Motocin agaji sun hau layin shiga Gaza kafin tsagaita yaƙi a safiyar Alhamis

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najieriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Abdullahi Bello Diginza, Umaymah Sani Abdulmumin and Umar Mikail

  1. Takardun hukuncin shari'ar Kano sun tada jijiyoyin wuya

  2. Bayanai kan yarjejeniyar Isra'ila da Hamas

    • Ana sa ran za a sanar da tsagaita wuta tsawon kwana hudu nan da sa'a 24
    • A wannan lokaci, Hamas za ta saki mutum 50 da take garkuwa da su daga Gaza
    • Sannan Isra'ila za ta saki mata da matasa Falasɗinawa 150 da Isra'ila ke tsare da su
    • Isra'ila ta fitar da jerin sunayen Falasdinawa 300 da za a iya sakinsu gaba daya - galibinsu matasa ne maza
  3. Kotu ta bada belin Godwin Emefiele a kan naira miliyan 300

    GodwinE

    Babbar kotun Tarayya da ke Abuja a Najeriya ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin ƙasar Godwin Emefiele, kan kuɗi naira miliyan 300 da kuma mutum biyu da za su tsaya masa.

    Mai shari’a Hamza Mu’azu ne ya bayar da belin, tare da sharaɗin karɓe takardun tafiyar tsohon gwamnan.

    Godwin Emefeile wanda bai halarci zaman kotun da aka yi na bayar da belin nasa ba, an yi masa sharaɗin sai ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa, da suke da takardun mallakar gida ko filaye a unguwar Maitama da ke Abuja.

    Cikin sharuɗan kotun da ta gindaya na ba da belin ta ce sai Emefeile ya bayar da takardun tafiye-tafiyensa ga rijistaran kotun sannan duk zirga-zirgar da zai yi ba zai fita daga kwaryar birnin Abuja ba.

    Har yanzu dai yana tsare a gidan yarin Kuje da ke Abuja, zuwa lokacin da zai cika sharudan da aka zayyana.

    Wannan hukunci na zuwa ne watanni huɗu bayan babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da belin Emefiele kan kuɗi naira miliyan 20.

    Yanzu kuma babbar kotun tarayyar da ke zamanta a Abuja ta sake bayar da belin nasa kan kuɗin da suka kai naira miliyan 300.

    Tun da fari an tuhumi Emefeile da laifuka 20 waɗanda suka jiɓanci almundahana ta takai naira biliyan 6 da miliyan 500, amma daga baya aka rage su zuwa guda shida da suka jiɓanci almundahana ta takai naira biliyan 1 da miliyn 600.

    A sabbin tuhume-tuhume shidan da aka gabatar, Emefeile kawai ake ƙara ba tare da wani abokin aikinsa ba.

  4. An zargi sojojin Sudan ta Kudu da kai hari kan fararen hula a Abyei

    ...

    Asalin hoton, AFP

    An zargi Dakarun tsaron Sudan ta Kudu (SSPDF) da kai harin kwantan ɓauna a kan fararen hula a safiyar ranar Lahadi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 40 a yankin Abyei da ake takaddama a kai.

    Sultan Bulabek, shugaban masarautu tara a Abyei, ya shaida wa BBC cewa sojojin sun kai hare-haren haɗin-gwiwa a kauyuka da dama tare da matasa masu dauke da makamai daga lardin Twic na jihar Warrap.

    Ya yi iƙirarin cewa harin na nufin korar al'ummar Ngok daga gidajensu.

    Wani mazaunin garin ya shaidawa BBC a ɓoye cewa an kashe ɗan uwansa a harin, kuma sun gagara fitar da gawarsa daga wurin.

    Manjo Janar Akuei Ajou, kwamandan runduna ta uku ta SSPDF, ya musanta zargin yana mai cewa manufar kafa rundunar ita ce kare al'umomin Twic da Abyei.

    Sannan ya kara da cewa matasan Abyei ne suka kai hari a sansanin soji da ya kashe sojoji bakwai da fararen hula ciki har da yara, a ranar 13 ga watan Nuwamba.

