Ƴan bindiga sun kashe limaman coci 23 a Kaduna - CAN

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ana zargin matashi da kashe wasu mutum biyu ta hanyar tsafi a Bauchi

    'Yan sanda

    Asalin hoton, OTHER

    A Najeriya, rundunar 'yan sandan kasar tana gudanar da bincike kan wani matashi mai sana'ar gawayi da ke kauyen Taranka, na jihar Bauci, wanda ta damke bisa zargin kashe wasu mutum biyu 'yan asalin kauyen Dankunkuru na yankin karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano.

    Ana zargin matashin da kashe mutane ya na cin namansu, kuma an gano gawawwakin matasan biyu da ya binne a gidansa.

    Rundunar 'yan sandan ta ce matashin mai suna Ibrahim Muhammad, mai shekara 40, na hannunta inda za a fadada bincike bisa zargin da ake masa.

    SP Ahmed Mohammed Wakil, shi ne mai magana da yawun rundunar 'yan sandan a jihar Bauci, ya shaida wa BBC cewa matashin ya musanta dukkan zargin da ake masa, to amma ko a lokacin da aka kai shi ofishin 'yan sandan an same shi da jini a roba, to amma sai ya ce jini ne na bushiya da kurkuru ba jinin mutum ba ne, kuma da jinin ya ke amfani ya na maganin maciji.

    SP Ahmed Wakil, ya ce koda suka je gidansa an ga adduna da fatanya da jini a cikin roba.

    Ya ce, " Game da kaburburan da ake zargi ya binne matasa biyu da ya kashe, muna bincike a kai don gano gaskiyar komai."

  2. Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ya yi murabus

    Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan, Volker Perthes, ya yi murabus daga mukaminsa.

    Volker Perthes, ya ce ya ajiye aikin nasa ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.

    Ya ce rikicin da ya barke tsakanin bangarorin soji da ke gaba da juna a watan Afrilu a Sudan, ya kama hanyar zama cikakken yakin basasa.

    Mista Perthes, ya ce a kodayaushe suna tare da fararen hula, da mata da yara kanana na Sudan da kuma al'umma masu rauni wadanda ke fuskantar munin rikicin.

    Mista Perthes, ya ce ya fuskanci suka daga wasu da dama a kasar Sudan, wadanda suke ganin bai dauki matakin da ya dace ba a lokacin da shugabannin soji suka karbe mulki shekaru biyu da suka gabata, tare da dakatar da shirin mika mulki ga farar hula.

  3. An kama ƴan sintiri bisa laifin ƙwace da hantarar al'umma

    ...

    Asalin hoton, Imo Police Command

    Rundunar 'yan sandan Imo da ke kudancin Najeriya, ta ce ta kama 'yan sintiri shida da laifin ƙwace da hantarar mutane.

    'Yan sintirin shida an tura su jihar ne domin su yi bincike da kuma kawar da ɓata gari a jihar, kuma sun hadar da jami'ai uku daga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA, da sifetan ɗan sanda guda da kuma jami'an tsaro na NSCDC.

    Ana zargin mutanen shida da hantara da azabtarwa da kuma sace wa Nnaemeka Pat Obiji, kudi har naira dubu 360 a ranar 7 ga watan Satumbar 2023.

    Kazalika sun sace kuɗi a unguwar Ohii/Egbeada, ta hanyar sanya mai amfani da POS ya tura musu kudi cikin asusun aiyarsu na banki.

    Haka kuma ana zargin 'yan sintirin da sacewa Mr Eluigwe Christian kudi har naira dubu 959 da kuma dubu 30 na wata mata Princess Chisom Duru.

    Bayan kama mutanen, rundunar 'yan sandan ta ce ta gano abubuwa da dama da mutanen suka sace ko suka ƙwata a hannun mutanen ciki har da wayar salula 12.

  4. Kalli yadda ambaliya ta shafe wasu biranen Libiya

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo
  5. Labarai da dumi-dumi, Mutum 8 sun jikkata sakamakon fashewar bama-bamai a Mogadishu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, ...

    Rahotanni daga birnin Mogadishu na cewa an kai hari kan wata mota makare da bama-bamai a wani shingen bincike a gundumar Dayniile inda 'yan sandan da sojoji suke.

