Ambaliyar Libya: An dakatar da koyarwa na wucin-gadi

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan gwamnatin hadin kan ƙasa ta Libiya Abdul Hamid Al-Dabaiba ya dakatar da koyarwa a makarantu a duk fadin kasar na tsawon kwanaki 10, a wani mataki na nuna goyon baya ga 'yan ƙasar da ambaliyar ruwa ta shafa a ranar 11 ga watan Satumba.
Gwamnatin hadin kan kasa ta kasar Libya mai hedkwata a Tripoli babban birnin kasar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da yammacin jiya Laraba.
Gwamnatocin Libya biyu masu gaba da juna, gwamnatin hadin kan kasa da kasashen duniya suka amince da su karkashin jagorancin firaministan Al-Dabaiba da kuma gwamnatin gabashin Libya, karkashin jagorancin firaminista Osama Hamad.
Dukkansu suna gudanar da ayyukan mayar da martani a gabashin Libya da ambaliyar ruwa ta shafa.
Sanarwar ta kara da cewa dakatar da koyo zai ba da damar yin amfani da makarantu a matsayin mafaka na wucin gadi ga waɗanda suka tsira daga ambaliya.
- Ana fargaba fiye da mutum 20,000 sun mutu a bala'in ambaliyar Libya
- 'Tamkar ambaliyar tsunami ce ta auka wa birnin Libya'

