Likitoci a Gaza sun ce Isra'ila ta umarce su da ficewa daga manyan asibitocin yankin

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa musamman kan yaƙin Gaza da Isra'ila.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu sake dawowo domin kawo muku wasu sabbin labaran.

    Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.Rufewa

  2. MDD ta yi gargaɗin rugujewar tsarin doka a Gaza

    Hukumar agaji ta MDD ga Falasdinawa ta yi gargaɗin cewa tsarin kiyaye doka ya fara rugujewa a Zirin Gaza.

    Ta ce dubban mutane sun wawushe manyan wuraren ajiye kayayyakin abinci.

    Sakataren MDD Antonio Guterres, ya ce mummunan halin da ake ciki a Gaza na ƙaruwa duk bayan sa'a daya.

    Mista Guterres ya nanata roƙonsa na tsagaita buda wuta.

    Isra'ila ta ce Masar da Amurka na ƙara faɗada shigar da kayan jin-kai zuwa Gaza.

    Akwai manyan motoci dakon kaya 10 da aka bari suka shiga daga Masar a yau Lahadi,

    Sai dai Masar ta ce akwai ɗaruruwa da aka riƙe saboda binciken Isra'ila

  3. Kalli hayaƙi a kusa da asibitin Al-Quds

    Bidiyon da aka wallafa shafin Telegram ya nuna yadda hayaƙi ya turnuƙe bayan fashewar wani abu a kusa da asibitin Al-Quds da ke arewacin Gaza.

    Tun da farko likitoci da ƙungiyar agajin Falasɗinawa ta Red Crescent da ke aiki a asibitin, sun ce sojojin Isra'ila sun yi musu gargaɗin gaggauta ficewa daga asibitin.

    Red Crescent ta ce akwai kimanin marasa lafiya 400 da ke kwance asibitin, kuma kwashe su abu ne mai sauƙi ba.

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon hayaƙin da ya turnuƙe
  4. Sojojin Ira'ila sun ce sun kashe mayaƙan Hamas a kusa da kan iyakar Isra'ila da Gaza

    .

    Asalin hoton, IDF

    Dakarun soji Isra'ila sun ce sun kashe mayaƙan ƙungiyar Hamas masu yawa a hanyar ƙarƙashin ƙasa a Zirin Gaza, kusa da mashigar Erez da ke kan iyakar Isra'ila da Gaza.

    Cikin wani saƙo da ma'aikatar tsaron Isra'ila ta wallafa a shafinta na Telegram, ta ce sojojinta sun far wa mayaƙan ne a daidai lokacin da suke fitowa daga hanyar ƙarƙashin ƙasar.

    Mashigar Erez na kan iyakar Isra'ila da arewacin Gaza.

    Rundunar sojin Isra'ilar ta ce a baya ta mashigar ne dubban mazauna Gaza ke shiga Isra'ila domin neman aiki ko nema magani idan ba su da lafiya.

    "Hamas ta gina hanyar ƙarƙashin ƙasa a kusa da mashigar Erez, don ta samu damar kai hari kan fararen hula, tare da cutar duk wanda ke zaune a yankin, 'yan Isra'ila da Falasɗinawa," kamar yadda sojojin Isra'ilar suka yi iƙirari.

    A ckin sanawar, Isra'ila ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare zuwa Gaza. Hotunan da ta wallafa tun da farko sun nuna tankokin yai a kusa da tekun yammacin Gaza.

  5. Mutumin da tsoron Allah ya shige shi bayan yin ido-biyu da mutuwa

  6. Labarai da dumi-dumi, An samu rahoton fashewa a kusa da asibitin Al-Quds

    ;

    Asalin hoton, Reuters

    Daraktan ƙungiyar agajin Falasɗinawa ta Red Crescent, Marwan Jilani, ya shaida wa BBC cewa an ji ƙarar abubuwan fashewa a kusa da asibitin Al-Quds, kuma wani makamin roka ya faɗa 'yan mitoci da asibitin.

    Ya ce Harin ya lalata tagogi tare da tilasta wa mutanen da ke zaune a wani ɓangaren ginin zuwa ɗaya ɓangaren.

    Cikin wata sanarwar da ƙungiyar Agaji ta Red Cross ta Duniya - wadda uwa ce ga ƙungiyar agajin Falasɗinawa ta Red Crescent - ta fitar, ta ce ma'aikatan lafiya a asibitin sun ce mata an samu rahotonnin hare-hare a dab da asibitin.

    Mista Jilani ya ƙara da cewa gwamnatin Isra'ila ta sanar da ƙungiyarsa ta baƙin jami'an MDD cewa an soke umarnin kwashe marasa lafiya daga asibitin, to amma ya ce saƙon ya ishe su ne a daidai lokacin da hare-haren bom ke ci gaba da aukuwa a kusa da asibitin.