    Wani dan ƙunar bakin wake ne ya tuƙa motar da ke dauke da bam din ya nufi wajen da sojojin ke zaune.

    Sojoji bakwai da fararen hula sun jikkata sakamakon harin kamar yadda majiyoyi na kasar suka bayyana.

    Kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin, inda ta ƙara da cewa ɗaya daga cikin matasanta 'yan ƙunar bakin waken ne ya kai harin.

    A 'yan watannin baya-bayan nan dai kungiyar ta Al-Shabaab ta sha wahala wajen shigar da ababen fashewa cikin birnin, kuma an ƙara daukar matakan tsaro na duba motocin da ke shiga babban birnin kasar.

  6. Yara miliyan 333 na rayuwa cikin tsananin talauci a duniya - UNICEF

    Yara

    Asalin hoton, OTHER

    Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya fitar da wani rahoto da ke cewa kimanin yara miliyan 333 na rayuwa cikin kangin talauci a duniya.

    Rahoton na UNICEF da hadin gwiwar Bankin Duniya ya nuna cewa tsananin talaucin na da nasaba da annobar korona da sauran kalubale da dama da suka hada da sauyin yanayi.

    Rahoton ya ce alkaluma sun nuna cewa yaro daya cikin shida na rayuwa a kan kasa da dala biyu a kowacce rana.

    A cewar rahoton, nahiyar Afirka ta yamma da Sahara na cikin wuraren da ke da mafi yawan yara kanana da adadinsu ya kai kashi 40 cikin 100 wadanda ke rayuwa a wani mawuyacin hali na tsananin talauci.

    Bayan wani bincike da aka gudanar shekaru goma da suka wuce, an gano cewa yankin Afirka ta yamma da sahara ya daga daga matakin da aka san shi, inda a shekarar a 2013 ya ke da kashi 54.8, a 2022 kuma ya koma kashi 71.1 cikin dari.

    Akwai dai manyan dalilai da aka bayyana da ke taka rawa wajen karuwar talaucin da suka hada da karuwar jama’a cikin sauri da rikici da ta’adin annobar korona da sauyin yanayi mai nasaba da aukuwar itila’i daban-daban, wadanda sun taimaka wajen munana yanayin.

    A cewar rahoton na UNICEF, yara da ke gidaje matalauta na fama da kalubalan rayuwa da suka danganci rashin wadataccen abinci da wurin kwana da ingantaccen kiwon lafiya da ilimi, wadanda abubuwa ne da za su taimake su a rayuwa.

    Rahoton na UNICEF ya kara da cewa irin wadannan yaran na rayuwa ne a yankunan karkara da kuma wadanda ke zaune a gidaje matalauta inda galibin iyayensu na da karancin ko rashin ilimi.

    Daga bisani UNICEF, ya zayyano wasu muhimman matakan da ya ce gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu a duniya su lura da su,ciki har da mayar da hankali wajen tallafawa yara da ke rayuwa a kasashen da ke fama da tsananin talauci ko a yankunan da ke fuskantar rikici.

  7. Sojojin Mali sun ce sun kashe mayaƙa 46

    Sojoji

    Asalin hoton, OTHER

    Rundunar sojin Mali ta ce ta kashe akalla wasu maza 46 da ta bayyanasu a matsayin 'yan ta'adda.

    Kazalika rundunar ta ce an kashe ma ta sojojinta 10, da kuma raunata wasu da dama bayan wani hari da aka akai a sansanin Bourem/Embourgagne.

    Ana mummunan fada a arewacin Gao da kuma Timbuktu tsakanin 'yan tawayen Tuareg da sojoji.

    Yanzu haka mahukunta a Mali ba sa bambance tsakanin 'yan gwagwarmayar Azawad da kuma kungiyoyin masu jihadi.

  8. Gwamnan Kano ya dakatar da jami'in da ake zargi da sayar da hatsin gwamnati

    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf

    Asalin hoton, FACEBOOK/Abba Kabir

    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin dakatar da shugaban kamfanin samar da kayan aikin gona na jihar (KASCO), bisa zargin shi da sayar da hatsi mallakar gwamnati.

