Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa zuwa Litinin

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Mu kwana lafiya!

    Masu bibiyar mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarun da muke kawo muku na ranar Lahadi, sai kuma gobe Litinin idan Allah Ya kai mu.

    Haruna Ibrahim Kakangi ke cewa mu kwana lafiya!

  2. Usman Ododo na APC ya lashe zaɓen gwamnan Kogi

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta bayyana Usman Ahmed Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda lashe zaɓen gwaman jihar Kogi na shekara ta 2023.

    Babban jami'in tattara sakamakon zaɓe na hukumar INEC a jihar Kogi, Johnson Ozoemenam Urama ne ya tabbatar da nasarar ta Ododo a sanarwar da ya bayar cikin daren ranar Lahadi.

    INEC ta ce Ododo na APC ya samu ƙuri'a 446,237, saboda haka shi ne halastaccen zaɓaɓɓen gwamnan jihar, kasancewar shi ne ya samu ƙuri'a mafi rinjaye.

    Muritala Yakubu Ajaka na jam'iyyar SDP shi ne ya zo matsayi na biyu, inda ya samu ƙuri'a 259,052.

    Dino Melaye na jam'iyyar PDP ne ya zo na uku da ƙuri'u 46,362.

    Sai kuma Abejide Leke Joseph na jam'iyyar ADC wanda ya samu ƙuria 21,819.

    Gabanin sanar da nasarar Ododo, hukumar zaɓen ta ce ba za a gudanar da zaɓuka a rumfunan da ta dakatar da zaɓe ba a ranar Asabar.

    An dakatar da zaɓe a wasu rumfuna ne bayan samun bayanai na almundahana, inda aka ga cikakkun takardun sakamako tun gabanin fara kaɗa ƙuri'a.

    Sai dai a bayanin da jami'in hukumar INEC ya yi gabanin sanar da wanda ya yi nasara, ya ce yawan katin zaɓe da aka karɓa a dukkanin wuraren da aka soke zaɓe ya tsaya ne a 16,247.

    Hakan na nufin koda an sake zaɓen ba zai shafi nasarar ɗan takarar da ke gaba a yawan ƙuri'a ba.

    Ahmed Ododo ya bai wa mai biye masa ratar ƙuri'a 187,185.

  3. Ba za a sake zaɓen gwamnan Kogi a rumfunan da aka dakatar ba - INEC

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya a jihah Kogi ta ce ba za a gudanar da zaɓe a mazaɓun da aka dakatar ba kasancewar yawan waɗanda suka yi rajista ba su da yawan a-zo-a-gani.

    Babban jami'in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar ne ya bayyana haka yayin da yake sanar da jimillar sakamakon zaɓen gwamnan jihar da yammacin ranar Lahadi.

    Ya ce yawan katin zaɓen da aka karɓa a inda aka dakatar da zaɓen shi ne 16,247.

    Hakan na nufin cewa ƙuri'un da za a kaɗa ba za su iya sauya sakamakon da ake da shi a hannu yanzu ba.

  4. APC na kan gaba a zaɓen gwamnan Kogi bayan tattara sakamakon ƙananan hukumomi 21

    Bayan tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kogi daga dukkanin ƙananan hukumomi 21 na jihar, alƙaluma na nuna cewa jam'iyyar APC ita ce ke gaba a yawan ƙuri'a.

    Sakamakon da Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta bayyana bayan kawo ƙaramar hukuma ta ƙarshe, wato Ibaji, ya nuna cewa a jimilla:

    • APC ta samu ƙuri'u 446,237
    • SDP ta samu ƙuri'u 259,052
    • PDP ta samu ƙuri'u 46,362

    Yanzu haka dai jami'an hukumar ta INEC na ganawa domin tattara alƙaluman nasu tare da bayyana matsayar da suka cimma.

    Tun farko hukumar ta sanar da cewa akwai wasu gundumomi a jihar ta Kogi da aka dakatar da zaɓukansu sanadiyyar zargin aikata ba daidai ba.

    Babu tabbas ko hakan zai shafi sanarwa ta ƙarshe da hukumar za ta bayar domin ayyana wanda ya yi nasara.

  5. Labarai da dumi-dumi, Kogi: An kawo sakamakon ƙaramar hukuma ta ƙarshe

    Ƙaramar hukumar Ibaji

    Masu katin zaɓe - 90556

    Masu zabe da aka tantance - 25099

    APC - 6991

    ADC - 133

    PDP - 269

    SDP - 16984

    Adadin ƙuri'un da aka kaɗa - 25053

    Halastattun ƙuri'u - 24589

    Ƙuri'un da aka soke - 464

  6. Hamas ta ce mutanen da suka mutu a Gaza sun kai 11,180

    Hukumomi a Gaza sun ce adadin mutanen da suka mutu tun bayan ɓarkewar rikicin baya-bayan nan ya kai 11,180.