    “MDD na ƙoƙarin tabbatar da sahihancin batun soke umarnin ƙwashe marasa lafiyar, domin ankarar da sojoji don bai wa asibitin kariya".

  7. Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama domin sauraron shirin
  8. 'Ba mu da tudun mun-tsira'

    .

    Asalin hoton, Rueters

    Abu Qusai Al-Deeb ya kwashe mako uku yana zaune a asibitin Al-Quds da ke birnin Gaza, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

    Ya ce kusan sau shida ana yi masa gargaɗin barin asibitin.

    "Mun ce musu, su gaya mana wuraren da ke da kariya daga hare-haren, za mu fice daga asibitin. Babu wurin mai garanti game kariya, babu a kudu babu a ɗaukacin yankin Gaza," kamar yadda ya ce.

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Daraktan asibitin ya ce kimanain mutum 14,000 ne ke zaune a asibitin Al-Quds
  9. 'An umarce mu da gaggauta ficewa daga asibitin Al-Quds a Gaza'

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Daraktan asibitin Al-Quds da ke birnin Gaza, Bassam Mourad, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ya samu saƙonni masu yawa da ke gargaɗinsu da ficewa daga ginin asibitin.

    “Na samu saon farko ta hanyar kiran waya daga ƙungiyar agajin Falasɗinawa ta Red Crescent, wadda sojojin Isra'ila suka buƙace ta da kwashe duka marasa lafiya da ma'aikata, da duk mutanen da ke zaune a asibitin, zuwa kudancin Gaza".

    "Sun ce wannan wurin zai koma filin gumurzun soji, don haka za a samu arangama mai hatsari a wurin don haka dole mu gaggauta ficewa,” in ji daraktan.

    Ya ƙara da cewa adadin mutanen da ke zaune a asibitin a yanzu ya kai tsakanin 12,000 zuwa 14,000.

    "Adadin na sauyawa a kowace rana, a sashe daban-daban na asibitin da ɓangarorin kula da marasa lafiya".

  10. Amsoshin Takardunku

    Bayanan sautiLatsa hoton da ke sama don sauraron shirin
  11. Muna cikin fargaba kan umarnin sojin Isra'ila na barin asibitin Al-Quds - PCRS

    Gaza

    Asalin hoton, PRCS

    Gamayyar ƙungiyar agaji ta Red Cross & Red Crescent ta ce "ta kaɗu" game da umarnin da ojojin Isra'ila suka bai wa ma'aikata a asibitn Al-Quds da ke Gaza da su bar wajen.

    Asibitin yana bai wa aƙalla mutum 14,000 mafaka da kuma ɗaruruwan marasa lafiya da ke samun kulawa.

    Sanarwar da ƙungiyar ta fitar ta ce: "Asibitoci wuri ne na taimako da kuma neman mafaka, dole ne a kare su. Asibitin Al-Quds da ke Birnin Gaza na kula da ɗaruruwan masu rauni da kuma marasa lafiyar da ke jinya.

    "Kwashe marasa lafiya, ciki har da waɗanda suke sashen kulawa akai-akai da kuma jariran da ke cikin kwalaba, ba zai yiwu ba a irin yanayin da ake ciki.

    "Haka nan ma'aikatanmu sun bayar da rahoton wani hari kusa da asibitin da ke ƙara jefa rayuwar mutane cikin haɗari. Al-Quds na ƙarƙashin kulawar PRCS, gamayyar ƙungiyar Red Cross da Red Crescent da sauran cibiyoyin lafiya kuma dokar ƙasashen duniya ta ba shi kariya."

    Ta ƙara da cewa bai kamata a dinga "jefa ma'aikatan lafiya cikin halin tsaka mai wuya ba ta yadda za su bar marasa lafiya a kwance".

  12. Ƙarin motocin agaji 10 sun shiga Gaza - PCRS

    Ƙungiyar agaji ta Red Crescent reshen Falasɗinu ta ce ta karɓi ƙarin mota 10 na kayan agaji daga mashigar Rafah ta iyakar Gaza da Masar.

    Ta ce motocin na ɗauke da kayan abinci da kuma na kula da lafiya.

    Ta ƙara da cewa jimillar adadin motocin agaji da suka shiga zirin yanzu sun zama 94 tun bayan 7 ga watan Oktoba.

    Sai dai ta ce babu wadda ke ɗauke da man fetur.

  13. Matatar mai ta Kaduna za ta ci gaba da aiki a ƙarshen 2024 - Ministan fetur na Najeriya

    Najeriya

    Asalin hoton, NNPCL

    Ƙaramin Ministan Man Fetur a Najeriya Heineken Lokpobiri ya bayyana cewa za a kammala aikin gyaran matatar mai ta jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar nan da ƙarshen shekarar 2024.