    Sanarwar da babban sakataren yaɗa labarai ga gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, na cewa a ranar Talata 12 ga watan Satumban 2023 ne, Gwamna Abba Kabir, ya bayar da wannan umarni.

    Sanarwar ta ce ana zargin Dr. Tukur Ɗayyabu Minjibir, ne da sayar da hatsin gwamnati, ba ta hanyar da ta dace ba.

    Gwamnatin jihar ta umarci Dr Tukur Ɗayyabu, ya miƙa ragamar gudanar da kamfanin ga jami'i mafi girman muƙami nan take, ya zuwa lokacin da za a ji sakamakon ƙarin bincike.

    • Farashin shinkafa zai tashin da bai taɓa ba cikin shekara 12 - MDD
    • Ko rushewar yarjejeniyar fitar da hatsi ta Ukraine za ta janyo ƙarancin abinci?
    • Abin da dokar ta-ɓaci kan samar da abinci ke nufi ga talakan Najeriya
  9. Teku yana ta tunkudo gawawwaki a Libya

    Mutane na daukar gawawwaki

    Asalin hoton, Libyan Red Crescent/Reuters

    Akwai wuraren da ambaliyar ruwa ta yi wa mummunar barna a birnin Derna da ke gabashin Libya bayan da madatsar ruwa ta karye.

    Gwamnatin da kasashen duniya suka amince da ita a Tripoli ta ce akalla mutum 2,300 sun mutu a birnin, yayin da gwamnatin da ke iko da Derna ta ce an gano gawawwaki fiye da 5,300.

    Har yanzu akwai dubban mutanen da ba a gani ba, sannan mininstan da ya fito daga gabashin kasar ya ce, teku na ta turo gawawwaki.

    Akalla mutane dubu 34 sun rasa muhallansu a yankunan da ambaliyar ta fi barna, kazalika wasu hotuna sun nuna irin mummunar barnar da aka samu a yankunan, da kuma yadda tsaunuka da baraguzan gini suka murkushe motoci.

    Akwai kayan tallafin da suka fara isa kasar, to amma saboda rarrabuwar kawunan da a ke fama da su a tsarin siyasar kasar musamma a gabashi da kuma yammaci, firaiministan kasar a Tripoli ya ce za su karbi kayan tallafin da suka zamo wajibi ne kadai.

  10. Yaƙi ba mafita ba ne ga Nijar a rikicinta da su Ecowas - Masana

  11. Ƴan bindiga sun kashe fasto-fasto 23 a Kaduna - CAN

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Kiristoci a Najeriya wato CAN, ta fitar da wata sanarwa da ke cewa hare-haren ‘yan bindiga sun yi sanadiyyar kashe limaman mujami’u 23 a jihar Kaduna.

    Hakazalika, a cikin shekaru huɗu kawo yanzu lamarin ya kai ga rufe kimanin mujami’u 200 da ke faɗin jihar.

    Shugaban ƙungiyar ta CAN reshen jihar Kaduna, Rev. John Hayab, ya bayyana damuwarsu kan lamarin da ya ce ya kai intaha.

    Bayanan sautiLatsa lasifika domin sauraron tattaunawa
  12. Ambaliyar ruwar Libya: Sama da mutum 34,000 sun rasa gidajensu

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, ...

    Hukumar Kula da 'yan ci-rani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla mutum 34,000 ne suka rasa muhallansu a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a ƙasar Libya.

    Birnin Derna mai tashar jiragen ruwa inda wata mahukaciyar guguwa mai suna Daniel ta yi sanadin fashewar madatsun ruwa guda biyu, ya fi taɓuwa, inda a halin yanzu mazauna 30,000 suka rasa matsugunansu.

    Hukumar ta ce mazauna yankin na bukatar matsuguni da abubuwan da ba na abinci ba, amma miƙa taimako ga iyalai da abin ya shafa na da kalubale ganin yadda akasarin hanyoyin yankin ke ci gaba da fuskantar cikas da kuma cika da ambaliyar ruwa.

  13. Mazauna garin Hanoi sun makale a wata gobara da ta tashi a Vietnam

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, ...

    Akalla mutum takwas sun mutu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wata gobara da ta tashi a wani gida a Hanoi babban birnin kasar Vietnam.

