Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail, Haruna Kakangi and Abdullahi Bello Diginza
Ɗan takarar APC a Bayelsa ya kaɗa ƙuri'arsa
Ɗan takarar gwamnan Bayelsa a jam'iyyar APC, Timipre Sylva, ya jefa ƙuri'arsa a zaɓen gwamnan jihar da ke gudana.
Akwatinsa mai lamba Unit 4 Dukuraku Central Open Space Ward 4, tana yankin ƙaramar hukumar Okpoama Brass da ke jihar.
Mutane ɗauke da sanduna na korar 'yan jaridar BBC daga rumfar zaɓe
Wasu mutane ɗauke da sanduna na korar 'yan jarida daga rumfar zaɓe mai lamba 200 Unit Estate da ke birnin Lokoja na jihar Kogi.
"Dole suka kora mu bayan wasu manyan duwatsu da suka shata layi da su," a cewar tawagar BBC da ke birnin.
Mutanen sun kori tawagar BBC duk da cewa sun yi musu bayanin cewa 'yan jarida ne su.
"Mun faɗa musu cewa mu 'yan jarida ne amma duk da haka sun ce mu tafi sai an fara ƙirga ƙuri'a sannan mu dawo," in ji su.
Ana fargabar bakwaini 39 za su mutu a Gaza bayan katsewar lantarki a asibiti
Asalin hoton, Getty Images
Ministan lafiya na Falasinawa ya ce jarirai bakwaini guda 39 waɗanda ke cikin kwalba na cikin hatsarin mutuwa a asibitin Al-Shifa da ke Gaza.
Duk da cewa jariran na cikin kwalba, to amma katsewar wutar lantarki na nufin cewa iskar da suke amfani da ita ita ma za ta katse.
Yanzu haka ma'aikatan lafiya na bakin ƙoƙarinsu na ganin sun samar wa bakwainin iska kai-tsaye.
Sai dai ma'aikatan lafiyar na cewa jariran za su iya mutuwa cikin watanni ƙalilan.
Rumfar zaɓen da mutum ɗaya ya kaɗa ƙuri'a a Imo
Yayin da akeci gaba da kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓe daban-daban a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya, wasu rumfunan ba abin da ake yi sai jira kawai.
A wanann rumfar da ke St. Luke’s Referral Hospital a birnin Owerri, mutum ɗaya ne kacal ya kaɗa ƙuri'arsa zuwa ƙarfe 12:00.
Jimillar mutum huɗu ne suka yi rajista a rumfar. "Wannan na nuna irin ƙarancin fitowar masu jefa ƙuri'a a zaɓen," in ji wakilin BBC Tunde Osasanya.
An toshe hanyoyin zuwa ƙananan hukumomi a jihar Kogi
A jihar Kogi, hukumomi na amfani da manyan motoci don toshe hanyoyin zuwa wasu ƙananan hukumomi yayin da ake ci gaba da kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar.
Wakiliyar BBC a Lokoja Madina Maishanu ta ce mutane ba su da damar tsallakawa zuwa wasu garuruwan ko da kuwa suna da katin shaidar zirga-zirga da hukumomi ke bayarwa.
Waɗannan hotunan da ta ɗauka suna nuna yadda aka toshe hanyar zuwa garin Obajana daga Lokoja, babban birnin jihar.
Bai kamata a dinga yin zaɓe lokuta daban-daban a jihohin Najeriya ba - Goodluck Jonathan
Bayanan hoto, Goodluck Jonathan ya mulki Najeriya daga 2010 zuwa 2015
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya nemi majalisar tarayyar ƙasar ta mayar da lokutan zaɓen gwamna lokaci ɗaya a ƙasar ba tare da ware wasu ba kamar yadda ake yi a yanzu.
Jonathan ya yi kiran ne jim kaɗan bayan ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen gwamnan jihar Bayelsa da ke gudana a yau Asabar tare da na jihohin Kogi da Imo.
"Idan muka ci gaba da yin irin wannan zaɓen na bayan babban zaɓe saboda shari'o'i to wata rana shi ma zaɓen shugaban ƙasar Najeriya zai sauka daga lokacin da aka saba yin sa," in ji shi.
Ya bayar da misali da zaɓen shugaban ƙasa na 2007, inda ya ce alƙalan kotun ƙoli uku cikin bakwai ne suka ce a sake zaɓe, yayin da huɗu suka amince da sahihancinsa.
"Da a ce alƙali ɗaya ya bi sawun waɗanda suka ce a sake zaɓe da tuni zaɓen shugaban ƙasa ya sauka daga kan lokacin da aka saba yin sa."
