WHO ta kira al-Shifa da 'sansanin mutuwa'

Asalin hoton, Reuters
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya bayyana asibiti mafi girma a Gaza na Al-Shifa da cewa ya zama "sansanin mutuwa", bayan ficewar ɗaruruwan mutane daga cikinsa
Tawagar haɗin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya ƙarƙashin jagrancin WHO ta samu ziyartar asibitin na tsawon sa'a guda bayan sojojin Isra'ila sun mamaye shi tare da tilasta kwashe marasa lafiya.
Tawagar ta ce ta ga hujjojin da ke nuna kai hare-haren makami da harbe-harben bindiga, tare da gano wani babban kabari a ƙofar shiga asibitin, wanda aka shaida musu cewa gawarwaki 80 aka binne a ciki.
A kwanakin baya-bayan nan ne sojojin Isra'ila suka kai samame asibitin, a wani ɓangare na abin da suka kira ''kai hari kan mayaƙan Hamas".
Sai dai ba ta bayyana wata ƙwaƙƙwarar hujjar da za ta tabbatar da iƙirarin nata na cewa mayaƙan ƙungiyar na gudanar da ayyukansu a hanyoyin ƙarƙashin ƙasa da ke ƙarƙashin asibitin.


