Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Likitoci a Gaza sun ce Isra'ila ta umarce su da ficewa daga manyan asibitocin yankin

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Abdullahi Bello Diginza

  1. Ayyukan Isra'ila za su iya tilasta wa kowa ya ɗauki mataki - Shugaban Iran Raisi

    Shugaban Iran Ebrahim Raisi ya ce ayyukan Isra'ila "sun wuce iyaka" kuma "za su iya tilasta kowa da kowa ya ɗauki mataki".

    Cikin wani saƙon X - wanda aka sani da Twitter a baya - Raisi ya ƙara da cewa: "Amurka ta nemi kada mu shiga yaƙin amma tana ci gaba da nuna goyon baya ga Isra'ila. Amurkar ta aika saƙonni ga Dakarun Ƙawance 'yan Gwagwarmaya kuma ta gamu da martani ƙarara a filin yaƙi."

    "Dakarun Ƙawance 'yan Gwagwarmaya" na nufin ƙawancen ƙungiyoyin da Iran ke mara wa baya a faɗin Gabas ta Tsakiya, wanda Hamas ke ciki.

    Hukumomin Amurka sun sha gargaɗin Iran da kada ta shiga yaƙin Isra'ila da Hamas da zimmar hana yaƙin yaɗuwa.

    Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon wadda ita ma ke samun taimakon Iran, mayaƙanta na ci gaba da gwabzawa da na Isra'ila a 'yan makonnin nan.

  2. 'Isra'ila ta kashe ƙarin mutum uku a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan'

    Dakarun Isra'ila sun kashe ƙarin mutum uku tsakar dare a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan - garin Falasɗinawa da ta mamaye, in ji ma'aikatar lafiya ta Falasɗinawa.

    Tashin hankali ya ƙaru a yankunan da ƙasar da ta mamaye tun bayan harin da Hamas ta kai cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

    Isra'ila ta kashe sama da mutum 100 a yankin tun bayan fara kai hare-haren baya-bayan nan, da kuma harin 'yan kama-wuri-zauna suke kai wa Falasɗinawa.

    A ranar Asabar, wani ɗan Isra'ila ya harbe wani Bafalasɗine mai shekara 40 a kusa da garin Nablus, a cewar ma'aikatar lafiyar.

  3. Hare-haren Isra'ila na ci gaba yayin da layukan sadarwa suka fara dawowa a Zirin Gaza

    Hanyoyin sadarwa na waya da internet sun fara dawowa a Zirin Gaza bayan Isra'ila ta katse su yayin da take ƙara kai hare-hare a yankin.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce muhimmin abubuwan da ya sa a gaba shi ne rusa Hamas tare da kuɓutar da mutanen da take garkuwa da su.

    Yanzu haka Isra'ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza tare da kai farmaki ta ƙasa bayan Mista Netanyahu ya bayyana cewar yaƙin zai ɗauki dogon lokaci.

    Ma'aikatar kiwon lafiya ta Hamas a Gaza ta ce akalla mutum 8,000 aka kashe tun bayan kaddamar da hare-hare ta sama a matsayin martani ga kisan da Hamas ta yi wa Isra'ilawa 1,400 mako uku da suka gabata.

  4. Barka

    Maraba da sake haɗuwa a shafin rahotonni kai-tsaye.

    Ku biyo ni Umar Mikail don sanin halin da ake ciki a yaƙin da Isra'ila take yi da Hamas a Zirin Gaza.