    Kafofin yada labaran ƙasar sun ce an ceto wasu mutum 70 daga ginin mai hawa tara amma rahotannin cikin gida sun ce adadin ya zarta haka.

    An dai kashe gobarar wadda ta tashi cikin dare amma ana ci gaba da aikin ceto.

    Hukumomi a Hanoi sun ce sabbin gidaje da aka gina da yawa ba sa ba su bi ka'idojin kiyaye aukwar gobara ba.

    Yawan mutanen birnin ya rubanya zuwa sama da miliyan 5 a cikin shekaru 20 da suka gabata.

  14. Cikakken jerin ƙasashen da za su buga Gasar cin Kofin Afirka ta 2024

    African Cup of Nations

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Afirka 24 ne suka cancanci samun gurabe, don buga Gasar cin Kofin Afirka da za a yi a ƙasar Ivory Coast cikin watan Janairun 2024.

    Sun haɗar da:

    • Afirka ta Kudu
    • Aljeriya
    • Angola
    • Burkina Faso
    • Cape Verde
    • Equatorial Guinea
    • Gambia
    • Ghana
    • Guinea
    • Guinea-Bissau
    • Jamhuriyar Ɗimokraɗiyyar Kongo
    • Kamaru
    • Mali
    • Masar
    • Mauritaniya
    • Moroko
    • Mozambique
    • Najeriya
    • Namibiya
    • Senegal
    • Tanzaniya
    • Tunisiya
    • Zambia

    Akwai kuma ƙasar Ivory Coast, wadda za ta karɓi baƙuncin da ke da gurbi kai tsaye.

    • Kamaru ta samu gurbin zuwa buga kofin Afirka a 2024
  15. Ƴan aikin sa kai uku sun mutu yayin aikin ceto a Libiya

    f

    Asalin hoton, International Federation of Red Cross and Red Crescent Societies

    Kungiyar agaji ta Red Cross da Red Crescent ta duniya ta bayyana cewa, 'yan aikin sa-kai uku sun mutu lokacin da suke taimakawa mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a gabashin Libya.

    Hamdi Belaid da Khaled Adwal da kuma Abadi Al-Kharm sun mutu ne yayin da suke taimakawa wasu mazauna garin Derna, da ambaliyar ruwa ta ritsa da su, in ji babban sakataren ƙungiyar Red Cross, Jagan Chapagain.

    "Ina bayyana takaici tare da miƙa sakon ta'aziyyata ga iyalansu da abokan aikinmu na ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta Libya," in ji shi.

    Ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceto, daidai lokacin da ake fargabar ɓatan mutum 10,000, sanadin ambaliyar ruwa.

  16. Jami'an tsaro sun kama mutum 10 bisa zargin fasa bututun mai

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Security and Civil Defence Corps/Facebook

    Bayanan hoto, ...

    Hukumar tsaron fararen hula ta NSCDC, reshen jihar Ribas, ta ce ta kama mutum 10 bisa zargin fasa bututan man fetur, da satar ɗanyen mai da kuma safarar haramtattun abubuwa.

    Cikin saƙon da hukumar ta wallafa a shafinta na X wanda a baya ake kira Tuwita, ta ce ta kama wasu motoci guda tara maƙare da kayan sata a cikin buhunhuna, tare da lita 28,225 ta man dizel.

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Security and Civil Defence Corps/Facebook

    Bayanan hoto, ...

    Mutum goman da ake zargin sun haɗar da, Chinedu Michael wanda aka bayar da belinsa watanni biyu a baya, lokacin da hukumar ta kama shi bisa zargin tace man fetur ba bisa ƙa'ida ba.

    ...

    Asalin hoton, Nigeria Security and Civil Defence Corps/Facebook

    Bayanan hoto, ...

    Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar rundunar da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, Kwamandan jihar, Basil Igwebueze ya bayyana cewa, rundunar ta cafke wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban a fadin jihar.

    • 'Sai hukumomin tsaro sun haɗa kai a ga bayan matsalar tsaron Najeriya'
  17. Masar ta gano ƙarin gawarwaki masu yawa da suka mutu a ambaliyar ruwan Libiya

    h

    A yau ne ake zaman makokin 'yan Masar da dama da suka mutu sakamakon guguwa da kuma ambaliya da ta mamaye wasu yankunan gabashin ƙasar Libiya a wasu ƙauyukan ƙasar.

