Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa zuwa Litinin

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Kogi: Ƙaramar hukumar Mopamoro

    Masu zaɓe: 26827

    Masu zaɓen da aka tantance: 9193

    APC - 5077

    ADC - 2027

    PDP - 1562

    SDP - 253

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 9185

    Halastattun ƙuri'u: 9049

    Ƙuri'un da aka soke: 136

  2. Labarai da dumi-dumi, Ina kiran Inec ta soke zaɓen Kogi - Dino Melaye

    Ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya yi watsi da sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe ta Inec ta tattara zuwa yanzu.

    Cikin wani bidiyo da wallafa a shafinsa na dandalin X, wanda aka sani da Twitter a baya, Mista Melaye ya nemi Inec ta soke zaɓen gaba ɗayansa.

    "A wurare da yawa da na yi nasara, an faɗa wa wakilaina cewa babu takardun da za a shigar da sakamakon zaɓen, kuma muna da hujjojin da za mu tabbatar da wannan iƙirari," in ji shi.

    "Inec ba abar amincewa ba ce, sun nuna son-kai, sun goyi bayan wani ɓangare."

    Sai dai BBC ba ta tabbatar da wannan iƙirari nasa ba.

  3. Labarai da dumi-dumi, An sake yin garkuwa da jami'anmu a Bayelsa - Inec

    Hukumar zaɓen Najeriya Inec ta ce an yi garkuwa da wasu jami'anta a ƙaramar hukumar Brass ta jihar Bayelsa da ke kudancin ƙasar.

    Kwarmaton da Inec ɗin ta yi a dandalin X na zuwa ne kwana ɗaya bayan sakin baturiyar zaɓe Ms Ebehireme Blessing Ekwe, wadda aka yi garkuwa da ita a jihar ta Bayelsa kafin fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamna na ranar Asabar.

    "Wannan lamari zai iya kawo cikas ga sahihin zaɓe," in ji Inec.

    Ta ƙara da cewa "muna kira ga jami'an tsaro da su gaggauta kuɓutar da su".

  4. Bayelsa: APC na zargin Inec da sauya wurin tattara sakamako

    Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Bayelsa ta yi watsi da yunƙurin hukumar zaɓe ta Inec na mayar da zaman tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Nembe da Kudancin Ijaw zuwa Yenagoa babban birnin jihar.

    APC ta yi zargin cewa ta samu tabbacin Inec na shirin mayar da tattara ƙuri'un Yenagoa ne bayan kaɗa su a wuraren da take ganin tana da ƙarfi.

    A cewar Kakakin APC na Ƙasa Felix Morka, shirin "ba abin amincewa ba ne" kuma "abin zargi" saboda zai iya shafar ingancin zaɓen na Bayelsa.

    "Muna kira ga Inec ta tattara sakamakon a wuraren da aka kaɗa ƙuri'un," kamar yadda ya yi kira a sanarwar da ya fitar.

  5. Sakamakon zaɓen Kogi da Bayelsa kai-tsaye

    Baya ga bayanan da muke wallafawa kai-taye a wannan shafi, kuna iya samun tsuran adadin da kowace jam'iyya ta samu idan kuka latsa nan.

  6. An tafi hutu a zaman tattara sakamakon Kogi

    Babban Baturen Zaɓe na jihar Kogi, Farfesa Johnson Ozoemenam Urama, ya ɗage zaman tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka yi ranar Asabar.

    Ya ce sai ƙarfe 4:00 za su ci gaba da zaman.

    Zuwa yanzu sakamakon ƙaramar hukuma uku ne kawai suka rage kafin a bayyana wanda ya lashe zaɓen bayan bayyana 18 tun daga safiyar yau Lahadi.

  7. Kogi: Ƙaramar hukumar Ijumu

    Masu zaɓe: 66482

    Masu zaɓen da aka tantance: 20405

    APC - 10524

    ADC - 1898

    PDP - 6909

    SDP - 356

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 20375

    Halastattun ƙuri'u: 19991

    Ƙuri'un da aka soke: 384

  8. Kogi: Ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas

    Masu katin zaɓe: 53436

    Masu zaɓen da aka tantance: 18001

    APC - 7096

    ADC - 7453

    PDP - 2615

    SDP - 312

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 17993

    Halastattun ƙuri'u: 17649

    Ƙuri'un da aka soke: 344

  9. Kogi: Ƙaramar hukumar Kabba/Bunu

    Registered votes Masu katin zaɓe: 87162

    Masu zaɓen da aka tantance: 24242

    APC - 12376

    ADC - 1537

    PDP - 8566

    SDP - 942

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 24242

    Halastattun ƙuri'u: 23823

    Ƙuri'un da aka soke: 419

  10. Kogi: Ƙaramar hukumar Okehi

    Masu katin zaɓe: 94456

    Masu zaɓen da aka tantance: 57243

    APC - 53062

    ADC - 689

    PDP - 2722

    SDP - 153

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 57176

    Halastattun ƙuri'u: 57002

    Ƙuri'un da aka soke: 174

  11. Kogi: Ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma

    LGA - Yagba West

    Masu katin zaɓe: 51234

    Masu zaɓen da aka tantance: 17152

    APC - 7969

    ADC - 4556

    PDP - 3010

    SDP - 1002

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 17101

    Halastattun ƙuri'u: 16738

    Ƙuri'un da aka soke: 363

  12. Bayelsa: An tafi hutu a zaman tattara sakamako

    Babban Baturen Zaɓe na jihar Bayalesa Farfesa Farouk Kuta ya ɗage zaman tattara sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar ranar Asabar.