    Mista Lokpobiri ya bayyana haka ne lokacin da ya je ganin yadda aikin ke tafiya ranar Asabar, yana mai bayyana gamsuwa da saurin aikin.

    Ya kuma ci alwashin cewa za su ci gaba da tuntuɓar dukkan masu ruwa da tsaki wajen kammala aikin a kan lokaci.

    A cewarsa, akwai buƙatar kammala gyaran matatar cikin gaggawa "don ciyar da tattalin arzikin ƙasa gaba da kuma samar da isasshen makamashi a cikin ƙasa, waɗanda su ne hanyoyin cigaba mai ɗorwa".

  14. Muna yin bakin ƙoƙarinmu wajen ƙwato mutanen da aka sace - Sojin Isra'ila

    Isra'ila

    Asalin hoton, Reuters

    Yayin da sojojin Isra'ila ke faɗaɗa hare-hare a Gaza, dangin mutanen da Hamas ke garkuwa da su sun bayyana fargabar game da 'yan uwan nasu ganin yadda yaƙin ke ƙara rincaɓewa.

    Bayan ta bayar da rahoton cewa ƙarin dakarunta sun shiga Gaza da tsakar dare, kakakin rundunar sojin Isra'ila Daniel Hagari ya haƙiƙance cewa ƙwato mutanen "shi ne babban abin da muka saka a gaba".

    Ya ce mutanen su 230 ne, amma a baya hukumomin Isra'ila sun ce 229 ne Hamas da sauran ƙungiyoyi ke riƙe da su a Gaza bayan harin da suka kai ranar 7 ga watan Oktoba.

    "Muna yin duk abin da za mu iya don ganin mun ceto su, shi ne abin da muka saka a gaba. Sojin Isra'ila yanzu haka abin da suke ƙoƙarin yi ke nan a filin daga," in ji shi.

    A gefe guda kuma, Shugaban Isra'ila Isaac Herzog zai gana da wakilan dangin mutanen a yau.

  15. Hamas ta ce dakarunta sun gwabza da na Isra'ila a arewacin Gaza

    Rundunar sojan Isra'ila ta ce har yanzu dakarunta na cikin Gaza bayan hare-haren da suka ƙaddamar ta ƙasa ranar Juma'a da dare.

    Cikin 'yan awannin da suka wuce, shafin Rundunar Izzedine al-Qassam - ɓangaren soji na ƙungiyar Hamas - ya bayar da rahoton cewa sun gwabza da dakaru da kuma motocin yaƙi na Isra'ila a arewa maso yammacin birnin Gaza.

    An samu irin waɗannan rahotonni a jiya daga shafin na Telegram game da fafatawa a arewacin.

    Da tsakar dare kuma, wannan shafn dai ya ce an fafata a gabashin birnin.

    BBC na ƙoƙarin tabbatar da sahihancin wani bidiyo da ya nuna ana ɓarin wuta tsakanin ɓangarorin, wanda aka wallafa a safiyar yau, kuma za mu kawo muku ƙarin bayani da zarar mun samu.

  16. Sarkin Ibira Ado Ibrahim ya rasu

    Ohinoyi of Ebiraland Dr. Abdul-Rahman Ado Ibrahim

    Asalin hoton, State House

    Rahotanni daga Jihar Kogi a tsakiyar Najeriya na cewa Sarkin Ibira Dr. Abdul-Rahman Ado Ibrahim ya rasu yana da shekara 95.

    Kafofin yaɗa labarai na ƙasar sun ambato majiyoyi daga fadar Mai Martaba Ohinoyi na Ƙasar Ibira na cewa sarkin ya rasu ne a ranar Asabar yayin da yake jinya a wani asibiti a Abuja.

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya miƙa ta'aziyya ga iyalansa da kuma al'ummar jihar Kogi, yana mai bayyana sarkin da "ƙwararre wajen tafiyar da al'amura". Ya yi Allah ya ji ƙan sa.

    Marigayin ya hau kujerar mulki a shekarar 1997 bayan wanda ya gada, Sanni Omolorim, ya bar kujerar.

    An haife shi ne ranar 7 ga watan Fabrairun 1929 kuma ya bar 'ya'ya da jikoki da dama.

  17. Netanyahu ya nemi afuwa kan kalaman ɗora wa sojoji laifi a harin Hamas

    Baya ba ta da kaɗan, domin kuwa Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya nemi afuwa game da kalaman ɗora wa jami'an tsaron ƙasar laifi da ya yi game da harin Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba.