    Alƙaluman na baya-bayan nan sun nuna cewa ƙananan yara 4,609, tare da mata 3,100 ne suka mutu.

    Hukumomin sun ce mutanen da suka jikkata sun kai 28,200.

  7. Labarai da dumi-dumi, INEC ta ɗage karɓar sakamakon Bayelsa zuwa gobe Litinin

    Hukumar zaɓen Najeriya ta sanar da ɗage karɓar sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa zuwa ƙarfe 12:00 na ranar gobe Litinin 13 ga watan Nuwamba.

    Hakan ya faru sakamakon har yanzu ana ci gaba da ƙarbar sakamakon a matakan rumfuna da mazaɓu a ƙananan hukumomin Brass da Ijaw ta Kudu da suka rage.

    Shugaban sashen hulda da jama'a da ilimartar da masu kaɗa ƙuri'a na hukumar zaɓen Jihar, Wilfred Ifogah ya ce an sake gudanar da wasu zaɓukan a wasu mazaɓu da rumfunan zaɓe a ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu, annan har yanzu ana karɓar sakamakon a matakan mazaɓu a ƙaramar hukumar Brass.

    Ya kuma ƙara da cewa sakamakon yanayin da wuraren ke ciki, da koguna suka kewaye, hukumar ta ɗauki matakin ɗage karɓar sakamakon zuwa gobe, domin ba su damar kammala tattara sakamakon a matakan ƙananan hukumomi.

  8. Labarai da dumi-dumi, Zaɓen Kogi: An sake tafiya hutu zuwa ƙarfe 9:00pm

    Hukumar zaɓe ta sake tafiya hutun aƙalla sa'a guda, kafin ta dawo ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kogi.

    A halin yanzu ƙaramar hukumar ɗaya ce kawai ta rage a kammala tattara sakamakon zaɓen daga ƙananan hukumomin jihar

  9. Kogi: Ƙaramar hukumar Lokoja

    Masu katin zaɓe - 157248

    Masu zaɓe da aka tantance - 36526

    APC - 19105

    ADC - 758

    PDP - 4028

    SDP - 10380

    Yawan ƙuri'un da aka kaɗa - 36140

    Halastattun ƙuri'un da aka kaɗa - 34932

    ƙuri'un da aka soke - 1208

  10. Kogi: Ƙaramar hukumar Igalamela/Odolu

    Masu katin zaɓe: 77577

    Masu zaɓen da aka tantance: 27365

    APC - 2976

    ADC - 61

    PDP - 140

    SDP - 23185

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 26725

    Halastattun ƙuri'u: 26665

    Ƙuri'un da aka soke: 696

  11. Labarai da dumi-dumi, INEC ta ci gaba da karɓar sakamako a jihar Kogi

    Hukumar zaɓen Najeriya ta dawo daga hutun da ta tafi daga karɓar sakamakon ƙananan hukumomin jihar.

    A hali yanzu ƙananna hukumomi uku ne suka rage a karɓe su.

    Tun da farko INEC ta ɗage karɓar sakamakon zuwa ƙarfe 7:00 na maraice

  12. INEC ta sake dakatar da zaɓe wasu rumfuna a Kogi

    Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce ta sake dakatar da zaɓukan wasu rumfunan zaɓe a wasu sassan jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.

    Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta samu ƙarin bayanan zargin cike takardun sakamako tun kafin fara kaɗa ƙuri'a a wasu sassan jihar.

    Sanarwar ta ce an samu wannan zargi a rumfunan zaɓe biyar a ƙaramar hukumar Adavi, da wasu rumfunan biyar a ƙaramar hukumar Ajaokuta da biyar a ƙaramar hukumar Okene da ɗaya a ƙaramar hukumar Okehi.

    INEC ɗin ta ƙara da cewa ɗaukar matakin sake zaɓe a wuraren ya dogara ne da irin ratar da ke tsakanin wanda ya ci zaɓen bayan kammala tattara gaba ɗaya sakamakon zaɓen.

  13. Amsoshin Takardunku

  14. An sake ɗage karɓar sakamakon zaɓen gwamnan Bayelsa zuwa ƙarfe 6:00

    Can ma a jihar Bayelsa da ke yankin kudu maso kudancin Najeriya hukumar zaɓe ta INEC ta sake ɗagw karɓar sakamakon zuwa ƙarfe 6: 00 na maraice.

    A halin yanzu ƙananan hukumomi biyu ne suka rage a kammala tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar.

