun tsananta a yankin.

    Hukumomin lafiya na Falasdinawa sun ce an kashe mutum fiye da 180 a hare-hare ta saman da aka kai a jiya Juma'a.

    Majalisar Dinkin Duniya ta sake gargaɗi a kan taba fararen hula.

  2. Maraba

    Barkanmu da hantsin Asabar, barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotonni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Za mu fi mayar da hankali kan yaƙin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza.

    Kuna tare da Umar Mikail a wannan hantsi.