INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa zuwa Litinin

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Har yanzu Inec ba ta zauna ba a jihar Kogi

    A jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, har yanzu hukumar zaɓe ba ta fara zaman tattara sakamakon zaɓen gwamna da aka yi ranar Asabar ba.

    Tun da farko an ce 10:00 za a fara zaman, amma har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton 'yan jarida da wakilan jam'iyyu ne kawai ke zaune a ɗakin taron da ke birnin Lokoja.

    Kogi
    Kogi
    Kogi
  2. Labarai da dumi-dumi, Uzodimma ya lashe zaɓen gwamnan Imo

    Gwamnan Imo kuma ɗan takarar jam’iyyar APC, Hope Uzodimma, ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.

    Gwamnan wanda ya samu wa’adi na biyu a kan karagar mulki ya cinye dukkan ƙananan hukumomi 27 na jihar.

    Babban Baturen Zaɓe Farfesa Abayomi Fashina na Jami'ar Tarayya ta Oye Ekiti ne ya bayyana Mista Uzodimma a matsayin wanda ya yi nasara, inda ya ce ɗan takarar na APC ya samu ƙuri’a 540,308.

    Ɗan takarar jam’iyyar PDP, Samuel Anyanwu, ya samu ƙuri'u 71,503. Sai kuma Achonu Nneji na jam'iyyar Labour Party da ya samu 64,081.

    Tun da misalin ƙarfe 2:00 na dare ranar Asabar aka fara tattara sakamakon zaɓen, wanda ake ganin ya tafi lafiya ƙalau a mafi yawan rumfunan zaɓe duk da faragabar tashin hankali da aka dinga yi sakamakkon ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

  3. Ana shirin bayyana wanda ya yi nasara a zaɓen gwamnan Imo

    Imo

    Gwamnan Imo kuma ɗan takarar jam’iyyar APC, Hope Uzodimma, ya lashe dukkan ƙananan hukumomin jihar 27 a zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar Asabar.

    Babban Baturen Zaɓe Farfesa Abayomi Fashina na Tarayya ta Oye Ekiti ne ke jagoran tattara sakamakon kuma a kowane lokaci nan gaba kaɗan zai iya bayyana wanda ya yi nasara a zaɓen.

    Zuwa yanzu APC na da ƙuri'a 540,308, sai kuma PDP mai ƙuri'u 71,503, da kuma Labour Party mai ƙuri'u 64,081.

    Tun da misalin ƙarfe 2:00 na dare ranar Asabar aka fara tattara sakamakon zaɓen, wanda ake ganin ya tafi lafiya ƙalau a mafi yawan rumfunan zaɓe duk da faragabar tashin hankali da aka dinga yi sakamakkon ayyukan ‘yan bindiga a jihar.

  4. Inec za ta fara zaman tattara sakamako a jihar Kogi

    Kogi

    Hukumar zaɓe ta Inec a jihar Kogi za ta fara zaman tattara sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar ranar Asabar.

    A cewar hukumomi, za a fara tattara sakamakon daga ƙananan hukumomi da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar yau Lahadi.

    'Yan takara 18 ne suka fafata a zaɓen na jiya Asabar.

    Kogi na da ƙananan hukumomi 21 kuma ana sa ran bayyana wanda ya lashe zaɓen nan da tsakar dare ko kuma safiyar Talata.

  5. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar BBC Hausa barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye.

    Umar Mikail ne ke fatan kun tashi lafiya tare da fatan za ku biyo mu don sanin waɗanda suka yi nasara a zaɓukan gwamna a jihohin Kogi, da Imo, da Bayelsa.

    Ku biyo mu.