    An samu gawarwaki fiye da mutum 70 a ƙauyen Ihnasia da ke Beni Suef a kudancin birnin Alkahira, a lokacin da guguwar Daniel da kuma ambaliyar ruwan.

    Wasu 'yan uwan ​​waɗanda abin ya shafa sun ce waɗanda suka mutu yawancinsu ma'aikata ne da masu sana'a.

    Masar na fuskantar mahaukaciyar guguwa mai suna Daniel sakamakon ambaliyar ruwan Libya

    A ranar Talata hukumomin Libiya suka sanar da samun gawarwakin 'yan Masar 145 da suka nutse a cikin ruwan da ya afkawa yankunan Derna da Al-bayda da ke gabashin ƙasar Libiya.

    Karamar Hukumar Tobruk ta bayyana cewa an mayar da gawarwakin Misrawan zuwa kasar ta tashar jirgin ruwa ta Salloum.

    Hukumomin Libya sun kuma buƙaci duk ‘yan ƙasashen waje da su kai rahoton waɗanda suka ɓace domin neman su ko gawarwakinsu.

    Ƙasar ta Libya ta kuma yi kira ga mazauna Tobruk su ƙaurace wa gidajensu, tare da hana tafiye-tafiye a kan manyan titina domin kare rayuwarsu da nesantar gabar teku.

    Ma'aikatar harkokin wajen Masar a cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya ta ce, tana ci gaba da yin aiki tare da mahukuntan Libya domin ƙidaya adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwan.

  18. 'Mutum 936 ne suka mutu a hatsarin kwale-kwale cikin shekara uku a Najeriya'

    g

    Asalin hoton, Getty Images

    Aƙalla mutum 936 ne suka mutu a hatsarin jirgin ruwa daba-daban da suka faru a Najeriya cikin shekara uku.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ƙarancin hanyoyin cikin ruwa marasa cunkushewa da yayi da kuma ɗaukar fasinjoji da suka wuce iyaka na cikin matsalolin da ke janyo wannan lamari.

    Hakan ya sa a ranar Talata Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin gudanar da bincike kan yawan kifewar kwale-kwale a Najeriya da yake neman zama ruwan dare.

    Masana dai na ta bayar da shawara cewa ya kamata mahukunta su ɗauki matakin da ya wuce na furtawa da fatar baki kawai a gani a aikace don a shawo kan wannan matsala.

    Sun kuma bayar da shawara kan cewa kamata ya yi a maye gurbin kwale-kwalen da ake da su na gargajiya da na zamani, domin ci gaba da sufuri da su.

    A Najeriya dai sufuri ta hanyar jirgin ruwa na gudana ne a hannun mazauna ƙauyukan da ruwan yake, abu ne da gwamnati ba ta mayar da hankali a kai ba, wanda hakan ya sabawa ka'idar aikin da aka shimfiɗa a duniya.

    Hatsarin da ya faru a makon jiya ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 20, ya janyo wa hukumomin da ke lura da sufurin jiragen ruwa suka na rashin mayar da hankali kan abin da ke gudana arewacin Najeriya da Allah ya albarkanta da tafkuna da kuma ƙoramu.

    Sai dai kullum hukumomi na iƙirarin suna iya ƙoƙarinsu domin daƙile wannan matsala.

    • 'Yadda na tsira daga hatsarin jirgin ruwan da ya kifar da mutum 160 a Kebbi'
  19. Hoton tauraron ɗan'adam na ɓarnar da ambaliya ta yi wa Libya

    Mun samu hoton tauraron ɗan'adam na gefen garin Derna kafin da kuma bayan ambaliyar da ta faru a yankin gabashi da ke kusa da tashar jirgin ruwa.

    Kalli yadda ruwan ya yi barna.

    re

    Asalin hoton, Reuters

  20. Bidiyon tarkacen motoci da gine-gine bayan ambaliyar Libya

    Bayanan bidiyo, Bayan samun musifar ambaliyar ruwa a Libya, an samu asarar dukiya mai yawa, motoci da gine-gine sun lalace.