Nijar ta hana fitar da iskar gas zuwa ƙetare

Asalin hoton, Getty Images
Jamhuriyar Nijar ta hana fitar da iskar gas zuwa ƙasashen waje har zuwa wani lokaci.
Gwamnatin ƙasar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talatar da ta gabata.
Sanarwar ta ce ya kamata a yi amfani da gas din da ake haƙowa a ƙasar wajen wadata kasuwannin cikin gida, kuma idan aka samu wadatan shi sosai, za a iya neman izini na musamman na fitar da shi zuwa kasashen waje.
Nijar dai ta saba fitar da iskar gas din ta zuwa makwabciyarta Najeriya.
- 'Mutane sun wahala a Nijar kuma suna neman wanda za su ɗora wa laifi'
- Abin da ya sa Rasha ta dakatar da bai wa Turai iskar gas