    Wata sanarwar haɗin-gwiwa da ofisoshin jakadancin ƙasashen Norway da Birtaniya da Amurka suka fitar, ta buƙaci Sudan ta Kudu da ta janye sojojinta daga Abyei domin hana ci gaba da tashe-tashen hankula.

    Abyei dai ya kasance batun takaddamar da aka daɗe ana fama tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu.

  5. Ƴan bindiga sun kashe mutum tara a kasuwar Kamaru

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu da ake zargin mayaƙan 'yan a-ware ne daga yankin renon Ingilla na Kamaru sun kashe kimanin mutum tara a wani samame da suka kai a wani ƙauye da ke yankin yammacin kasar.

    Harin ya afku ne a wata kasuwa da ke sashen gudanarwa na Galim, mai tazarar kilomita 15 daga yankin Arewa maso Yamma mai fama da rikici inda 'yan a-waren yankin renon Ingila ke fafatawa da sojojin jihar.

    Moïse Mbazoa, wani ma'aikacin yankin da ke tabbatar da jikkata da asarar rayuka ya ce maharan sun yi garkuwa da mutane tare da sace babura.

    Duk da rashin samar da hanyoyin daƙile harin, an aike da dakarun soji daga garuruwan da ke makwabtaka da yankin.

    Har yanzu dai ba a fayyace dalilin kai harin ba, amma hukumomi na cewa wannan ba shi ne karon farko da ake zargin 'yan a-ware da kai hari Galim ba.

    Ko a kwanakin baya sai da a kai hari kan cibiyoyin gwamnati da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

    Wannan lamari na zuwa ne makonni bayan da wasu da ake zargin 'yan a-ware ne suka kashe aƙalla mutum 20 a garin Mamfe da ke yankin Kudu maso Yammacin yankin reinon Ingila.

    Yankin yammacin Kamaru, wanda galibin masu amfani da harshen Faransanci ne, yana da iyaka da yankin Arewa maso Yamma mai fama da rikici.

    Garuruwa da ƙauyuka daban-daban a yankin Yamma sun fuskanci hare-hare daga 'yan tawaye da ake kyautata zaton mayaƙan 'yan a-ware ne da suka samo asali daga yankin reinon Ingila mai makwabtaka.

  6. 'Yan bindiga sun yi garkuwa da mata takwas a Abuja

    Rahotanni daga birnin Tarayyar Najeriya, Abuja na cewa an yi garkuwa da wasu mata takwas a yankin Kuje.

    Wannan labari na zuwa ne kasa da sa'o'i 48 da sace mataimakin shugaban karamar hukumar Kwali da wasu mutane shida a kauyen Yewuti da ke Kwalin.

    Matan da manoma ne an sace su ne a wata gona da ke kauyen Gwombe da ke masarautar Gwargwada a karamar hukumar Kuje.

    Wani mazaunin Gwargwada, Usman Yakubu ya shidawa jaridar Daily Trust ta Najeriya cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin.

    Ya kuma kara da cewa wasu 'yan bindiga ɗauke da bindigogi kirar AK-47 ne suka yi awon gaba da matan, wadanda dukkaninsu matan aure ne da ke aikin girbi a gonakinsu.

    Wani basaraken kauyen da ya zaɓi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace mutanen, sannan ya zargi cewa maharan 'yan bindiga ne daga Kebbi da 'yan banga Miyetti Allah suka tarwatsa a karshen mako.

    Babu wani martani daga kakakin rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, kan lamarin kawo yanzu.

  7. Fadar shugaban kasa ta yi watsi da sukar Obasanjo kan dimokuraɗiyya

  8. An kai hari hedikwatar 'yan sanda ta Adamawa

    ...

    Asalin hoton, AFP

    An kai hari hedikwatar 'yan sanda da ke Adamawa a sanyin safiyar Laraba, lamarin da ya ɗaga hankula da jefa al'umma cikin yanayi na kaɗuwa a birnin Yola.

    An shafe kusan rabin sa'a ana harbe-harbe, a cewar mazauna kusa da hedikwatar.