  15. An sake ɗage karɓar sakamakon zaɓen gwamnan Kogi zuwa ƙarfe 7:00 na yamma

    Hukumar zaben Najeriya ta sake ɗage lokacin karɓar sakamakon zaɓen gwamnan jihar Kogi zuwa ƙarfe 7:00 na maraice.

    Ƙananan hukumomi uku ne suka rage ba a bayyana sakamakonsu ba, saboda rashin isa ɗakin tattara sakamakon zaɓen, da ke birnin Lokoja.

    Tun da farko jami'in tattara sakamakon zaɓen ya sanar da hutu zuwa ƙarfe 4:00 na yamma, domin bayar da dama ga ƙananan hukumomin su ƙarasa.

    Wakiliyar BBC da ke ɗakin tattara sakamakon ta ce a halin yanzu ƙarama guda ta isa zauren tattara sakamakon, to sai dai an sake tsawaita hutun zuwa ƙarfe 7:00 na yamma domin bayar da dama ga sauran biyun da ke kan hanya su ƙarasa.

  16. Hamas ta ce majinyata na mutuwa a asibitin Al-Shifa saboda rashin aikin likitoci

    A ƙarshen makon da muke cikin hankula su koma kan babban asibitin Al-Shifa da ke Gaza.

    A ɗazu ne, gidan talbijin na Al-Jazeera ya ambato mai magana da yawun ƙungiyar Hamas - wadda ke iko da ma'aikatar lafiyar Gaza - na cewa mutum biyar da suka samu raunuka a asibitin sun mutu saboda likitocin sun kasa yi musu aiki.

    Hakan na faruwa ne sakamakon rashin man fetur a asibitin, kuma duka asibitin ya tsaya da aiki, sakamakon hare-haren Isra'ila, kamar yadda Ashraf al-Qudra ya bayyana.

    Sai dai bai bayyana haƙiƙanin lokacin da majinyatan suka mutu ba.

    Hukumomi lafiya da likitoci masu rajin kare hakƙin ɗan'adam sun ce jarirai biyu da aka ajiye a kwalba sun mutu, yayin da rayukan gommai ke cikin hatsari.

    To sai dai yanayi a asibtin Al-Shifa - ciki har da rashin man fetur - ya tsananta

    Shugaban Isra'ila Isaac Herzog ya shaida wa BBC cewa "komai na tafiya daidai a asibitin, kuma iƙirarin da rashin wutar lantarki 'juyar da gaskiya ne da Hamas ke yi".

    Sojojin Isra'ila sun musanta kai hari asibitin, amma sun ce suna yaƙi da Hamas a kusa da asibitin.

    Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce rasa hanyoyin sadarwa da jami'anta da ke asibitin.

  17. Amfanin ganyen Ugu ga lafiyar ɗan'adam

    Ganyen Ugu na daga cikin abinci dangin gayayyaki da ke da matuƙar amfani da lafiyar ɗan'adam.

    Ganye ne da ake iya samunsa a kowane yanayin lokaci na shekara.

    Ugo na ɗauke da sinadari masu yawa da ke taimaka wa wajen ƙarin jini da sauran sinadarai

  18. APC na kan gaba a zaɓen gwamnan jihar Kogi

    Bayan da hukumar zaɓen Najeriya (INEC) ta sanar da sakamakon ƙananan hukumomi 18 a zaɓen gwamnan jihar Kogi, ɗan takarar jam'iyyar APC, Usman Ahmed Ododo ne ke kan gaba.

    Yanzu ana jiran sakamako daga ƙananan hukumomi uku.

    Ƙananan hukumomin da ake jiran sakamakonsu a zaɓen na gwamnan su ne:

    • Lokoja
    • Igalamela- Odolu
    • Ibaji

    Kogi na da ƙananan hukumomi 21 a jimilla.

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ce ke da hurumin sanar da wanda ya yi nasara bayan kammala tattara sakamakon zaɓen.

  19. Kogi: Ƙaramar hukumar Ofu

    Masu katin zaɓe: 101964

    Masu zaɓen da aka tantance: 36087

    APC - 5245

    ADC - 297

    PDP - 293

    SDP - 28768

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 35767

    Halastattun ƙuri'u: 35180

    Ƙuri'un da aka soke: 587

  20. Kogi: Ƙaramar hukumar Adavi

    Masu katin zaɓe: 114663

    Masu zaɓen da aka tantance: 103251

    APC - 101156

    ADC - 268

    PDP - 1005

    SDP - 268

    Jimillar ƙuri'un da aka kaɗa: 103172

    Halastattun ƙuri'u: 103105

    Ƙuri'un da aka kaɗa: 67