    Ya ce sai ƙarfe 3:00 na rana za a ci gaba da zaman.

    Zuwa yanzu an bayyana sakamakon ƙaramar hukuma uku na Kolokuma/Opokuma, da Ogbia, da Yenagoa.

  13. Shahararren ɗan wasan kwaikwayo Samanja ya rasu

    Shahararren ɗan wasan kwaikwayon nan Usman Baba Pategi, wanda aka fi sani da Samanja Mazan Fama, ya rasu yana da shekara 81, kamar yadda iyalansa suka faɗa wa BBC.

    Rahotonni sun ce tsohon ɗan wasan ya rasu ne ranar Asabar da tsakar dare a garin Kaduna bayan ya sha fama da jinya.

    Ɗan marigayin mai suna Mohammed Usman ya faɗa wa jaridar Daily Trust cewa mahaifinsa ya bar mata biyu.

    "Ya bar mata biyu da 'ya'ya 12," a cewarsa.

    Samanja ya shahara ne a fina-finan gidan talabijin na NTA a shekarun 1980 zuwa 1990, inda ya taka rawa a matsayin soja.

  14. Kogi: SDP ta cinye ƙaramar hukumar Idah

    Masu katin zaɓe: 64,339

    Masu zaɓen da aka tantance: 23,044

    APC: 2,033

    ADC: 91

    PDP: 271

    SDP: 20,059

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 23,022

    Halastattun ƙuri'u: 22742

    Ƙuri'un da aka soke: 280

  15. Ogori/Mogongo: Ƙaramar hukuma mai cike da taƙaddama a zaɓen Kogi

    Yanzu kuma sai ƙaramar hukumar Ogori/Mogongo ta jihar Kogi, inda hukumar zaɓe ta soke sakamakon zaɓen na jiya Asabara a mazaɓu tara cikin 10 da ke yankin saboda zargin maguɗi.

    Saboda haka, sakamakon mazaɓa ɗaya kacal aka gabatar daga ƙaramar hukumar kamar haka:

    A - 0

    AA-0

    AAC - 0

    APC - 362

    ADC - 11

    ADP -1

    APGA - 0

    APN - 0

    APP - 0

    BP - 0

    LP - 1

    Nnpp -0

    NRN - 2

    PDP - 86

    PRP - 0

    SDP - 195

    YPP - 0

    ZLP - 0

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 665

    Halastattun ƙuri'u: 658

    Ƙuri'un da aka soke: 7

  16. Bayelsa: PDP ta sake lashe ƙaramar hukumar Ogbia

    Masu katin zaɓe: 119,571

    Masu zaɓen da aka tantance: 36,955

    APC: 16,319

    LP: 57

    PDP: 18,435

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 35,468

    Halastattun ƙuri'u: 34,971

    Ƙuri'un da aka soke: 497

  17. PDP ta ci ƙaramar hukumar Kolokuma/Opokuma ta Bayelsa

    Jimillar adadin masu katin zaɓe: 65,364

    Waɗanda aka tantance: 24,171

    APC: 5,349

    LP: 22

    PDP: 18,465

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 24,059

    Halastattun ƙuri'u: 23,918

    Ƙuri'un da aka soke: 141

  18. An fara tattara sakamakon zaɓe a jihar Bayelsa

    Babban baturen zaɓe da tawagarsa sun fara zaman tattara sakamakon zaɓen gwamna da aka gudanar ranar Asabar.

    Yanzu haka wani baturen zaɓe ne daga wata ƙaramar hukuma ke gabatar da sakamakon mazabarsa.

  19. ICPC ta kama mutum shida da zargin sayen ƙuri'u a jihar Imo

    Dakarun hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya ta ICPC sun kama mutum shida da zargin sayen ƙuri’a yayin zaɓen gwamna a jihar Imo.

    Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a dandalin X ta ce a kama mutanen ne a rumfunan zaɓe bakwai tare da ƙwace kuɗi naira miliyan huɗu da 100,000 (N4,101,750 ) a hannunsu.

    Kazalika, an karɓe wani littafi ɗauke da sunayen mutane da lambobin wayarsu daga hannun ɗaya daga cikin mutanen, in ji ICPC.

    Hukumar ta ce ta ɗauki bayanan dukkaninsu kafin daga baya ta bayar da belinsu, yayin da take ci gaba da bincike a kansu.