    Wasu majiyoyi na cewa sojoji ne suka kai harin na ramuwa, bayan sun zargi wani ɗan sanda da kashe wani jami'insu.

    Wata sanarwa da kwamishinan 'yan sanda CP Afolabi Babatola, ya fitar ta tabbatar da harin tare da Allah-wadai da rikicin da ya ɓarke tsakanin jami’an ‘yan sanda da sojoji.

    A cewar sanarwar rikici ne ya rikiɗe zuwa musayar harbe-harben bindiga wanda ya kai ga wani mummunan hari kan ofishin ‘yan sanda da ya yi sanadin mutuwar wani Sufeto, Jacob Daniel.

    CP Babatola ya bayar da umarnin a gudanar da bincike cikin gaggawa domin tabbatar da adalci da kuma dawo da zaman lafiya.

    Ya kuma jaddada cewa ba za a sake lamuntar duk wani hari da ake kai wa jami'an tsaro a bakin aiki.

    Babatola ya jaddada muhimmanci rayuwar dukkanin jami'an tsaro tare da shan alwashin cewa za a magance irin waɗannan rikice-rikicen bisa dokokin da ake dasu.

    Kwamishinan ya kuma bayyana kudirin rundunar na kare rayuka da dukiyoyin jama'a tare da yin kira da a haɗa kai a tsakanin rundunonin tsaro domin kare haƙƙinsu.

    CP Babatola ya kuma buƙaci jama'a su kwantar da hankulansu, inda ya tabbatar cewa manyan jami’an tsaron biyu na aiki tukuru bisa tsarin doka don shawo kan duk wata matsala ta tsaro.

  9. Tattaunawar Habasha da ƙungiyar 'yan tawayen OLA ba ta yi nasara ba

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Habasha ta ce tattaunawar sulhu na baya-bayan nan da aka yi da ƙungiyar 'yan tawayen Oromo Liberation Army (OLA) ta gaza kawo ƙarshen yarjejeniya.

    Ɗaya daga cikin masu shiga tsakani na gwamnati, Redwan Hussein, ya zargi ƙungiyar ta OLA, da "kawo cikas ga tattaunawar da kuma yin "bukatun da ba su dace ba".

    Gwamnatin ƙasar ta yi nadamar faruwar lamarin," in ji Redwan a kan shafin sada zumunta na X (tsohon Twitter).

    A martanin da ta mayar, OLA ta ce gwamnatin Habasha tana da sha'awar yin hadin gwiwa ne kawai "maimakon fara magance matsalolin da ke tattare da ƙalubalen tsaro da na siyasa da ake ganin ba za a iya shawo kan gundumar ba".

    Kungiyar OLA - da gwamnatin Habasha ta ayyana a matsayin ƙungiyar ta’addanci - ta shafe shekara hudu tana yaƙar gwamnati, saboda abin da ta kira 'zaluncin kabilar Oromo'.

    Tattaunawar da aka yi tsakanin gwamnati da ƙungiyar OLA - da aka yi a birnin Dar es Salaam na Tanzaniya - na fatan samar da zaman lafiya a yankin Oromia mafi girma a kasar Habasha.

    A yankin na Amhara dake makwabtaka da ƙasar, ana ta samun tashe-tashen hankula tsakanin sojoji da ‘yan bindiga da gwamnatin ƙasar ke ƙoƙarin wargazawa.

    • Ethiopia: Yadda Habasha ta ɗaure ƙananan yara a gidan yari
    • Abin da ya sa yaƙin Ethiopia ya sake zama sabo a Tigray da Amhara
  10. Isra'ila na kai hare-hare a Gaza kafin soma aikin yarjejeniyar tsagaita wuta

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Dakarun tsaron Isra'ila sun bayyana cewa suna ci gaba da kai hare-hare ta sama da kasa da kuma teku a Zirin Gaza kafin yarjejeniyar tsagaita bude wuta na kwanaki hudu ya fara aiki.

    Sun ce za a sanar da lokacin farawa na tsagaita wutar a cikin sa'o'i 24 masu zuwa.