Jihohin sun sauka daga layin lokacin da aka saba gudanar da babban zaɓe ne saboda hukunce-hukuncen kotu da ke ƙwacewa ko kuma su bayar da umarnin a sake zaɓe a jihohin.
Akwai jihohi bakwai da ba su yin zaɓen gwamna tare da saura a Najeriya, waɗanda suka haɗa da Kogi, da Imo, da Bayelsa, da Edo, da Anambra, da Osun, da Ekiti.
Labarai da dumi-dumi, Muna bincike kan takardun sakamakon zaɓe da aka cike kafin fara zaɓe - Inec
Hukumar zaɓe ta ƙasa a Najeriya, Inec, ta ce tana bincike kan ƙorafin da aka kan wasu takardun rubuta sakamakon zaɓe da aka cike tun kafin fara kaɗa ƙuri'a a jihar Kogi.
"Hukumar na ɗaukar wannan lamari da muhimmanci," in ji ta cikin wani saƙon X.
"Manyan jami'anmu da aka tura jihar na bincike game da lamarin, kuma za mu bayyana matakin da muka ɗauka nan take."
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Ƙungiyar sa-ido kan zaɓuka da kyautata dimokuraɗiyya ta Yiaga Africa ta ce lamarin ya faru ne a rumfar zaɓe mai lamba PU 004, Eni Ward da ke ƙaramar hukumar Ogori/Magongo.
Ƙungiyar ta wallafa wani hoto da ake zargin na sakamakon zaɓen rumfar ne da aka riga aka cike, tana mai kira ga hukumar zaɓe ta Inec da ta bincika lamarin.
Shi ma ɗan takarar gwamnan Kogi na PDP, Sanata Dino Melaye, ya yi irin wannan zargi cikin wani bidiyo da ya wallafa.
Goodluck Jonathan ya kaɗa ƙuri'arsa
Tsoohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya kaɗa ƙuria'rsa a zaɓen gwamnan Bayelsa.
Jonathan ya jefa ƙuri'ar ce a rumfar zaɓe ta Unit 39 Ward 13 da ke Otuoke, ƙaramar hukumar Ogbia.
Gwamnan Bayelsa Douye Diri ya kaɗa ƙuri'arsa
Asalin hoton, Bayelsa Government House
Gwamnan Bayelsa, Douye Diri, ya kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen gwamna da ke gudana yau Asabar.
Ya kaɗa ƙuri'ar tasa ne tun da misalin ƙarfe 8:40 a rumfar zaɓe mai lamba Unit 4 Ward 6 da ke Sampou a ƙaramar hukumar Kolokuma/Opokuma.
Gwamna Diri na neman wa'adi na biyu ne ƙarƙashin jam'iyyar PDP.
Ana zargin cike takardar sakamakon zaɓe tun kafin fara kaɗa ƙuri'a a Kogi - Yiaga Africa
Ƙungiyar sa-ido kan zaɓuka da kyautata dimokuraɗiyya ta Yiaga Africa ta ce ta karɓi ƙorafi game da takardun rubuta sakamakon zaɓe da aka cike tun kafin a fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan jihar Kogi.
Cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X, Yiaga Africa ta ce lamarin ya faru ne a rumfar zaɓe mai lamba PU 004, Eni Ward da ke ƙaramar hukumar Ogori/Magongo.
Ƙungiyar ta wallafa wani hoto da ake zargin na sakamakon zaɓen rumfar ne da aka riga aka cike, tana mai kira ga hukumar zaɓe ta Inec da ta bincika lamarin.
Shi ma ɗan takarar gwamnan Kogi na PDP, Sanata Dino Melaye, ya yi irin wannan zargi cikin wani bidiyo da ya wallafa.
Zaɓen gwamnan Kogi: An girke motoci masu sulke a sassan Lokoja
Yayin da aka fara kaɗa ƙuri'a a rumfunan zaɓe da dama da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi, da ma wasu yankunan na jihar, jami'an tsaro sun bazu a sassa daban-daban na jihar domin tabbatar da tsaro.
A birnin Lokoja za a iya ganin motoci masu sulke ɗauke da jami'an sojoji da na ƴan sanda.
Gabanin zaɓen, hukumomin tsaro da dama sun yi bayanin cewa za su tabbatar an gudanar da zaɓen ba tare da tashin-tashina ba.
Kwana ɗaya gabanin zaɓen, mai taimaka wa shugaban Najeriya kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu ya fitar da wata sanrwa inda ya ce gwamnatin ta sha alwashin daƙile duka wani yunƙuri na tayar da husuma.
A wasu wuraren kuma jami'an tsaro sun kafa shinge domin hana mutane zirga-zirga.