    Tun da farko Netanyahu ya wallafa a dandalin X cewa ba a gabatar masa da wasu bayanan sirri ba kafin harin na Hamas, yana mai ɗora wa babban hafsan sojan ƙasa da kuma shugaban hukumar leƙen asiri ta Shin Bet laifi.

    "Na yi kuskure. Abubuwan da na faɗa ba su dace ba kuma ina neman afuwa kan haka. Ina goyon bayan dukkan shugabannin tsaron ƙasar," a cewarsa cikin wani saƙon X.

    Ya nemi afuwar ce bayan 'yan siyasar ƙasar sun caccake shi game da ƙara yaga ɓarakar da ke tsakanin jam'iyyun siyasar.

  18. Shugabannin Isra'ila na rigima da juna kan harin Hamas

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Firaminista Netanyahu (hagu) ke nan tare da ministan tsaro Yoav Gallan lokacin wani taron manema labarai

    Jagoran adawa a Isra'ila, Yair Lapid, ya caccaki Firaminista Benjamin Netanyahu da cewa "ya wuce iyaka" bayan ya ɗora wa jami'an tsaron ƙasar laifin gazawa kan harin da Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoba.

    "Yayin da dakarun sojan Isra'ila [IDF] da kwamandojinsu ke yaƙar Hamas da Hezbollah, shi kuma yana ƙoƙarin ɗora musu alhaki maimakon goya musu baya," kamar yadda Lapid ya wallafa a dandalin X.

    Ya ƙara da cewa: "Yunƙurin wanke kai da ɗora wa jami'an tsaro laifi zai lahanta rundunar IDF yayin da take yaƙar maƙiyan Isra'ila. Dole ne Netanyahu ya nemi afuwa."

    Tuni Netanyahu ya goge saƙon da ya wallafa a dandalin X, inda ya zargi jami'an da gazawa.

    An shafe tsawon lokaci ana rikicin siyasa a Isra'ila kafin harin Hamas da ya kashe Isra'ilawa 1,400 ya tilasta musu jingine rikicin, inda aka kafa gwamnatin gaggawa da za ta jagoranci martani kan 'yan gwagwarmayar na Falasɗinawa.

    Ana kiran gwamnatin da majalisar yaƙi ko kuma war cabinet a Turance.

  19. Mazauna Gaza sun yashe wuraren ajiyar abinci na MDD

    Gaza

    Asalin hoton, AFP

    Dubban mazauna Gaza sun kutsa wuraren ajiyar kayan abinci a kudanci da tsakiyar birnin, inda suka kwashi kayayyaki, a cewar hukumar 'yan gudun hijirar Falasɗinawa ta MDD (UNRWA).

    "Wannan alama ce mai tayar da hankali cewa an fara karya doka bayan sati uku ana yaƙi da kuma toshe hanyoyin kai kayan agaji zuwa Gaza," in ji UNRWA cikin wata sanarwa.

    "Mutane na firgice, ransu a ɓace kuma cikin zaƙuwa. Lamarin ya ƙara ta'azza bayan katse layukan waya da na intanet."

    Sai dai sanarwar da aka fitar a yau Lahadi ba ta fayyace wuraren ajiyar da aka ɓalla ba.

    A ranar Alhamis shugaban sashen ba da agaji na MDD, Martin Griffiths, ya ce "da kyar idan akwai wani kayan agaji da ya shiga Gaza" a makon da ya gabata, yayin da Isra'ila ke ci gaba da ruwan wuta a zirin.

  20. Ƙungiyar Red Cross ta nanata buƙatar tsagaita wuta a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, EPA

    Ƙungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bukaci a sassauta rikicin Gaza cikin gaggawa bayan ta tsoratar game da yanayin da fararen hula ke ciki a Gaza.

    Red Cross ta kuma ƙara da cewa zai yi wuya agaji ya isa Gaza sakamakon ƙawanyar da sojojin Isra'ila suka yi wa zirin, don haka tana kira ga duniya gaba daya ta yi Allah-wadai da matakin Isra'ila na toshe kafofin shigar da kayan agaji.

    Wani mazaunin Gaza mai suna Abdullah ya ce "abin da muka gani sa'o'i 24 da suka wuce, ba mu taba ganin irinsa ba a shekaru 74, Gaza na cikin duhu gaba ɗaya, Isra'ila ta katse duk hanyoyin sadarwa".

    Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce ya yi mamakin yadda Isra'ila ta ke ci gaba da kai farmaki Gaza ba ƙaƙƙautawa.

    Ya kuma yaba wa goyon bayan da aka samu tsakanin ƙasashen duniya na buƙatar tsagaita wuta don a samu damar sakin waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma shigar da kayan agaji.