    Dakarun tsaron Isra'ila sun sanar da hakan ne a shafin sada zumunta na X kuma sun bayar da cikakkun bayanai game da hare-haren jiragen sama da musayar wuta da 'yan bindigar Hamas da kuma lalata kayayyakin more rayuwa da ake zargin na Hamas ne.

    Da alama Khan Younis da ke kudancin Zirin Gaza yana cikin wuraren da aka kai harin.

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    • Tsagaita wuta zai ba Hamas damar sake shiri don kai hare-hare - Anthony Blinken
    • Luguden wutar Isra'ila ya kashe mutum fiye da 900 a Gaza
  11. Koriya ta Kudu ta dakatar da yarjejeniyar soji tsakaninta da ta Koriya ta Arewa

    ...

    Koriya ta Kudu ta ɗan dakatar da yarjejeniyar soji tsakaninta da Koriya ta arewa, bayan Pyongyang ta sanar da yin nasarar harba tauraron leken asiri na farko zuwa sama.

    Yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2018, an yi ta ne da nufin rage tashin hankali tsakanin ƙasashen makoftan juna.

    Terrence Roehrig, farfesa a kwalejin sojin ruwa a Amurka ya ce tauraron ɗan adam din zai bai wa Koriya ta Arewa damar ganin abin da ke faruwa a Koriya ta Kudu.

    Akwai hatsari sosai ganin Arewar na cewa za ta harba ƙarin tauraron ɗan adam din.

    Firaiministan Koriya ta Kudu Han Duck-soo, ya ce sojoji za su koma aikin sa ido kan lamuran da ke gudana a iyakar kasashen, wanda a baya aka janye.

    • Kumbon leƙen asirin Koriya ta arewa ya faɗa cikin teku
    • Me ya sa alaƙar Rasha da Kim Jong Un ke neman rikita duniya?
  12. Amurka ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wuta

    Shugaba Joe Biden na Amurka ya yi maraba da nasarar da aka samu a tattaunar da za ta bayar da damar saƙo waɗandan Hamas ta yi garkuwa da su lokacin da ta ƙaddamar da hari a Isra'ila ranar 7 ga watan Okotoba.

    Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya ce ana sa ran aƙalla Amurkawa uku cikin wadanda mayaƙan Hamas suka yi garkuwa da su a Gaza, har da wani yaro mai shekara uku na daga cikin waɗanda za a sako nan ba da kwanaki masu zuwa.

    Sai dai wakilin BBC ya ce Isra'ila ta ce duk da wannan yarjejeniya, yaki tsakaninta da Hamas yanzu aka fara har sai ga bayan ta da tabbatar da babu wata barazana da za a fuskanta daga Gaza a nan gaba.

    • Biden na fuskantar ƙarin bijirewa a cikin gida kan yaƙin Isra'ila a Gaza
    • Asibitocin da yakin Isra'ila da Hamas ya ritsa da su a Gaza
  13. Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin-gadi

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila da Hamas sun tabbatar da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi, inda Hamas za ta sako 'yan Isra'ila 50 da take garkuwa da su, dukkansu mata da kananan yara.

    Cikin wata sanarwar da Hamas ta fitar, ta yi ƙarin bayani kan cewa Isra'ila za ta saki Falasɗinawa matasa da mata 150 da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila.

    Wakiliyar BBC ta ce jami'an Isra'ila sun ce an cimma yarjejeniyar dakatar da wuta ta kwanaki huɗu.

    A tsakanin kwanakin ne za a miƙa Isra'ilawa 50, idan komai ya tafi daidai za a tsawaita dakatar da buɗe wutar da ƙarin kwanaki uku.

    Qatar - wadda ta shiga tsakani - ta ce nan da sa'o'i 24 za a sanar da lokacin fara aikin yarjejeniyar.

    • Rikicin Isra'ila da Gaza: Mene ne asalin sa?
    • Yaya mamayen ƙasa na sojojin Isra'ila zai kasance a Gaza?
  14. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba da Hausawa ke yi wa kirari da 'Ta Bawa ranar samu'.

    Abdullahi Bello Diginza da Aisha Babangida ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafa wa a shafukanmu na sada zumunta