Jagoran adawa a Isra'ila, Yair Lapid, ya caccaki Firaminista Benjamin Netanyahu da cewa "ya wuce iyaka" bayan ya ɗora wa jami'an tsaron ƙasar laifin gazawa kan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba.
"Yayin da dakarun sojan Isra'ila [IDF] da kwamandojinsu ke yaƙar Hamas da Hezbollah, shi kuma yana ƙoƙarin ɗora musu alhaki maimakon goya musu baya," kamar yadda Lapid ya wallafa a dandalin X.
Ya ƙara da cewa: "Yunƙurin wanke kai da ɗora wa jami'an tsaro laifi zai lahanta rundunar IDF yayin da take yaƙar maƙiyan Isra'ila. Dole ne Netanyahu ya nemi afuwa."
Tuni Netanyahu ya goge saƙon da ya wallafa a dandalin X, inda ya zargi jami'an da gazawa.
An shafe tsawon lokaci ana rikicin siyasa a Isra'ila kafin harin Hamas da ya kashe Isra'ilawa 1,400 ya tilasta musu jingine rikicin, inda aka kafa gwamnatin gaggawa da za ta jagoranci martani kan 'yan gwagwarmayar na Falasɗinawa.
Ana kiran gwamnatin da majalisar yaƙi ko kuma war cabinet a Turance.