Rundunar ƴan sanda ta ce an hana duk wata zirga-zirga al'umma da ababen hawa waɗanda ba su zama wajibi ba daga ƙarfe 12 na daren ranar Asabar.
Mun hana dakarunmu raka jami'an gwamnati kaɗa ƙuri'a - 'Yan sandan Kogi
Asalin hoton, NPF
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kogi da ke tsakiyar ƙasar ta ce ta hana jami'anta yi wa jami'an gwamnati da masu hannu da shuni rakiya zuwa rumfunan zaɓensu a yau.
DIG Abu Amadu Sani, shi ne shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar wanda kuma aka tura don jagorantar tsaro yayin zaɓen gwamnan Kogi, ya ce sun ɗauki matakin ne don ƙara yawan jami'an tsaron a rumfunan zaɓe.
'Yan takara 18 ne ke fafata da juna a Kogi, sai dai ana ganin za ta fi zafi ne tsakanin jam'iyyun APC mai mulki, da PDP, da kuma SDP.
Baya Kogi, masu zaɓe na kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamna a jihohin Imo (a kudu maso gabas) da kuma Bayelsa (a kudu maso kudu).
Hukumar zabe ta ce za a fara kaɗa ƙuria da karfe 8;30 na safe zuwa karfe 2;30 na rana.
Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Raliya Zubairu daga jihar Kogi:
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari rahoton Raliya Zubairu daga jihar Kogi:
Jirgin ruwa ya kife da ma’aikatan zaɓe a Bayelsa
Hukumar
zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) a jihar Bayelsa ta tabbatar da cewa
wani jirgin ruwa ɗauke da malaman zaɓe da kayan aiki ya kife a ƙaramar hukumar
Ijaw ta kudu da ke jihar.
A
cikin wata sanarwa da ta fitar ta hannun shugaban sashen hulɗa da jama’a da
wayar da kan al’umma na hukumar a jihar ta Bayelsa, Inec ta ce malaman zaɓen na
kan hanyarsu ce ta zuwa rumfar zaɓe ta Koluama.
Sai
dai sanarwar ta ce an yi sa’a babu ko ɗaya daga cikin malaman zaɓe 12 da ke
cikin jirgin ruwan da ya rasa ransa.
Amma
ta ce kayan zaɓe, kamar takardar rubuta sakamako da sauran kayan malaman zaɓen
sun salwanta a cikin ruwa.
Inec ta ce duk da haka za ta yi ƙoƙarin ganin an gudanar da zaɓe a yankin.
An sace malamin zaɓe
Haka nan sanarwar ta ci gaba da cewa an sace wani malamin zaɓe da aka tura mazaɓar Ossioma da ke ƙaramar hukumar Sagbama a jihar ta Bayelsa.
Ta ce an sace mutumin ne sa'ilin da yake jiran jirgin ruwan da zai shiga zuwa inda aka tura shi, a tashar jiragen ruwa ta Amassoma.
Inec ta ce an sanar da jami'an tsaro game da ɓacewar jami'in nata.
Mazauna Lokoja sun fara jefa ƙuri'a
Masu zaɓe sun fara jefa ƙuri''unsu a Lokoja, babban birnin jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya.
Wannan rumfar zaɓe ta Ward A, Open Space, Unit 14, ta ɗauki harama, inda tuni aka fara cika akwati da ƙuri'u.
Mazauna birnin Owerri na Imo sun fara kaɗa ƙuri'a
A birnin Owerri na jihar Imo ma an fara kaɗa ƙuri'a a zaɓen gwamnan.
Kelechi Okafor ne mutum na farko da ya kaɗa ƙuri'arsa a rumfar zaɓe ta Ikenegbu Layout Primary School da ke jihar a kudu maso gabashin Najeriya.
'Yan takarar gwamna a jihar Bayelsa
Asalin hoton, X/Douye Diri
Bayanan hoto, Gwamna Douye Diri na PDP na neman wa'adi na biyu a kan mulki
Hukumar INEC ta ce kimanin mutum 1,056,862 ne suka yi rajistar zaɓe jihar, inda mutum 1,017,613 suka.
Ƴan takara 16 ne ke fafatawa a zaɓen domin neman ɗarewa kujerar gwamnan, ciki har gwamnan jihar, Sanata Douye Diri na jam'iyyar PDP da ke neman wa'adin mulki na biyu.
Daga cikin manyan ƴan takarar da ke fafatawa a zaɓen na yau har da tsohon ministan man fetur, Timipre Sylva na jam'iyyar APC, da Udengs Eradiri na LP.
'Yan takarar gwamna a jihar Imo
Asalin hoton, Facebook/Hope Uzodinma
Bayanan hoto, Gwamna Hope Uzodinma na jam'iyyar APC na neman wa'adi na biyu a kan mulki
Hukumar zaɓen ƙasar ta ce mutum 2,419, 922 ne suka yi rajistar zaɓe a jihar, yayin da mutum 2,318,919 suka karɓi katunan zaɓensu.
Manyan ƴan takarar da ke kan gaba a zaɓen gwamnan jihar, sun haɗa da gwamnan jihar, Hope Uzodinma na jam'iyyar APC. wanda ke neman wa'adin mulki na biyu.
Mista Uzodinma - wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne - na neman wa'adin mulkin jihar karo na biyu.
Sai Athan Achonu na jam'iyyar LP, wadda ke da farin jini a yankin kudu maso gabashin ƙasar.
Samuel Anyanwu na jam'iyyar PDP da kuma Tony Ejiogu na jam'iyyar APGA, da Ben Uche Odunze na NNPP, sai kuma Obinna Bright Ekwelem na jam'iyyar SDP.
'Yan takarar gwamnan jihar Kogi
Asalin hoton, Twitter/Facebook
Ƴan takara 18 ne ke fafatawa a zaɓen gwamnan jihar Kogi.
Sai dai ana ganin fafatawar za ta fi zafi ne tsakanin ƴan takarar APC, Ododo Ahmed Usman, da Sanata Dino Melaye na PDP, da kuma Murtala Yakubu Ajaka na jam'iyyar SDP.
Mutum 1,932, 654 ne suka yi rajistar zaɓe a jihar Kogi, yayin da mutum 1,833,160 suka karɓi katin zaɓensu kamar yadda bayanan hukumar INEC ɗin suka nuna.
Masana harkokin siyasa na ganin cewa manyan ƴan takarar uku da ke sahun gaba a zaɓen sun fito ne daga ƙabilu daban-daban, kamar Ebira, Igala, da kuma Okun, kuma hakan zai iya yin tasiri sosai kan sakamakon zaɓen.
Sun ƙara da cewa yayin da jam'iyyar APC za ta iya samun yawan ƙuri'u daga tsakiyar jihar, SDP za ta iya bayar da mamaki a gabashin jihar, inda ita kuma PDP mai ɗimbin magoya baya a yammacin jihar, za su zaɓi Dino Melaye.
Sauran ƴan takarar su ne:
Jibrin Usman Oyibe – A
Braimoh Olayinka Adenehon – AA
Achimugu Augustine Abu – AAC
Abejide Leke Joseph – ADC
Elukpo Julius – ADP
Ilonah Idoko Kingsley – APGA
Isah Dauda Utenwojo – APM
Onaji Sunday Frank – APP
Muhammad Kabir Umar – BP
Okeme Adejoh – LP
Musa Saliu Mubarak – NNPP
Dirisu Bala Abdulghafar – NRM
Dr. Abdullahi Bayawo – PRP
Omale Samson Agada – YPP
Suleiman Taiye Fatima - ZLP
An fara kaɗa ƙuri'a a Bayelsa
Masu zaɓe a ƙaramar hukumar Yenagoa ta jihar Bayelsa sun fara kaɗa ƙuri'a.
Kamar yadda ake gani a wannan hoton na sama, wannan matar ce ta farko da ta kaɗa ƙuri'a a rumfar zaɓe ta 14 Amarata da ke Mazaɓar I.
Kwale-kwale ya kife da jami'an Inec ɗauke da kayayyakin zaɓe
A jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya, hukumar zaɓe ta ƙasa National Independent Eloctoral Commission (Inec), ta tabbatar da hatsarin da wani jirgin ruwa ya yi lokacin da yake jigilar jami'anta.
Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa rumfar zaɓe ta 17 a Koluama da ke ƙaramar hukumar Ijawa ta kudu ɗauke da kayayyakin zaɓe masu muhimmanci.
Shugaban sashen wayar da kan masu kaɗa ƙuri'a na Inec a jihar Bayelsa, Wilfred O. Ifodah, ya ce an ceto dukkan jami'ai 12 da ke cikin jirgin.
Sai dai ya ce akwai kayan aikin zaɓe da suka ɓace, waɗanda suka haɗa da takardar rubuta sakamakon zaɓe, da na'urorin cajin batirin kwamfutar aikin zaɓen, da kuma wasu kayyayakin.
Sanarwar da Inec ta fitar ta ce masu zaɓe 5,368 ne suka yi rijista a yankin, kuma 5,311 sun karɓi katin zaɓensu.
Inec ta ce tana bakin ƙoƙarinta don ganin an gudanar da zaɓe a yankin lami lafiya.